Hamma Amadou ya gudu Belgium

Rahotannin kafafen watsa labarai a Jamhuriyyar Nijar sun ce, shugaban Majalisar Dokokin kasar, Malam Hamma Amadou ya gudu zuwa kasar Beljiyum.Tun a makon jiya ne Malam Hamma Amadou ya fice daga kasar Nijar ya shiga kasar Burkina Faso, bayan da wani kwamitin Majalisar Dokokin kasar ya zartar da kudurin cire masa rigar kariyar da yake […]

Hamma Amadou ya gudu Belgium
Hamma Amadou ya gudu Belgium

Rahotannin kafafen watsa labarai a Jamhuriyyar Nijar sun ce, shugaban Majalisar Dokokin kasar, Malam Hamma Amadou ya gudu zuwa kasar Beljiyum.
Tun a makon jiya ne Malam Hamma Amadou ya fice daga kasar Nijar ya shiga kasar Burkina Faso, bayan da wani kwamitin Majalisar Dokokin kasar ya zartar da kudurin cire masa rigar kariyar da yake da ita.
Matakin majalisar zai ba da dama a gurfanar da Hamma Amadou a gaban shari’a domin kare kansa daga zargin hannu a safarar jarirai daga Najeriya zuwa Nijar.
Sai dai Hamma Amadou na zargin cewa akwai siyasa cikin wannan lamari, wanda ya yi sanadin ci gaba da tsare matarsa tare da wasu mutum 16 tun cikin watan Yuni.
Jam’iyyar PNDS Tarayya mai mulkin Nijar ta ce ba za ta dauki wani mataki a kan batun ba, sai kotun tsarin mulkin ta yanke hukunci game da batun cire wa Hamma Amadou rigar kariya.
Mahukuntan Jamhuriyyar Nijar sun kuma cafke Ministan Noma Abdou Labo a ranar Asabar a kan zargin bayan kame matarsa tun farko game da badakalar.
A watan Yuni ne ’yan sandan Nijar suka kama mai dakin Hamma Amadou da uwargidan Abdou Labo.
Sai dai lauyan mai dakin Hamma Amadou, Maitre Sule Umaru ya musanta zargin, kuma a cewarsa an kama su ne ba tare da wata shaida ba a kan laifin da ake tuhumarsu.
Hukumar Yaki da Fataucin Mutane ta Najeriya (NAPTIP) ta ce ba ta da masaniya a kan batun da ya shafi fataucin yara zuwa Nijar daga Najeriya.
A Nijar dai akwai rikicin siyasa tsakanin ’yan adawa da Shugaban kasa Muhammadou Issoufo da ke son yin tazarce, yayin da Hamma Amadou ne ake ganin babban mai kalubalantarsa.