Halin Kirista (1)

Da farko ina nuna godiyata ga Sarki Allah wanda a cikin ikonSa ne nake isar da sakonSa ga al’umma, bari iko da girma da daukaka su ci gaba da kasancewa a gare Shi. A wannan mako zan yi magana ne dangane da hali irin na Kirista, domin an kai wani matsayi ko lokaci da wadansu […]

Halin Kirista (1)
Halin Kirista (1)

Da farko ina nuna godiyata ga Sarki Allah wanda a cikin ikonSa ne nake isar da sakonSa ga al’umma, bari iko da girma da daukaka su ci gaba da kasancewa a gare Shi.
A wannan mako zan yi magana ne dangane da hali irin na Kirista, domin an kai wani matsayi ko lokaci da wadansu Kiristoci da dama ke tunanin mafita musamman idan aka yi la’akari da irin abubuwan da ke aukuwa a wannan duniya.
Ita dai wannan kalma ta Kirista kamar yadda na saba bayyanawa suna ne da ake kiran mabiya Almasihu da shi, kuma ta samo asali ne tun a zamanin Almasihu, ba kuma wani abu ne ya sa ake kiran mabiyan Almasihu da wannan suna ba illa yin la’akari da yadda suke tafiya tare da Almasihu da kuma yadda suke gudanar da komai ta hanyoyin da ke faranta wa Almasihu rai.
Wani abin mamaki a yau duk da ikirari da tinkahon da muke yi da sunan Almasihu da dama daga cikinmu sun kauce daga bin sahu ko gurbi da halayya irin na Almasihu.
Mafi yawanmu da ke tinkaho da Almasihu a wannan lokaci mun kauce nesa daga maganar Ubangiji da ke rubuce cikin LittafinSa Mai Tsarki (Baibul), za kuma mu iya gano haka ne sakamakon yadda yawancinmu muka koma ga dogara da kanmu kacokan, ba mu barin Ubangiji Ya jagorancemu a kan duk wani abin da muka sanya a gaba. Ba mu cika manufofinsa kamar yadda Ya umurce mu, inda muka sanya gaba da kiyayya da ramuwa da son kai da rashin tausayin juna da cin rashawa da shaye-shaye da zinace-zinace da rantsuwar karya da fahari da sauransu da dama fiye da son Almasihu a cikin zukatanmu.
An kai matsayin da Kiristoci suka koma ga dogara kacokan ga karfin tuwo da hikima da basirar da suke ganin suna da ita, sun manta batun kaurace wa ayyukan assha balle har su yi tunanin cewa addu’a ita ce mabudin hanyar magance kowace irin damuwa.
Kamar yadda na bayyana a baya, a irin wannan lokaci da abubuwa ke aukuwa a sassa daban-daban a fadin duniya, kamata ya yi kowa ya gyara halayensa, mu tuba daga zunubanmu, mu koma ga aikata adalci maimakon mugunta, mu daina barin duk wani abu da ya kasance abin ki ko kyama ga Ubangiji ya kasance a tsakaninmu. Mu kasance masu kauna da tausayin juna, mu daina yaudarar kanmu ta hanyar amsa sunan Kirista ba tare da yin aiki da maganar Ubangiji ba, mu daina daukar wani da kima fiye da wani wai don ya fi wancan hali ko matsayi. Matanmu su daina sanya kayayyakin da ke fidda tsiraicinsu, shugabanninmu musamman na majami’u su kasance da tsarki, kada su maida hankali ga yadda za su samu dukiya, yayin da matan da mazajensu suka rasu na tunanin abincin da za su ci koda na rana daya. Mu daina amfani da sunan Ubangiji muna zamba ko danne hakkin wani, sannan mu juyo zuwa ga Ubangiji muna rokonSa ta hanyar addu’o’i, Shi kuma da yake Yana da jinkai da tausayi sai ya manta da zunubanmu da sauran laifuffukanmu, ya maido da wanzuwar zaman lafiya a kasa tamkar babu wani abu na rashin jin dadi ko tashin hankalin da ya taba aukuwa.
Mu tuna da abin da ya faru da mutanen Saduma da Gwamrata wadanda Ubangiji Ya nemi koda mutum goma masu tsarki a tsakaninsu don Ya gafarta musu, amma babu lamarin da ya sanya Shi halakar da su. Haka kuma yake a zamanin Nuhu inda ya ci gaba da shelar bisharar tuba, maimakon haka sai aka koma ga yi masa ba’a kafin su ankara ruwa ya halakar da su.
Don haka babu wani abin da ya kamata Kirista ya yi a irin wannan lokaci da duniya ke cike da rudani da ya wuce tuba daga zunubi kamar yadda Esther ta bukaci ’ya’yan Isra’ila da yi a lokacin da suke fuskantar matsi.
Esther ta fara da bukatar Isra’ilawa su gudanar da azumin kwana uku a jere ba ci ba sha, daga su har dabbobinsu sannan ita da kanta ta fuskanci Sarki don nema musu ahuwa.
Kamar yadda ya ce a rubuce cikin Littafi Mai tsarki (Baibul) mutum daya ne kacal ya shirya makarkashiyar da ta nemi janyo daukar matakan halakar da ’ya’yan Isra’ila, ammamaimakon su dauki fansa ta hanyar shirya tasu makarkashiyar, sai suka sanar da Esther ganin cewa tana tare da Sarki.
Jin wannan magana ke da wuya sai Esther ta bukace su su gudanar da wannan azumi, sannan ta fuskanci Sarki duk da cewa ba ranar da ya kamaci a gan shi ba ne, amma ta bada gaskiya cewa Ubangiji Yakan magance kowace irin damuwa idan har al’ummarSa suka daidaita al’amuransu ta yadda za su faranta masa rai.
Bayan kammala wannan azumi, sai Esther ta doshi fadar Sarki, to shi Sarkin yana da wata al’ada da idan har bai kira mutum ba ya shiga fadarsa sai ya ki daga sandarsa sama idan fadawa suka ga haka sai a kame mutumin a yi masa hukuncin kisa.
Amma da Esther ta shiga fadar, Sarki ya ganta sai ya mika mata sanda da ke nuni da alamun an marabce ta, Sarkin bai tsaya nan ba, ya fara da tambayarta abubuwan da ke tafe da ita sannan yayi alkawarin ba ta koda rabin mulkinsa ne.
Esther ta bayyana masa dalilan zuwanta shi kuma ya gaggauta gudanar da binciken da ya kai ga halaka wanda ya shirya wa Isra’ilawan makarkashiya, a takaice dai reshe ya juye da mujiya.
Don haka wannan lokaci ko hali da duniya ke ciki lokaci ne da ya kamaci Kirista ya nuna halinsa a fili wanda Almasihu ya koya mana maimakon tunanin daukar matakai na kashin kai.