Hamas ta saki wasu Amurkawa da ta yi garkuwa da su — Isra’ila

Akwai akalla mutum 200 da har yanzu Hamas din ke rike da su.

Hamas ta saki wasu Amurkawa da ta yi garkuwa da su — Isra’ila

Gwamnatin Isra’ila ta ce Hamas ta saki wasu Amurkawa biyu a ranar Juma’a wadanda take zargin suna daga cikin mutanen da kungiyar ke rike da su tun bayan harin da Hamas din ta kai na ba-zata a Isra’ila makonni biyu da suka gabata.

Amurkawan wadanda suka hada da wata mata da ‘yarta matashiya wadanda asalinsu ‘yan Isra’ila ne, na daga cikin mutanen farko da aka sako.

Akwai akalla mutum 200 da har yanzu Hamas din ke rike da su kamar yadda Muryar Amurka VOA ya ruwaito.

Hamas ta ce ta mika mutanen biyu, Judith da kuma Natalie Raanan ga Gwamnatin Qatar bisa dalilai da suka shafi lamari na jin-kai.

Bayanai sun ce Hamas ta yi garkuwa da matar da kuma ’yarta ce a Kibbutz Nahal Oz, da ke Kudancin Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken ya yi lale marhabin da sako Amurkawan.

“Har yanzu akwai wasu Amurkawa akalla goma da ba a san inda suke ba, mun kuma san cewa wasu daga cikinsu Hamas na rike da su hade wasu mutum akalla 200,” in ji Blinken.

Sauran ‘yan uwan wadanda ake rike da su sun nuna farin cikinsu ga wannan sabon al’amari suna masu kira da su ma a saki nasu ‘yan uwan.

Hakan na faruwa ne yayin da Shugaban Amurka Joe Biden ya mika bukatar neman dala biliyan 61.4 ga majalisar dokokin kasar don bai wa Ukraine a matsayin tallafi a yakin da Rasha ke yi da ita.

Tallafin na dauke da wani kaso na biliyoyin daloli da za a samar da makaman soji da ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon za ta mika wa Ukraine da kuma tallafawa kasar a fannin tattalin arziki da ‘yan gudun hijirar Ukraine da ke zaune a nan Amurka.

Babu dai tabbacin ko majalisar dokokin Amurkar za ta amince da wannan bukata ta Biden wacce za ta ci akalla jimullar dala biliyan 105, ciki har da wani kaso da za a ware wa Isra’ila da kuma samar da tsaro akan iyakar Amurka.

Majalisar Wakilan Amurka na cikin wani yanayi na rudani yayin da ‘yan Republican da ke da rinjaye suka gaza zaban sabon Kakakin majalisar.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan