Halin matsin da ake ciki jarrabawa ce daga Allah – Imam Aliyu

Limamin Masallacin Juma’a na ’Yan Doya da ke garin Jos a Jihar Filato, Imam Aliyu Aliyu ya ce halin matsin da al’ummar kasar nan suke fama da shi na rashin kudi wata jarrabawa ce daga Allah. Imam Aliyu Aliyu ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Jos, inda ya ce […]

Halin matsin da ake ciki jarrabawa ce daga Allah – Imam Aliyu
Halin matsin da ake ciki jarrabawa ce daga Allah – Imam Aliyu

Limamin Masallacin Juma’a na ’Yan Doya da ke garin Jos a Jihar Filato, Imam Aliyu Aliyu ya ce halin matsin da al’ummar kasar nan suke fama da shi na rashin kudi wata jarrabawa ce daga Allah.
Imam Aliyu Aliyu ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Jos, inda ya ce jama’a su yi hakuri da halin rashin kudin, kuma su sani Allah ne Yake kawo arziki kuma Yake kawo talauci.
“Kamar yadda aka sani ne yadda dadi ba ya dauwama, haka talauci ma ba ya dauwama. Wannan gwamnati ta Muhammadu Buhari muna yi mata kyakyawan zato, in Allah Ya yarda bayan wannan ’yar wahala dadi zai zo abubuwa su inganta. Saboda haka jama’a su yi hakuri su ci gaba da yi wa gwamnatin addu’ar alheri,” inji shi.
Ya ce da ma duk lokacin da mutane suka yi hasashen alheri, sai Allah Ya jarrabe su, don haka su yi hakuri su ci gaba da yin addu’o’i idan suka yi haka alheri zai biyo baya.
Ya yi kira ga al’ummar kasar nan kan su rike gaskiya da amana domin rashin rike su ne ya jawo wa kasar nan rashin zaman lafiya da talauci da yamutsin da ake fama da su.