Hamza Aliyu, a Bauchi Wani xan qabilar Ibo da ke zaune a Bauchi, Cif Mathew Okochukwu ya bayyana cewa babu wani mutum da zai iya ya raba Najeriya gida biyu, domin tun lokacin da aka rantsar da Buhari a ranar 29 ga watan Mayu, sama da kashi 85 cikin 100 n
Wani dan kabilar Ibo da ke zaune a Bauchi, Cif Mathew Okochukwu ya bayyana cewa babu wani mutum da zai iya ya raba Najeriya gida biyu, domin tun lokacin da aka rantsar da Buhari a ranar 29 ga watan Mayu, sama da kashi 85 cikin 100 na ’yan kasa sun gamsu da manufofin gwamnatin.Ya bayyana […]
Wani dan kabilar Ibo da ke zaune a Bauchi, Cif Mathew Okochukwu ya bayyana cewa babu wani mutum da zai iya ya raba Najeriya gida biyu, domin tun lokacin da aka rantsar da Buhari a ranar 29 ga watan Mayu, sama da kashi 85 cikin 100 na ’yan kasa sun gamsu da manufofin gwamnatin.
Ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da wakilin Aminiya a ofishinsa da ke Bauchi. A cewarsa ya kamata a rika zantawa ta kafafen watsa labarai, domin bayyana wa duniya wasu daga cikin manufofin Shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Ya kara da cewa yankin Arewa maso gabas ya fuskanci dimbin matsaloli da kashe-kashe amma da zuwan wannan gwamnati kowa ya ga yadda abubuwa suka fara gyaruwa tun daga kan matsalar tsaro har zuwa fannin wutar lantarki. “Najeriya kasa daya ce kuma ina tabbatar wa duniya cewa babu wanda ya isa ya raba kasar nan, domin Allah ne Ya yi Musulmi da Kirista, dole mu zauna tare domin ba mu da wata kasa sai Najeriya. Saboda haka ina rokon ’yan Najeriya Musulmai da Kirista, da mu ci gaba da addu’o’i na musamman ga shugabanni, domin su kawo gyara, yadda babu batun fifita wata kabila kan wata.”
Ya kara da cewa: “Ni dan Jihar Bauchi ne a yanzu, domin tun ina matashi na zo Bauchi; yau ga shi na shafe sama da shekara 35. Na haifi ’ya’ya, wasu daga cikinsu ma har sun yi aure a jihar nan. Saboda haka ni yanzu cikakken dan Bauchi ne.”