Halin da na samu kaina a karkashin Boko Haram -Wata mata da ta tsira
Wata mata da ta bukaci a boye sunanta saboda abin da ya shafi tsaro ta bayyana yadda ta yi rayuwa ta kwana 11 a garin Mubi bayan ’yan Boko Haram sun kwace ikon da garin. Ta bayyana yadda suka rika ba ta abinci da fadi-tashin da ta yi har ta fita daga garin, inda a […]

Wata mata da ta bukaci a boye sunanta saboda abin da ya shafi tsaro ta bayyana yadda ta yi rayuwa ta kwana 11 a garin Mubi bayan ’yan Boko Haram sun kwace ikon da garin. Ta bayyana yadda suka rika ba ta abinci da fadi-tashin da ta yi har ta fita daga garin, inda a karshe ta samu da taimakon Allah ta iso Abuja ta samu mijinta. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Aminiya: Kina daya daga cikin mutanen Mubi a Jihar Adamawa wadanda rikicin Boko Haram ya shafa, hakan ya sanya mutane suka yi gudun hijira saboda tsoron abin da zai je ya zo, gasliya ne kin yi kwanaki a garin bayan ’yan Boko Haram sun kwace iko da garin, kuma me ya jawo hakan? Me ya sa kika zabi zama a Mubi maimakon ki yi gudun hijira?
Na yi kwana 11 a Mubi bayan ’yan Boko Haram sun kwace iko da garin Mubi, jama’a sun watse, rashin lafiya ya sanya ni ma ban fita, na yi hadari a kwanakin baya hakan ya sanya kafata ta samu matsala, ga shi kuma ’ya’yana uku, daya ana goyonsa, daya kuma dan shekara 2, sai babbansu wanda ya bi sauran ’yan gudun hijira. Mijinmu yana da mata uku, ni kadai ce wadda take da matsakar kafa saboda hadarin da na yi, shi ne ya kai su Kamaru, ciki har da babban dana.
Aminiya: Yaya aka yi ba ki bi mijinki da kishiyoyinki ba?
Tafiyar kafa suka yi saboda babu mota, ni kuma kamar yadda na fada maka ba ni da lafiyar kafa.
Aminiya: Bayan kin zauna me ya faru?
Da yake kafin su tafi akwai kayan abinci a gida, to bayan na zauna sai na rika dafawa. Abincinmu ya kare, babu banki, babu kasuwa, na rasa yadda zan yi sai na yanke hukuncin in same su don su ba ni abinci. Ba su yi mini komai suka rika ba ni abinci, zuwana sau biyu, sai na fara fargabar kada wani abu ya faru, shi ne na bar garin.
Aminiya; Wane karfin gwiwa kika samu har kika tunkare su don su ba ki abinci kasancewar mutane suna tsoronsu?
dana yake mini kuka, yunwa ta dame shi, kuma babu inda zan je in samu abinci, ina da kudi amma babu mai sayarwa, duk garin an gudu, babu mai sayar da abinci, haka ya sanya na tambaye su, abin da ya ba ni mamaki shi ne, idan na tambaye su ba sa yi mini tsawa ba, ko fada ko wani abu.
Aminiya: Ba ki yi tunanin ko za su yi miki wani abu ba?
Ba sa yi wa mata da kananan yara komai, hakan ya sanya na fita na same su.
Aminiya: Ke kadai ce kika rage a garin ko akwai wadansu matan?
A layinmu mu biyu ne muka rage.
Aminiya: Amma a wadansu layukan za a iya samun wadansu matan?
Za a iya samu, ina tsammanin suna nan.
Aminiya: Bayan ’yan Boko Haram sun kwace iko da garin wadanne ayyuka suka rika gudanarwa?
Ban ga suna gudanar da komai ba gaskiya, sai dai wani lokaci zan ji suna ta harbe-harbe, ba wani suke harbi ba, suna harbi a fili ne, bayan na samu na bar garin ne na je Gombi, inda kwana uku da zuwa na can suka sake zuwa Gombi. A Gombi ne harsashi ya sauka kusa da ni. Bayan na ji kara ne sai na juya, daga baya na ga ya fadi a kusa da ni.
Aminiya: A lokacin da za ki fito daga Mubi, ko ’yan Boko Haram suna sanya shingaye kamar yadda jami’an tsaro suke yi?
Ba a bari a bi hanya, ni ma daji na rika bi har a karshe bayan na zo wani kauye na samu wani mai babur ya dauke ni.
Aminiya: Wane kauye ke nan?
A gaskiya ban san sunansa ba, domin ban taba zuwa ba.
Aminiya: Amma mutanen kauyen ba su gudu ba?
Ba su gudu ba.
Aminiya: Mai babur din ne ya kai ki Gombi?
A’a, wani kauye ya kai ni, ni ma ban san sunan kauyen ba, a nan na samu mota da ta kai ni Gombi. Bayan na yi kwana uku a Gombi ne ‘yan Boko Haram din suka zo kuma.
Aminiya: A kwanakin da kika yi a Mubi, shin ba sa gudanar da wa’azi?
Suna yin wa’azi, don ina zaune a kofar dakina ina jin wa’azin da suke yi a kofar fadar sarki. Sun kwace fada, wadansu a nan suke kwana.
Aminiya: Me suke cewa a lokacin da suke wa’azin?
Ba zan iya maimaita abin da suke cewa ba. Maganganun da yawa.
Aminiya: Ki fada mana kadan daga ciki..
A gaskiya ina da yawan mantuwa, sannan a lokacin ina cikin tashin hankali.
Aminiya: Ba za ki iya tuna wani abu da suke cewa ba?
Suna cewa mutane su daina guduwa, sun zo da abu mai kyau ne, sun zo za su taimaki Musulmi ne, mutane su daina guduwa, ba da Musulmi suke yaki ba.
Aminiya: Amma an ce sun kashe Musulmi a Mubi, shin haka ne?
Ni dai ban ga wannan ba, Kirista aka ce sun kashe, ni ma labari na ji, amma ban gani ba.
Aminiya: A lokacin da kike bin daji don tsira da rayuwarki ba ki hadu da komai ba?
Na ji wari, idan na tambaya sai a ce an kashe mutum ne a wurin, haka na rika jin wari a wurare daban-daban, a wani wuri ma za ka ga jakar mutum, ga kayayyaki a ciki,
Aminiya: Lokacin da kika fita daga Mubi zuwa kauyen da kika samu mai babur, kin yi kamar kwana nawa?
Wuni daya ne kawai, amma na sha wahala.
Aminiya: daya dan naki shi ma bin ki yake a kafa?
Yana bi na, daya kuma na goya shi, ban kuma fito da komai ba.
Aminiya: Me ya sa?
Suna karba.

Sun ga lokacin da za ki fita ke nan?
Muna haduwa da su, su ne a bakin hanya, idan sun ga mutum da kaya ko a leda ne sai su karba, idan ya ce ba barin gari zai yi ba, sai su ce ya ajiye idan ya dawo ya zo ya dauki abinsa. Shi ya sa ban dauki komai ba.
Aminiya: Lokacin da kika je karbar abinci a wurinsu sun kai kamar nawa?
Idan na fito daga gidanmu sai in tsaya a bakin hanya, idan sun zo wucewa sai in tsayar da su, in ce musu ba ni da abinci, sai su hada ni da wani, sai in bi shi wata ma’ajiyar abincinsu ya ba ni.
Aminiya: Wane nau’in abinci suka ba ki?
Sun ba ni danyar shinkafa da masara da wake da ruwa (pure water) da sauransu. Suna da wurin da suka ajiye abincinsu.
Ko kin ga wadanda suke dafa musu abinci?
A’a, wurin da aka kai ni babu kowa, sai dai sun ajiye kayan abinci a wurin.
Aminiya: A kan me suke zuwa su wuce ta layinku?
A kan babur ne, wadansu kuma a kafa, dukkansu dauke da bindigogi.
Aminiya: Ba su bi gida-gida su rika dubawa ko akwai mutane?
Ba su bi, ni dai babu wanda ya zo duba gidanmu, ba su shiga wani gida a unguwarmu ba, sai dai suna waje suna zagayawa.
Aminiya: Bayan kin gudu zuwa Gombi sai kuma ga shi sun je can, ko kin ga daya daga cikin wadanda suka taimake ki lokacin kina Mubi?
Ban fita ba, ina zaune kawai a gida.
Aminiya: Kin je wurin danginki a Gombi ne, ko kuma kin bukaci taimako a wurin jama’a ne?
Na je wajen yayata ce.
Aminiya: Da suke je Gombi, ba ku gudu ba?
Da za mu gudu ni da ita, to ba zan iya ba, saboda tafiyar kafa ake yi, ganin haka sai ita ma ta zauna. Kasancewar yawancin mutane sun gudu a Gombi, da suka ji labarin za su zo Gombi.
Aminiya: Wane abu kika gani wanda ya fi daga miki hankali?
Yadda marasa lafiya suka rika guduwa daga asibiti duk da halin da suke ciki, inda wadansu suka rika mutuwa a hanya, saboda babu malaman asibiti, babu kowa da yake kula da su. A lokacin dana ma ba shi da lafiya, babu inda zan saya masa magani, abin da ya sa na bar Mubi din ma shi ne, ina da kudi amma babu wurin da ake sayar da abinci. Amma Boko Haram ba sa yi mana komai. Idan sun hadu da mu sai su ce ku daina guduwa ba wurinku muka zo ba. Mun zo mu kwato muku hakkinku ne, mu taimake ku.
Aminiya: Yaya aka yi kika samu kanki a Abuja?
Bayan na zo Gombi kafin a yanke sadarwa sai na fada wa maigidana ina Gombi, na fada masa ga shi kuma ’yan Boko Haram sun sake iske mu a can. kafin ya turo kudi sai aka sake rufe hanyar Gombi. Haka dai muka rika bin daji har muka zo bakin hanya, a karshe muka samu motar da ta kawo mu Yola. Bayan na zo Yola sai na samu nan ma mutane suna tsoro, wadansu sun gudu, sai na samu wani gida babu kowa a ciki, haka na yi kwana hudu a kicin. Bayan maigidana ya turo kudin ne sai wani dan gidan abokin mijina ya fitar mini da kudin a banki, shi ne na zo Abuja.
Aminiya: Kin ce sun gudanar da wa’azi a lokacin da kike Mubi, ko shugabansu wanda ake kira Shekau ya gabatar da wa’azi a garin?
Ban yi tsammanin hakan ba, domin ban gan shi ba, na ji dai ana cewa wai babbansu ya zo, har ya yi wa’azi a Masallacin Juma’a da ke kofar gidan sarki, tabbas na ji muryar wani, kuma an ce shi ne shugabansu gaba daya.
Aminiya: Wane ne ya fada miki hakan?
Haka wata mata da ke kusa da layinmu ta fada mini, a lokacin ta ce a ranar Juma’a shugabansu gaba daya zai zo ya yi wa’azi, sannan bayan ranar ta zo na ji muryarsa yana wa’azi.
Aminiya: Idan komai ya daidai za ki koma Mubi?
Ba ni da wani gari da wuce shi, don haka addu’armu ita ce, Allah Ya kawo karshen wannan al’amari.