Hana bara a Jihar Kaduna ya yi daidai, amma… – Sheikh Yusuf Sambo
Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai ta kasa ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah, Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun ya ce matakain da Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i ya dauka na hana bara a jihar ya yi daidai sai dai akwai bukatar gwamnati ta taimaka wa mabaratan da sana’o’i domin dogaro da kansu.Sheikh Yusuf […]
Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai ta kasa ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah, Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun ya ce matakain da Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i ya dauka na hana bara a jihar ya yi daidai sai dai akwai bukatar gwamnati ta taimaka wa mabaratan da sana’o’i domin dogaro da kansu.
Sheikh Yusuf Sambo ya ce koda yake mafi yawan mabaratan da ke yawo a kan titunan ba ’yan asalin jihar ba ne akwai bukatar a mayar da su garuruwansu domin gwamnatin ta samu damar kulawa da almajirai ’yan asalin jiharta.
Sheikh Sambo Rigachikum ya bayyana cewa hana bara da gwamnatin ta yi zai taimaka wajen magance mutuwar zuciyar da ta addabi wasu Musulmi.
Malamin ya bayyana haka ne a zantawa da manema labarai a gidansa da ke Rigachikun a tsakiyar makon nan “Hana bara yana da kyau, amma ya kamata a yi tunanin matakan da za a dauka domin taimaka wa wadannan nakasassun, domin yawancinsu magidanta ne masu iyali da sauran dawainiya ta ryuwar yau da kullum. Kuma yawancin mabaratan ba ’yan asalin Jihar Kaduna ba ne. Kamata ya yi gwamnati ta bi wadannan nakasassu, ta tantance baki daga cikinsu, a dauki kowanne a mayar da shi garinsa na asali. Su kuma ’yan asalin jihar a bi su garuruwansu a dubi sana’ar da mutum zai iya, idan yin nika ne a kofar gidansu, ko yin faci, kodai wata sana’a da nakasarsa za ta iya barinsa ya yi, sai a dauki nauyin saya masa kayan aiki,” inji shi.
A cewarsa idan aka yi haka, za a inganta rayuwar wadannan bayin Allah domin dama bara ba abar so ba ce ga addinin Musulunci.
A fahimtarsa sanya dokar hana barar za ta taimaka wa mabaratan ne wajen raba su da yawon kan titi, sannan an samar masu da sana’a, an mutuntasu a gidajensu, kuma an rufa musu asiri.
Game da tabarbarewar tarbiyya a tsakanin matasa kuwa, Sheikh Sambo ya bukaci iyaye su kula da tarbiyyar ’ya’yansu domin su zama mutanen kirki nan gaba.
“Ina tuna wata magana ta Marigayi Sheikh Lawal Abubakar, inda yake cewa ‘in ka ga tsohon banza, to yaron banza ne ya girma.’ Saboda haka, ka ga wannan yana nuni da cewa mutum yana zama mutumin kirki ne tun yana karami, zuwa saurayi, har zuwa tsufarsa,” inji shi.
Har ila yau ya shawarci iyaye su sani cewa su ne mutanen farko da za su ba ’ya’yansu tarbiyya, kafin gwamnati ta taimaka.
Sheikh Sambo ya yi kira ga al’ummar Musulmi su ci gaba da zama masu tsoron Allah da hakuri wadanda halaye ne da ya ce Musulmi na koya a cikin watan azumin Ramadan.