Hamas ta ɗora alhakin harin da Isra’ila ta kai a kan Amurka
Wannan ya tona asirin ƙaryar da suke yi na iƙirarinsu kan damuwa da kawo ƙarshen yaƙin.

Ƙungiyar Hamas ta ɗora alhakin hare-haren da Isra’ila ta ƙaddamar yau Talata a Zirin Gaza kan Amurka.
A wata sabuwar sanarwa da Hamas ta fitar, ta ce Amurka ce ke da “alhakin kisan gillar” da aka yi a Gaza bayan da ta bayyana cewa Isra’ila ta shaida wa Amurka shirinta na kai hare-haren gabanin kai harin.
- Majalisar Wakilai ta amince da ƙudirin dokar haraji
- Wike ya ƙwace filin Sakatariyar PDP da ke Abuja
- Isra’ila ta ƙaddamar da sabon hari a Zirin Gaza
Sanarwar ta ce hakan ya “tona asirin ƙaryar da suke yi na iƙirarinsu kan damuwa da kawo ƙarshen yaƙin.
“Muna buƙatar ƙasashen duniya su ɗauki matakin gaggawa na kama masu aikata laifukan yaƙi da masu goya musu baya,” in ji Hamas.
A gefe guda kuma kafar yaɗa labarai da ke da alaƙa da Hamas, mai suna Filastin, ta ce an kashe jami’an gwamnatin Hamas huɗu a hare-haren Isra’ila.
Hazalika, shugaban hukumar lafiya da Hamas ke jagoranta, Munir al-Barsh ya ce mutane fiye da 660 aka jikkata a hare-haren, kuma wasu da dama na ƙarƙashin ɓaraguzai.
Majiyoyin kiwon lafiyar Gaza sun shaida wa gidan Talabijin na Al Jazeera cewa fiye da mutane 400 ne aka kashe, kuma mafi yawancinsu mata da ƙananan yara da kuma dattawa.
Harin wanda ke nuna kawo ƙarshen yarjejeniyar zaman lafiyar da aka ƙulla tsakanin Isra’ila da Hamas a watan Janairu, Isra’ila ta ce ta ƙaddamar da shi ne bayan da Hamas ta ƙi sako ragowar mutanen da ta yi garkuwa da su.
Wani jami’in Isra’ila ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP cewa, za su ci gaba ta kai hare-hare har sai sun kawar da shugabannin Hamas da gine-ginensu da kuma kayan aikinsu.
Fadar White House ta bakin sakatariyar yaɗa labaranta Karoline Leavitt, ta ce sai da Isra’ila ta sanar da ita, kafin ɗaukar matakin kai harin.
“Isra’ila ta sanar da gwamnatin Trump da fadar White House kan harin da suka kai Gaza a daren yau, kamar yadda shugaba Trump ya bayyana Hamas da Houthis da kuma Iran, da ke neman addabar Isra’ila har ma da Amurka, za su ɗanɗana kuɗarsu.”