Halin da siyasar Sakkwatawa ke ciki

Lokaci bako ne, ya kan zo ya tafi. A shekarar 2014 da ta shigo aka fara ta hasashen mutanen da za su iya gadar Gwamnan Sakkwato na lokacin, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko tsakanin Jam’iyyar APC da PDP a karshe dai Barista Aminu Waziri Tambuwal ya gaje shi a zaben 2015. Shekara kwana yanzun kuma wata […]

Halin da siyasar Sakkwatawa ke ciki

Lokaci bako ne, ya kan zo ya tafi. A shekarar 2014 da ta shigo aka fara ta hasashen mutanen da za su iya gadar Gwamnan Sakkwato na lokacin, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko tsakanin Jam’iyyar APC da PDP a karshe dai Barista Aminu Waziri Tambuwal ya gaje shi a zaben 2015. Shekara kwana yanzun kuma wata 15 ne ya rage wata sabuwar gwamnati ta shigo, wasu sun fara kokorin raba gwamnan da kujerarsa a zaben 2019 yunkurin da nasara ko akasinta lokaci ne kadai zai iya fadinta bayan gudanar da zaben a 2019.

Aminiya ta fahimci cewa a jihar Sakkwato, Jam’iyar APC da PDP ne ke da karfi a jihar, wanda ya sanya siyasar ta tsaya tsakanin gidan tsofaffin gwamnonin jihar guda biyu, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa da Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko, hakan ya sanya ba wani gogaggen dan siyasa a yau, dake fadi a ji a jihar da ba daya daga cikin gidajen yake ba, kuma ba wata nasara da ake iya samu ta zabe sai an yi alaka da daya daga cikinsu. 

Wannan ne ya jefa Gwamna Aminu Waziri Tambuwal cikin kogin tunani da sanya wayon siyasa a wurinsa, a yau da yake gwamna sai ya janyo dukkan gidajen ya na alaka da su don ya fitar da na shi gidan siyasa. Matakin da bai yi wa wadanda suka kawo shi saman kujerar dadi ba, don adawarsu ta koma gaba, ba zai iya hade gidajen tare wuri daya, duk da shi ne gwamna a yanzu, wadannan abubuwan ne suka haifar da fara siyasar 2019 a jihar, kuma ta fito fili domin mafi yawan na kusa da shi sun fi aminta da ya yi tafiya daya da gidan siyasar Bafarawa, don  a tunaninsu ra’ayinsu ya fi tafiya da mutanen kuma ba za su iya dusashe su ba a matsayunsu na sabbin ‘yan siyasa, a lokaci daya suna kallon Wamakko a matsayin Bakaki da ya zama barazana ga tauraruwarsu da ta fara haske.

A yau jam’iyyun guda biyu sun dawo cikin siyasa gadan-gadan, domin ganin sun samu nasara a 2019, jam’iyyar PDP a jihar hoto ce don jagoran tafiyar, Bafarawa ya kashe adawa a jihar saboda alakarsa da Gwamna Tambuwal, ya sanya shi da makusantansa ba su sukar gwamnatin ko ta yi abin da suke gani ba daidai ba ne, saboda kawai ka da su taimaki siyasar Wamakko wajen neman gira suna kokarin rasa ido, domin  jiran samun dawo da gwamnan bangarensu da kamar wuya, ganin yadda gwamnan da Wamakko suka gwale masu son shiga tsakaninsu, cewa ba za su iya ba, suna tare tafiyar magaji da kanensa.

A halin da ake ciki a Sakkwato kisan da Bafarawa ya yi wa PDP ba za ta iya cin dan majalisar tarayya daya ba, ita kuma jam’iyar APC ta yi kokarin darewa gida biyu, yayin da wasu ke ganin gwamnan ya tsaya a jam’iyarsa da ya ci zabe komai zai faru kuwa, wasu na ganin ya tafi don kara alaka da wadanda ya fara sabuwar dangantaka da su, ganin da wuya Wamakko da yaransa su yafe wa Tambuwal kan alakarsa da Bafarwa, ganin shi ne mafi girman dan adawarsu da suka sani ko ya ya ne dai Tambuwal zai iya canja rawar daga nan har 2019.

Gwamna Tambuwal ya karbi ragamar jagoranci da kyakkyawan zato a kansa ganin shi matashi ne dan kasa da shekara 50 da ya rike majalisar wakilai ta kasa ba tangarda, amma kash! Hakan bai sanya ya tsaya ya natsu ya yi wa Sakkwatawa goma ta arziki ba, ya rika tafiye-tafiye marasa kan-gado da nisanta kansa da talakawa da kokarin alakanta kansa da siyasar kasa ya bar komai a zube, ganin talakawan jihar da kudi kadan kana iya saye imaninsu, su manta da duk gashin kumar da aka yi masu, ga shi kuma suna son shugaba Buhari kuma shi dan jam’iyyar masoyinsu ne, ko bai yi komai ba zai iya komawa saman kujerarsa ta gwamna, ko in Buhari ba zai yi takara ba ya nemi Shugaban kasa, tun da shi ke rike da karfin iko a jihar   ana iya kyale talakawa da ‘yan siyasa, sai lokacin zabe ya zo a fada masu yadda za su yi, tunda ba wani abin riko a wurinsu dole su yi yadda ake so, su yafe abin da aka yi masu a baya, tun da an cika su da alkalin daban-daban ko ba su gani a kasa ba za a cika zukatansu da tsammanin yi a gaba. 

A gwamnatin nan ne ake fitar da aikin hanya ta biliyoyin kudi a kwashe fiye da watanni baka ga an fara aiki ba, kuma bai hana a bayar da wani, ‘gwamnatin za a yi kenan’ Hakan ya sanya aka samu wasu dake ganin suna iya jayayya da gwamna su karbi ragamar a hannunshi su canja