Hana acaba a Legas ya kawo wa ‘sana’armu’ cikas – Dan fashi

Ya ce tun da aka hana acaba, suka fuskanci tsaiko

Hana acaba a Legas ya kawo wa ‘sana’armu’ cikas – Dan fashi

‘Yan acaba

Wani mutum da ake zargi da fashi da makami a Jihar Legas ya koka wa jami’an tsaro yadda sata ke musu wahala a yanzu, sakamakon hana acaba da gwamnatin Jihar ta yi.

Dan fashin ya yi wannan furuci ne bayan rundunar tsaron hadin gwiwa ta kamo shi tare da wasu abokansa biyu, lokacin da suke kokarin yi wa wata mace kwace a tasha.

“Watanmu shida muna fashi da babur, kuma hana acaba da aka yi ba karamin matsa mana yayi ba, domin dole sai koma wa kwacen waya muka yi.”

Shugaban rundunar, Shola Jejeloye ya ce sun samu nasarar kama dan fashin da abokansa ne bayan matar da suke kokarin yi wa kwacen ta yi kururuwar da ta ja hankalin jami’an tsaron da ke tashar.

Ya ce duk da sun yi yunkurin tsere wa a babur su ukun, guda daga cikinsu ya fadobayan sun fara tafiya, wanda kama shi ne ya kai ga kamo sauran.

Gwamnan Jihar, Babajide Sanwo-Olu ne dai ya hana sana’ar acahaban tun a shekarar 2022 a wasu sassan jihar, bayan kisan wani injiniya da wasu ’yan kabu-kabu suka yi a Lekki .