Halin Ni-’Ya-Su: Wa Ya Kamata Ya Jikan ’Yan Gudun Hijira?
Me ya sa mawadata ba sa tallafa wa ’yan gudun hijira?
Wasu ‘Yan gudun hijira
Hoto daga UNICEF
Mummunan halin da ’yan gudun hijira ke ciki a sansanoni daban-daban a wasu sassan Najeriya ba bakon abu ba ne.
Abin da kan zama bako shi ne samun wani mawadaci ko kungiyar mawadata su tallafa wa wadannan mutane.
A wannan shiri na Daga Laraba mun duba abin da ya sa masu hannu da shuni ba su cika taimaka wa wadannan bayin Allah ba.