Hana acaba a kananan hukumomi 15 za ta sanya mu cikin kunci – Mutanen Legas
A ranar Litinin da ta gabata ce Gwamnatin Jihar Legas ta fitar da sanarwar haramta hawan babur da aka fi sani da acaba da babur mai kafa uku (Kake-NAPEP) a kananan hukumomi 15 na jihar da kuma daukacin manyan hanyoyin jihar da saman gadoji, a wani mataki da gwamnatin ta ce na kare rayuka da dukiyoyin […]
A ranar Litinin da ta gabata ce Gwamnatin Jihar Legas ta fitar da sanarwar haramta hawan babur da aka fi sani da acaba da babur mai kafa uku (Kake-NAPEP) a kananan hukumomi 15 na jihar da kuma daukacin manyan hanyoyin jihar da saman gadoji, a wani mataki da gwamnatin ta ce na kare rayuka da dukiyoyin jama’a ne.
A sanarwar da gwamnatin ta fitar, ta ce za fara tilasta bin dokar sau-da-kafa daga gobe Asabar 1 ga Fabrairu.
Kwamishinan Watsa Labarai da Tsare-Tsare na Jihar Mista Gbenga Omotosho ne ya bayyana haka a taronsa da manema labarai, inda ya ce Gwamantin Jihar ta dauki matakin ne bayan ta gana da masu ruwa-da-tsaki a fannin tsaron jihar.
Kananan hukumomin da lamarin ya shafa sun hada da Apapa da Apapa Iganmu LCDA sai Lagos Mainland da Yaba LCDA da Surulere Itire-Ikate sai Coker-Aguda sai Ikeja da Onigbongbo da Ojodu; da Eti-Osa da Ikoyi-Obalende, sai Iru/Bictoria Island da Lagos Island da kuma Lagos Island East.

Ya ce matakin share fage ne inda aka soma da kananan hukumomi 15 domin ganin an tsabtace sashin sufuri na Jihar Legas.
Aminiya ta zanta da wadansu daga cikin wadanda matakin zai shafa kai-tsaye wato masu sana’ar acaba da Keke NAPEP da jama’ar gari da ke amfani da wadannan hanyoyi a yau da kullum.
Abubakar Muhammad matashi ne da ke acaba a kamfanin ‘Opay’ ya shaida wa Aminiya cewa a baya yana sana’ar canjin kudi ne, amma saboda tabarbarewar harkokin kasuwanci sai ya koma tukin babur, “Kimanin wata biyu ke nan da na fara aikin tuka babur kuma al’amura sun fara warwarewa domin muna samun rufin asiri sosai, domin daga ranar Litinin zuwa Juma’a muna ba kamfanin Naira dubu biyu ne duk rana daga nan duk abin da muka samu namu ne. Yanzu haka akwai dubban matasa da suka karbi babura daga kamfanin sai dai wannan mataki zai katse mana hanzari. Yawanci cikin garin Legas nake aiki inda aka haramta babur, muddin wannan abu ya tabbata dole mu hakura da aikin domin in ba cikin garin muka fita ba aikin ba zai yiwu ba” inji shi.
Ya ce akasarin wadanda yake dauka a babur ma’aikata ne da ke zuwa cikin gari aiki sai kuma ’yan makaranta da yakan yi jinga da iyayensu.
Shi ma Kashim Abdullahi da ke acaba da Kamfanin Opay ya shaida wa Aminiya cewa ya karanta injiniya ne, inda ya samu Babbar Diploma (HND), ya ce rashin aikin yi ne ya sa a baya yake gyarar wayar salula yana kuma sayar da wayar, amma da kamfanin bada babur din acaba na Opay suka fara aiki a Legas sai ya je aka ba shi ya fara. “Na fara aikin tukin babur din kimanin wata biyar da suka gabata a lokacin Kamfanin Opay na da shekara daya da zuwa Legas, zuwansa ya sanya jama’a da dama sun samu aikin yi, amma yanzu matakin da Gwamnatin Legas ta dauka ya sa jama’a da dama sun fara mayar da baburan da suka karba daga kamfanin, domin muddin ba za ka yi aiki a wuraren da gwamnatin ta tsame ba, to babu yadda za a yi ka iya hada kudin kamfani har ka samu naka,” inji shi.
A bangaren Garba Abdullahi Sarki mai babur mai kafa uku wanda aka fi sani da Keke Marwa a Legas cewa ya yi matakin na Gwamnatin Legas ba abu ne da zai yiwu ba, illa kawai an kara bai wa ma’aikatan da ke kula da sashen karfin cin zarafin masu sana’ar. Ya ce dama aka ba ’yan sanda da jami’an da ke kula da cinkoson ababen hawa don su uzzura musu. Ya ce “Ko a baya haka suke takura mana ba sa bari mu sake, daga mun yi dan ciniki sai su karbe. To yanzu an kara musu karfi, don na san ’yan acaba ba kowa zai kiyaye dokar ba, domin dole a fita a nemi abinci kuma dole mutane su yi tafiye-tafiye, don haka Gwamnatin Legas ta shigo da wannan doka ce don ta kara uzzura wa talaka. Dama mu talakawa ba mu da amfani sai lokacin zabe, a wannan lokaci ne ake lallaba mu, amma da zarar zabe ya wuce shi ke nan sai a yi watsi da mu. Idan sun hana mu neman abincinmu sun kawo motoncin da suke so a yi amfani da su, mu da ba mu yi karatu ba, za su ce ba mu da takarda ba za su ba mu aikin ba, ka ga rashin aiki ya karu ke nan. A baya acaba nake yi da takurar ta yi yawa na koma tuka babur mai kafa uku, shi ma ga shi an hana mu yanzu to ina ake so mu saka kanmu?”
“Duk da dai ba a hana mu aiki a Agege ba, amma muna zuwa kan gada wadda yanzu ba mu da ikon zuwa, idan ba ka je da nisa ba, yaya za a yi ka samu abin da za ka ba mai babur din? Don haka kiranmu ga gwamnati ta sake lale” inji shi’
Sarkin Hausawan Oshodi Alhaji Tukur Wurno cewa ya yi matakin gwamnatin na Legas ba zai taimaka wajen kyautata tsaro kamar yadda take ikirari ba, domin abu ne da zai sanya dubban matasa su rasa aikin yi, kuma hakan zai sanya da dama su fada mawuyacin hali, lamarin da zai iya sanya su fada wa miyagun ayyuka.
Ya ce tun kafin a kafa dokar an taba zuwa inda suke cikin tsakar dare aka kwashe baburan acaba sama da 600 na yaransu. “Bayan sun kwashe baburan suka kwashi mutanenmu da dama sai da muka kashe akalla Naira dubu 700 kafin a ba mu belinsu, yanzu haka baburan nan duk muna da takardunsu amma sun rike mana su har abada, Babu yadda ba mu yi ba sun hana, sai ga shi kuma an sanya wannan doka an kara musu karfi, idan gyara gwamnati ke son yi sai ta bari sai ta gyara hanyoyi an samu wadatar hanya sannan ta dauki mataki, amma yanzu hanyoyinmu a lalace suke, ba daidai ba ne a zo da wannan lamari,” inji shi.
Su ma masu hawa babura suna zuwa wajen harkokinsu ba a bar su a baya ba wajen kokawa da matakin na gwamnati.
Malam Kabiru Yusuf dan jarida ne mazaunin Legas ya shaida wa Aminiya cewa matakin na Gwamnatin Legas zai shafi rayuwar yau da kullum, “Na saba ba na hawa mota idan zan je aiki domin muddun mutum ya hau mota sai ya yi awa 2 zuwa 3 daga Idi-Araba zuwa Ikoyi. Ka ga ba zai yi kyau mutum ya rika makara kullum a wajen aiki ba, amma a babur cikin minti 20 zuwa 30 ka kai inda za ka. Shi ya sa ba na ganin tsadarsa domin biyan bukata ya fi dogon buri. Muddin wannan doka ta tabbata dole in rika fita aiki da zarar an yi Sallar Asuba ko kafin a yi,” inji shi.
Shi ma Malam Adamu Tela wanda ke hawa babur domin gudanar da al’amuransa na yau da kullum ya shaida wa Aminiya cewa shi madinki ne kuma masu babur na taimaka musu wajen cika alkawari,
Aminiya ta zanta da Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a na Hukumar Kula da Cinkoson Ababen Hawa ta Jihar Legas (LASTMA), Mista Olumide Filayen wanda ya ce Gwamnatin Legas ta dauki matakin ne domin tsabtace harkar sufuri da karfafa tsaro da kuma rage yawan haddura da baburan ke kawowa. Sannan ya ce jami’ansu a shirye suke su tabbatar ana bin dokar da zarar ta soma aiki a gobe.