Halittar kaina ta sa ba ni da masoyiya – Saurayi

Wani saurayi mai shekara 22 mai suna Anshu Kumar daga Jihar Punjab ta kasar Indiya, wanda Allah Ya yi wa halittar katon kai da hakan ya sa yake da kananan idanu kuma sumarsa bata fitowa ya koka kan yadda fasalin halittarsa ya hana shi samun budurwa. Anshur wanda lebura ne ya fada kangin soyayya kuma […]

Halittar kaina ta sa ba ni da masoyiya – Saurayi

Wani saurayi mai shekara 22 mai suna Anshu Kumar daga Jihar Punjab ta kasar Indiya, wanda Allah Ya yi wa halittar katon kai da hakan ya sa yake da kananan idanu kuma sumarsa bata fitowa ya koka kan yadda fasalin halittarsa ya hana shi samun budurwa.

Anshur wanda lebura ne ya fada kangin soyayya kuma yana son yin aure, sai dai yana bukatar a  yi masa tiyata don a rage girman kan nasa, inda a cewarsa girman da kan ke da shi ne ya sa ’yan mata ke gudunsa.

Ana dai yi wa Anshu Kumar lakabi da ‘Alien’ wato bakuwar halitta saboda girman da kansa ke da shi. Binciken likitoci ya gaza gano dalilin da ya sa yake da irin wannan halitta.

A cewar rahoton, sauran gangan jikin Anshu ba su da girma kuma bai fitar da suma a kansa.

Anshu dai yana samun albashin Fam 50 (kimanin Naira dubu 23 da 444) wanda hakan ya sa ba ya da kudin da zai iya ganin kwararren likita don binciko larurar da take damunsa.

Sai dai ya ce yana fata gwamnati za ta tallafa masa don yin maganin abin da ke damunsa, saboda ya ci gaba da rayuwa kamar kowa.

Anshu ya ce,  “A koyaushe ina sha’awar in ga ina yawo da yaran makwabtana, amma akasari na fi, yawo ni kadai. Kullum sai na je kamfanin da nake aiki inda nake kwashe sa’o’i 9 a wajen aiki.”

Ya kara da cewa, “Ina fatan zan samu sauki nan ba da jimawa ba, don ni ma in samu in yi aure in yi iyali kamar kowa. Wannan shi ne babban burina, duk inda na shiga jama’a ana kirana mai wata halitta daban, suna yi min kallon kamar ni ba jinsin kasar ba ne daga wata kasa nake daban don haka suke kirana ‘alien.’ Saboda girman da kaina ke da shi.”

A lokacin da iyaye na suka haife ni da irin wannan halittar sun tuntubi likita, amma sai aka ce masu ai wannan halittar ba tada magani.

 

 

Hamas da Isra’ila sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

HOTUNA: Yadda aka yi bikin tunawa da mazan jiya a faɗin Nijeriya

Sanusi zama daram kuma Sarki ɗaya tilo a Kano — Falana

An rantsar da Shugaban Mozambique Daniel Chapo