Hamani Tidjani da ake zargi da jagorantar satar motoci ya mutu a kurkuku
Mutumin nan da ake zargi da satar motoci a tsakanin iyakokin Najeriya da makwabtanta, Hamani Tidjani, ya rasu a kukurku bayan ya shafe shekara 10 yana tsare.Jaridar PREMIUM TIMES ta fara bayyana mutuwar Tidjani, wanda ake zargi da shirya sace-sacen motoci a kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar Benin, wanda aka ce ya cika da karfe […]

Mutumin nan da ake zargi da satar motoci a tsakanin iyakokin Najeriya da makwabtanta, Hamani Tidjani, ya rasu a kukurku bayan ya shafe shekara 10 yana tsare.
Jaridar PREMIUM TIMES ta fara bayyana mutuwar Tidjani, wanda ake zargi da shirya sace-sacen motoci a kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar Benin, wanda aka ce ya cika da karfe 9:00na safiyar Lahadin da ta gabata.
Kakakin Hukumar Gidan Yarin Legas Biyi Jeje, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa Mista Tidjani ya hadu da ciwon shanyewar barayin jiki tun wata tara da suka gabata. “Kuma mun ba shi kula sosai, amma ciwonsa ya ci gaba da tsananta. Kuma mun sanar da gwamnatin Jihar Legas, amma sai suka dauka muna kambama rashin lafiyar ce,” inji Jeje.
Ya ce a karshe cikin watan Disamba jami’an gwamnatin Legas sun ziyarci Mista Tidjani domin tabbatar da rashin lafiyarsa. “Mun dauka za su dawo da likitocinsu, amma har zuwa safiyar nan ba su zo ba,” inji shi.
A watan Saumban 2003 ne aka kama Tidjani kuma yana fuskantar shari’a ce a gaban Mai shari’a Sybil Nwala na Babbar Kotun Legas kan zarge-zarge uku da suka hada da hada baki don aikata fashi da makami da fashi da makami da kuma ajiye kayan sata.
Lokacin da jaridar ta tunubi lauyansa J. H. Bashir ya ce ya nufi kurkuku kirikiri ne domin tabbatar da halin da ake ciki. “Idan gaskiya ce an aikata rashin adalci a fahimtarmu, kuma alhaki na kan gwamnatin Legas da gwamnatin Obasanjo,” inji shi.