Hamas da Isra’ila sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza
Cimma wannan yarjejeniyar na zuwa ne yayin da yaƙin na Isra’ila da Hamas ya doshi cika watanni 15 da barkewa.
Kafofin watsa labarai da dama a faɗin duniya sun ruwaito cewa an cimma matsayar tsagaita wuta a faɗan da ake gwabzawa tsakanin Hamas da Isra’ila.
Firaministan Qatar, Mohammed ben Abdelrahmane Al-Thani wanda ke shiga tsakani a tattaunawar, ya gana da tawagogin Hamas da na Isra’ila daban-daban a birnin Doha.
- HOTUNA: Yadda aka yi bikin tunawa da mazan jiya a faɗin Nijeriya
- Sanusi zama daram kuma Sarki ɗaya tilo a Kano — Falana
Jim kaɗan bayan ganawar, firaministan ya ce an warware ’yar taƙaddamar da ta so hana ruwa gudu a tattaunawar, amma yanzu ya ce an samu daidaituwar baki.
Yarjejeniyar dai ta tanadi dakatar da buɗe wuta nan take, tare da sako mutanen da Hamas ke garkuwa da su a Gaza.
Mataki na farko na yarjejeniyar shi ne cikin kwana 42 dakarun Isra’ila za su janye daga yankuna masu yawan al’umma na Gaza.
Yarjejeniyar ta ƙunshi cewa Hamas za ta miƙa wa Isra’ila mutanen da ake garkuwa da su a Gaza, yayin da ita ma Isra’ila za ta miƙa wa Hamas wasu Falasɗinawa da ke tsare a Isra’ilar.
Kazalika, Shugaban Kwamitin Hulɗa da Ƙasashen Waje a Majalisar Dattawan Amurka, Sanata Jim Risch ya bayyana labarin yayin wani zama na tantance Sanata Marco Rubio, wanda Zaɓaɓɓen Shugaba Donald Trump ya zaɓa don zama Sakataren Harkokin Waje.
Matakin cimma wannan yarjejeniyar na zuwa ne yayin da yaƙin na Isra’ila da Hamas ya doshi cika watanni 15 da barkewa.