Hamas ta rusa gwamnatinta da ke mulkin Gaza kusan shekara 20

An ɗauki matakin ne domin kawar da duk wata hujja da Isra’ila ke amfani da ita wajen ci gaba da kai hare-hare a Gaza.

Hamas ta rusa gwamnatinta da ke mulkin Gaza kusan shekara 20

Ƙungiyar Hamas ta sanar da rusa hukumar da ta riƙa tafiyar da harkokin mulki a Zirin Gaza na kusan shekara 20, lamarin da zai bai wa wani kwamitin ƙwararru na farar hula damar gudanar da mulkin yankin.

Matakin ya nuna wani gagarumin sauyi na siyasa daga ɓangaren Hamas, wadda ta karɓe ikon Gaza tun shekara ta 2007 bayan ta kori jam’iyyar Fatah, sakamakon nasarar da ta samu a zaɓen ’yan majalisa na shekarar 2006.

Tun bayan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Hamas da Isra’ila ta fara aiki a watan Oktoban bara, ƙungiyar ta sha bayyana cewa a shirye take ta janye daga gudanar da harkokin yau da kullum na gwamnati, sai dai batun kwance ɗamarar mayaƙanta na ci gaba da zama babban ƙalubale.

Shugaban ofishin yaɗa labarai na Hamas a Gaza, Ismail al-Thawabta, ya ce shugaban kwamitin gaggawa na gwamnatin Gaza ya yanke shawarar rusa kwamitin domin sauƙaƙa miƙa ragamar mulki ga Kwamitin Ƙasa na Gudanar da Mulkin Gaza (NCAG).

An kafa NCAG, mai hedikwata a Alƙahira, ne ta Majalisar Zaman Lafiya ta Board of Peace, wata hukuma da Shugaban Amurka Donald Trump ya kafa lokacin da aka cimma yarjejeniyar tsagaita wutar Gaza a watan Oktoban 2025.

Kakakin Hamas, Hazem Qassem, ya ce ƙungiyar ta ɗauki wannan mataki ne domin kawar da duk wata hujja da Isra’ila ke amfani da ita wajen ci gaba da kai hare-hare a Gaza.

Sai dai shugaban NCAG, Ali Shaath, ya ce kwamitinsu a shirye yake ya karɓi ragamar gudanar da mulki da zarar an samar masa da isassun kayan aiki da albarkatun da ake buƙata.

Ya ce nasarar kwamitin za ta dogara ne kan kasancewar hukuma guda, doka guda da kuma rundunar tsaro guda ƙarƙashin wannan hukuma.

A nata ɓangaren, Isra’ila ta sake nanata cewa dole ne Hamas ta miƙa makamanta gaba ɗaya kafin a aiwatar da cikakken shirin zaman lafiya.

Ministan Harkokin Wajen Isra’ila, Gideon Saar, ya ce ƙasarsa na dagewa kan aiwatar da shirin Trump, wanda ya haɗa da kwance ɗamarar Hamas da sauran ƙungiyoyin masu riƙe da makamai a Gaza.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi maraba da matakin Hamas, inda kakakin Babban Sakataren MDD ya ce matakin zai kasance mai amfani idan zai taimaka wajen aiwatar da ƙudurin Kwamitin Tsaro, kare fararen hula da kuma ba da damar kai agajin jin ƙai ba tare da tangarɗa ba.

Sai dai wasu masu sharhi sun bayyana matakin a matsayin na siyasa kawai.

Masanin harkokin siyasa daga Gaza, Mkhaimar Abusada, ya ce matakin “wata alama ce ta siyasa kawai,” domin har yanzu Hamas ba ta amince da kwance ɗamararta ba, wanda shi ne babban abin da ke hana cimma matsaya.

Wani mazaunin Gaza, Hussam Majed, ya kuma ce sanarwar ba ta canja komai ba, yana mai cewa Hamas har yanzu ita ce ke iko da mashigai, ma’aikatu da harkokin tsaro a yankin.

A halin yanzu, tattaunawar da ake yi a Alƙahira tsakanin Hamas da sauran ƙungiyoyin Falasɗinawa na ci gaba da neman warware saɓanin da ke akwai, musamman kan mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta.

Duk da yarjejeniyar tsagaita wutar, rikici na ci gaba a Gaza, inda Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta ce an kashe Falasɗinawa fiye da 1,070 tun bayan fara aiki da yarjejeniyar, yayin da sojojin Isra’ila suka ce sun rasa dakaru biyar da kuma wani ma’aikacin kwangila guda a wannan lokaci.