Halin da ’yar wasa mata-maza Besse ta samu kanta
Besse Obot Bonuface, wata mata-maza ce ’yar wasan kwallon kafa ta kungiyar Ibom Angels ce. Ta shahara wajen wasan kwallo, sai dai kumaAllah Ya yi ta da halittar mazakunta da kuma na matunci, wato mata-maza ce. Duk da kasancewarta haka ta rungumi harkar wasan kwallon kafa. Kafin ta koma kungiyar Ibom Angels a jihar Akwa […]

Besse Obot Bonuface, wata mata-maza ce ’yar wasan kwallon kafa ta kungiyar Ibom Angels ce. Ta shahara wajen wasan kwallo, sai dai kumaAllah Ya yi ta da halittar mazakunta da kuma na matunci, wato mata-maza ce. Duk da kasancewarta haka ta rungumi harkar wasan kwallon kafa. Kafin ta koma kungiyar Ibom Angels a jihar Akwa Ibom, ta yi wa wadansu kungiyoyin wasa, da suka hada da Delta kueens a jihar Delta wadda kuma an gayyace ta buga wa babbar kungiyar kwallon kafa ta mata ta Nijeriya, wato kungiyar Falconet, a wata karawa da za su yi da kasar Chile a gasar wasan cin kofin mata matasa ’yan kasa da shekara 20, sai dai ta samu cikas, saboda wannan hali da take ciki, wanda y asanya aka dawo da ita gida.Awannan hirar da Aminiya ta yi da ita a Uyo ta bayyana yadda rayuwarta take a cikin wannan hali da kuma sauran matsaloli. Ga yadda hirar ta kasance:.
Aminiya: Ki gabatar mana da kanki?
Besse: Sunana Besse Obot Bonuface.
Aminiya: A ina aka haife ki, wadansu na cewa ke ‘yar asalin jihar Akwa Ibom ce?
Besse: A’a ba haka abun yake ba, ni dai an haife ni a garin Kalaba ne na jihar Kurosriba, daga can ne ma na dawo nan jihar Akwa Ibom da zama
Aminiya:Tun yaushe kika tsunduma cikin harkar wasan kwallon kafa?
Besse: na fara wannan harka ta kwallon kafa ce tun a shekarar 2005, kafin nan a shekara ta 2004 ina a makarantar samun horo akan kwallon kafa, wato Academy, a can Kalaba, na kuma fara yi wa kungiyar kwallon kafa ta Pelicans stars wasa a shekara ta 2004, daga baya kuma a shekara ta 2005 .na kama harkar kwallo gadan-gadan.
Aminiya: Shin ina gaskiyar magana an ce ana zargin cewa ke mata-maza ce?
Besse: Mhm! Gaskiya ce haka ne, ka san halin kuruciya ba za ka iya sanin halittar da aka yi ka ba, tunda ina yarinya ce ban san ciwon kaina ba sai daga bayan e na fahimci cewa a jikina ina da halittar matunci da kuma mazakunta gaba daya.
Aminiya: Ko hakan ya jefa ki cikin firgici da kuma rudani ko damuwa?
Besse: Sai daga baya ne da na fara girma hankali ya fara zuwa min na gane halin da nake ciki, kuma hakan sai na lura ba karamin kalubale ba ne a tare da ni, duk da kasancewa kamar yadda ka gani, ga dan kunne a kunnena, ina yin shigarmu ta mata, domin bangaren ’ya mace ya fi rinjaye a tare da ni. Lokacin nan ma ina a makarantar samun horon kwallo na fara gano hakan a lokacin da likitocinmu da unguwar zoma suka dauke mu ’yan wasa gaba daya za a yi mana gwaji, sai likita ya shaida mini cewa ga halin da nake ciki, kuma ma ba ni kadai ba ce har ma da wata ’yar uwata.
Aminiya: Kin ce ba ke kadai ba ce mata-maza a wannan kungiya, ina dayar?
Besse: dazu muna tare, amma ta fita kafin ka kirawo ni ta waya, ban san inda ta tafi ba.
Aminiya: Bayan da likita ya tabbatar maki da halin da kike ciki ya kike ji a jikinki, kina jin ke namiji ne ko ‘ya mace ?
Besse: Ni a lokacin ma ban san cewa ina da mazakunta ba, domin ni ko a jikina ban taba dauka cewa ni namiji ba ce, domin komai na ‘ya mace nake yi, kuma duk abun da ‘ya mace ke yi ni ma ina yi, hallitar mazakuntar ma ‘yar karama ce a jikin nawa. Ta haka dai na san halin da nake ciki.
Aminiya: Yaya rayuwa take kasancewa a gare ki?
Besse: [murmushi] Mhm! Ba zan iya yanke wa kaina hukuncin haka ba, sai dai in ce rayuwa a gare ni tana cike da kalubale da kuma damuwa matuka, idan na tuna cewa ina so ni ma wata rana in ga na mallaki iyali nawa na kaina, in yi aure in ga ni ma na haihu na samu magadana. Amma duk da haka rayuwa ta sai godiya ga Allah, domin b ani da wata matsala, sai dai ta yau da kullum da kowane dan Adam ke samunn kansa a ciki, ina kuma karawa da matukar hakuri da halayen mutane da nake cudanya da su, na daga irin kalaman da suke yi mini, sai dai in ji takaici abun in kawar da kai, a wadansu lokuta ma idan na daura zane ko na yi shigarmu ta mata na je wani wurin, haka mutane za su rika yi min cin fuska. Wannan abu ma ta kai har ya rika shafar kungiyoyi da muke karawa da su, idan suka samu labarin halin da nake ciki ba su yarda a sanya ni wasa .
Aminiya: Kin taba fuskantar tsangwama tsakanin al’umma ko ana nuna maki kyama?
Besse: Eh! kwarai abun zuwa-zuwa ne, a wadansu lokutan ana kyama ta, yayin da a wadansu lokutan kuma ba a nuna mini kyama, a duk lokacin da na fuskanci haka ta maza nakeyi kurum in hadiye fushina, sai in dake in yi mirsisi kamar ba ni ba.
Aminiya: Wata majiya ta shaida min cewa akwai wata kungiya mai zaman kanta ta yunkuro domin taimaka maki ki samu a yi maki aiki sai kuma aka ji shiru, meye gaskiyar maganar?
Besse: Mhm! (ta dan kada kai) Ba zan iya cewa ga sunan kungiyar ba, amma dai zan iya tunawa akwai wani mutum a shekara ta 2010 da ya yunkuro da magana kamar zai taimake ni ya nema mini taimakon kudi, har ma ya shaida min ya fara tuntubar wadansu mutane domin a yi mini gidauniya da za a yi min aiki in zama cikakkiyar mace, ko a ’yan kwanakin nan ma ya kira ni ta waya ya ce yana nan fa yana ci gaba da kokarinsa. A nawa tunani na dauka mutum ne ma wanda zai ce zai dauki nauyin aiki, amma sai ya buge min da kame-kame, ina da dan kudina a asusun ajiya Naira dubu 250, baya ga irin alkawarin taimaka min da ya yi, har ma ya karbi lambar asusun nawa, na kan je ma akai-akai ina dubawa ko an sako kudin, amma shiru. Akwai lokacin da ma na duba asusun nawa sai na ga kudin ciki ba su wuce Naira dubu 5 ba a ciki, daga nan sai na kirawo mutumin na tambaye shi yaya aka yi haka, sai ya ce d ani ai ya yi amfani da kudin ne wajen neman kudi. Daga nan sai na sallama, na karaya, na bar wa Allah ikonSa. Har yanzu dai ya ce da ni kada in fitar da tsammani, amma har yanzu da muke tattaunawar nan da kai ban sake jin duriyarsa ba.
Aminiya: Mu dawo kan kungiyar da kike yi wa wasa ta Ibom Angels, wane kokari mahukuntar kungiyar suke yi game da batun naki?
Besse: Ni dai tun daga lokacin da na zo jihar Akwa Ibom an rika ba ni shawara in kai kukana gare su, a lokacin waccan gwamnatin ce, amma tun da aka samu sauyin gwamnati babu wani mataki da aka dauka, sai dai ina fata shugabannin kungiyar za su taimaka mini su sanar wa gwamna. Da can na yi wa kungiyar kwallon kafa na Delta kueens wasa, daga nan ne kuma na dawo nan Ibom Angels da yi masu wasa, yanzu kuma daraktan kungiyar ne yake lallashina tare da shan alwashi za su sanya gwamna ya yi wani abu akai, ina ji a jikina shi da matarsa za su iya taimakona, duk da yawan tuna masu da nake yi suna ce da ni ki yi hakuri muna sane da ke. A wancan shekarun baya ke nan a 2004, amma yanzu kuma da aka kafa sabuwar hukumar wasanni ta jiha na yi farin ciki, domin shugaban kungiyar tamu na yanzu daga kauye daya muka fito, dan garinmu ne, ya kuma dauke ni tamkar ’yar da ya Haifa, shi ma ya aika min na je ya ji ta bakina da kuma samun bayanan likitocina kuma ya nuna min sai inda karfinsa ya kare wajen shiga da fita na a shawo kan matsalata.
Aminiya: A karshe, wane kira za ki yi wa hukumar wasanni ta kasa NFF da kuma ta jihar Akwa Ibom domin a taimaka maki ?
Besse: Mhm ! rokon da zan yi wa NFF da kuma hukumar wasanni ta jihar Akwa Ibom da ma sauran masu hannu da shuni ’yan Nijeriya, shi ne, su taimake ni domin in fita daga cikin halin da na samu kaina, saboda ni ma ina so in yi aure in haihu, ko da kuwa aikin da za a yi mini zai mayar dani ko wane jinsi na namiji ko na mace, bukatata ita ce ni ma in ga na yi aure na haifa na samu mai gadona Allah Ya sa mu dace!