Hamas za ta sako mutanen da ɗauke a Isra’ila —Netanyahu
Kungiyar Hamas dai ta bayar da tabbacin cika sharudan yarjejeniyar, amma an samu rabuwar kai tsakamin ministocin Isra’ila kan batun
Fira Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya sanar a safiyar ranar Juma’a cewa kungiyar Palasdinawa ta Hamas za ta saki rukunin farko a mutanen da ta yi garkuwa da su daga Isra’ila.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ba da rahoton cewa Netanyahu ya ce Hamas za ta sako su ne a ranar Lahadi a wani bangare na yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla ranar Laraba tsakanin Hamas da kasarsa.
A safiyar ofishin Netanyahu ya ba da tabbacin samun amincewar Majalisar Tsaron Isra’ila da yarjejeniyar kafin zaman majalisar zartaswar da zai biyo baya a ranar.
Idan yarjejeniyar da aka kulla ta yi nasara, Isra’ila da Hamas za su dakatar da yake-yaken da ya mayar da Zirin Gaza kufai.
- Matatar Dangote ta kara farashin fetur zuwa N955
- Sun kashe yaron da suka sace bayan neman fansar N25m
- CP Hauwa Ibrahim: Bakanuwar farko da ta zama Kwamishinar ’yan sanda
Akalla Palasdinawa fararen hula 46,000 ne Isra’ila ta kashe a Gaza, yawancinsu mata da kananan yara da tsofaffi, baya da tilasta wa miliyoyin mazauna gudun hijira a yankin mai mazauna miliyan 2.3.
Fira Minista Netanyahu ya ce majalisar zartarwa Isra’ila za ta tattauna domin amince da yarjejeniyar zaman lafiyar bayan an bayyana fargabar da aka nuna na cewa za ta iya samun jinkin aiwatar da yarjejeniyar.
Isra’ila ta ci gaba da kai hari a Gaza
Sai dai kuma Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare a Gaza, inda zuwa safiyar Juma’a ta kashe mutum 101 ciki har da mata da kananan yara 58, tun bayan kulla yarjejeniyar ta ranar Laraba.
Kazalika an samu rabuwar kai tsakanin ministocin Isra’ila inda wasu ke adawa da yarjejeniyar lamarin da ya sa aka dage zaman majalisar ministocin kasar wanda das farko aka shirya gudanarwa ranar Alahmis domin kada kuri’a kan batun.
Kungiyar Hamas dai ta bayar da tabbacin cika sharudan yarjejeniyar, amma Isra’ila na zarin kungiyar da kawo cikas.
Amma a safiyar Juma’a ofishin Netanyahu ya ba da tabbacin samun amincewa majalisar tsaro majalisar zartaswar da batun.