Halin da na shiga bayan karbar kwagilar abincin bogi na N13m

Hajiya Aisha ta ce sai da gama dafa abincin mutane 9,600 dan kwangilar ya yi layar zana

Halin da na shiga bayan karbar kwagilar abincin bogi na N13m

Wata mata mai gidan abinci ta fada tarkon ’yan damfara inda aka ba ta kwangilar bogi ta samar da abinci na kwanaki uku kan kudi Naira miliyan 13.

An ba Hajiya A’isha Ibrahim kwangilar bogin ce da sunan za ta ciyar da mabukata dubu tara a kananan hukumomi uku na jihar.

Labarin Hajiya Aisha da ke sana’ar abinci a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi ya karaɗe gari ne bayan ta yi bidiyon halin da take ciki a kafofin sada zumunta.

Hakan ya sa gwamnan jihar, Sanata Bala Abdulqadir Muhammad ya shiga tsakani ya biya ta kudin data kashe wajen yin abincin, aka karbi abincin aka raba wa masu bukata.

A zantawar datayi da manema labarai, Hajiya Aisha ta ce wani mutum ne ya tuntube ta da ya ba ta kwangilar samar da abinci ga mutane 9,600 a kananan hukumomin Bauchi, Alkaleri, da Kirfi.

A yayin da take bayyana irin halin da ta shiga, duk da cewa ba ta bayyana sunan mutumin da ya ba ta kwangilar bogin ba, Hajiya Aishah ta ce mutumin ya ba ta tabbacin cewa nan ba da dadewa ba za a rattaba hannu kan yarjejeniyar kwangilar, kuma ba za a saka ta cikin hadari ba.

“Ya dage cewa in ci gaba da kwangilar saboda ba a sanya hannu kan yarjejeniyar ba, amma za a ba ni takardan yarjejeniyar yin kwangilar lokacin da aka sanya hannu,” inji Aisha.

Ta ce ta amince da tabbacin da ya ba ta saboda ta san yadda kungiyoyi masu zaman kansu suke yi, in suka bada irin wannan aiki, kuma suna biya bayan an kammala aikin.

Daga nan sai ta saki zucuyarta ta ci gaba da bin umurnin mutumin ta samo ma’aikata ta suka kwana suna aikin yin abinci.

Ta ce da suka kammala sai ta kira mutumin da nufin ta san wadanda za su karbi abincin, sai ya ce ta jira yana jiran a ba shi umurni tukuna.

“Bayan karfe 1 na rana ban ji duriyarsa ba, sai na tafi ofishinsa, ya ce in jira yana jiran umarni.

“Bayan uku na yamma na fara kiran sa sau da yawa, amma ba ya dauka.

“Da muka je ofishinsa da mijina da misalin karfe biyar na yamma, sai aka ce mana ba ya nan.

“Tun daga lokacin ya ki daukar wayata har qarfe biyar na yammaci.”

Hajiya A’isha ta ce ta yi matukar kaduwa da lamarin domin ta karbi basussuka ne ta yi abincin.

Da ta kasa samun mutumin, sai ta shiga kafafen sada zumunta tana neman taimako.

Ta ce “Kwamishiniyar jin qai da bada agaji na Jihar Bauchj Hajiya Hajara Yakubu Wanka ta kira ni inda ta ce Gwamna ya ga bidiyona a intanet kuma ya umarce ta da ta biya ni diyya.

“Ina godiya ga Gwamna Bala Mohammed kan matakin da ya dauka na ceto ni cikin gaggawa.”

Hajiya Aisha ta ce gwamnati ta biya kudin da ta sayi kayan Naira miliyan 7.5 ba, kuma ta karbi abincin aka rarraba shi wa masu bukata.

Da yake mayar da martani kan lamarin, babban sakatare a ma’aikatar, Alhaji Shuaibu Alhaji Muhammad, ya bayyana cewa asalin kudin kwangilar naira miliyan 13 ne, amma gwamnatin jihar ta biya diyya na ainihin kudin kayan abinci da Hajiya Aisha ta saya.

Wani abu daya ja hankalin jama’a shi ne Hajiys Aisha ta zabi kada ta bayyana sunan mutumin da ya yaudare ta, duk da cewa ta yi wa jami’an tsaro cikakken bayani.

Ta kuma gargadi jama’a game da masu zamba a asusun banki da za su ce za su rika neman tallafi da sunanta.

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja

Tirela murƙushe ’yan sanda 3 har lahira

An ƙwace kwantainoni 54 mallakin Emefiele

Fulawa da dabbobin Fadar Shugaban Ƙasa za su ci N125m a 2025