Halin hakuri da kauna
Godiya ta tabbata ga Ubangiji Allah Mai iko duka. Barkanmu kuma da sake saduwa a wannan mako. A wannan makon za mu yi nazari a kan muhimmancin hakuri a rayuwar mai bin Almasihu. Ba sai an gaya maka cewa a yau mutane da dama sun zama marasa hakuri ba; gaggawa domin samun biyan bukata ta […]
Godiya ta tabbata ga Ubangiji Allah Mai iko duka. Barkanmu kuma da sake saduwa a wannan mako.
A wannan makon za mu yi nazari a kan muhimmancin hakuri a rayuwar mai bin Almasihu.
Ba sai an gaya maka cewa a yau mutane da dama sun zama marasa hakuri ba; gaggawa domin samun biyan bukata ta kowane hali ba tare da tunanin ko kana cin zarafin wani ba, rashin hakuri kan sa mutane yin kisa, kwace, fashi, sata, zalunci don neman biyan bukata. Wadansu ma har su shiga halin sayar da jariran da suka haifa, ko su sace na wani don neman dukiya ko samun mukami a gaggauce. Mene ne ke kawo irin wannan? Littafi Mai tsarki na cewa “kauna tana sa hakuri da kirki. kauna ba ta sa kishi, ba ta yin kumbura. kauna ba ta sa daga kai ko rashin kara, kauna ba ta sa son kai, ba ta jin tsokana, ba ta riko. kauna ba ta sa yin farin ciki da mugunta, sai dai da gaskiya. kauna tana sa daure wa a cikin kowane hali, da ban-gaskiya a cikin kowane hali, haka kuma sa zuciya a cikin kowane hali da jimiri a cikin kowane hali” (1Korantiyawa 13:4-7). Rashin kauna kan haifar da son kai da mugunta da rashin hakuri wadanda za su kai mutum ga hallaka na har abada.
Kada kuma wani ya samu dalilin cewa ai ba ni da irin wannan hali a rayuwata, yin fushi na daya daga cikin irin wannan hali, mu duba dai a duk lokacin da mutum ya fusata da wani ko wani abu, za ka ga mutane na kokarin cewa; Ka yi HAkURI! Sai HAkURI! Idan har ya yi hakuri sai ka ga cewa an samu salama da zaman lafiya da kauna, amma idan bai yi hakurin ba, sai ka ga fushi ya kai shi ga yin kisa, ko wata barna da za ta kawo matsala. “Mutum mai kamewa yana da hikima, amma mai zafin rai yana bayyana wautarsa a fili.” (Karin Magana 14: 29). Ashe yin hakuri kan magance irin wannan hali. Shi ya sa hakuri na daya ga cikin albarkar ruhu da ya kamata mu zama muna da shi a koyaushe a cikin rayuwar nan da Allah Ya ba mu. Littafi Mai tsarki na cewa: “Ya fi kyau ka zama mai hakuri da ka zama mai karfi. Ya fi kyau ka iya mallakar kanka fiye da mallakar birane.” (Karin Magana 16:32).
Yin hakuri cikin zamaninmu na yanzu ba abu ne da ke da sauki ba, mutane na da halin tsokana idan har suka ga kana kokarin neman zaman lafiya. Suna yin haka ne don ba su san Ubangiji Allah ba, da sun san Shi, za su bi abubuwan da Ya fadi cikin LittafinSa Mai tsarki. Luka 10:25-28; “Sai ga wani masanin Attaura ya tashi tsaye yana gwada shi, ya ce, “Malam,me zan yi in gaji rai madauwami?” Yesu ya ce musu, “Me yake rubuce a Attaura? Yaya kake karantawa?” Sai ya amsa ya ce, “Ka kaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka da dukan ranka da dukan karfinka da dukan hankalinka. Ka kuma kaunaci dan uwanka kamar kanka.” Yesu ya ce masa, “Ka amsa daidai. Ka rika yin haka, za ka rayu.”
Sanin Ubangiji Yakan sa ka kaunace Shi da dukan zuciyarka da dukan ranka da dukan karfinka da dukan hankalinka, yin haka kuma zai sa ka kaunaci dan uwanka kamar kanka. kaunar dan uwanka kuma zai sa ka zama da hakuri, inda aka samu hakuri kuma a nan za samu salama da farin ciki da kauna. “Saboda haka, sai ku dauki halin tausayi da kirki da tawali’u da salihanci da hakuri, idan ku zababbu ne na Allah, tsarkaka, kaunatattu.” (Kolosiyawa 3:12)
Ban da rashin hakuri da juna, wadansu mutane a yau na nuna rashin hakurinsu ga Ubangiji Allah, ba su da hakurin jirar lokacin da Ubangiji Ya sa abubuwa su faru a rayuwansu. Son kai da kishin juna sun mamaye tunaninsu, idan makwabcinsu ya gina gida ko ya samu abin hannu, sai ka ga cewa su ma suna son su samu wannan abin ko ta wane hali. Ba sa tunanin mika damuwarsu ko bukatunsu ga Allah Mai biyan bukatar kowa da kowa. Allah kadai ne Ya san zuciyar mutum, Shi Ya san jiya Ya san yau da kuma nan gaba. Ubangiji ba Ya jinkirta alkawarinSa, yadda wadansu suka dauki ma’anar jinkiri, amma mai hakuri ne a gare ku, ba Ya so kowa ya hallaka, sai dai kowa ya kai ga tuba. (2 Bitrus 3:9).
Me zai hana ka dogara ga Mahalicinka wanda Ya san komai da komai don biyan bukatunka? Ba a rana daya aka hallice mu ba, ba kuwa kamanni daya muka zo da shi ba, haka nan lokutan da Ubangiji Allah Ya sanya mana sun bambanta, rashin sanin cewa Ubangiji Ya san komai bisa rayuwarmu kan sa mutum ya zama mara hakuri, shi ya sa za ka ga mutane na zuwa wurin kowane mutum da ya kira kansa fasto, ko gidan addu’a domin neman biyan bukatan kansu (dukiya, aure, haihuwa, gida, mota da sauransu). Amma ba don neman sanin Ubangiji ba, domin idan har ka san Ubangiji Allah kana kuma kaunarSa kamar yadda Ya fada a cikin maganarSa babu shakka za ka bi tafarkinSa kuma za ka zama mai hakurin jiran nufinSa bisa rayuwarka.
Sai mu lura, kada mu bar rashin hakurinmu ya sa mu gaba da Ubangiji da kuma ’yan uwanmu, mu roki Ubangiji Ya cika mu da albarkar ruhunSa ta kauna don mu zama masu hakuri da nufinSa da juna kuma. Kamar yadda Manzo Bulus ya rubuta; “Don haka, ni dan sarka saboda Ubangiji, ina rokonku ku yi zaman da ya cancanci kiran da aka yi muku da matukar tawali’u da salihanci da hakuri, kuna jure wa juna saboda kauna.” (Afisawa 4:1,2)
“Allah Mai ba da hakuri da ta’aziyya, Ya ba ku zaman lafiya da juna bisa halin Almasihu Yesu.” (Romawa 15:5), amin.