Hana bara: Nakasassu sun yi barazanar mamaye gidan gwamnatin Kaduna

kungiyar Nakasassu ta Jihar Kaduna ta yi barazanar mamaye gidan gwamnatin jihar idan har Gwamna Nasir Ahmed El-Rufa’i bai gaggauta janye dokar hana bara da ya sanya wa hannu a jihar ba.Gwamnan ya tura wa majalisar jihar kudirin dokar hana bara da talla a jihar inda majalisar ta amince, Gwamnan ya sa hannu ta zama […]

Hana bara: Nakasassu sun yi barazanar mamaye gidan gwamnatin Kaduna
Hana bara: Nakasassu sun yi barazanar mamaye gidan gwamnatin Kaduna

kungiyar Nakasassu ta Jihar Kaduna ta yi barazanar mamaye gidan gwamnatin jihar idan har Gwamna Nasir Ahmed El-Rufa’i bai gaggauta janye dokar hana bara da ya sanya wa hannu a jihar ba.
Gwamnan ya tura wa majalisar jihar kudirin dokar hana bara da talla a jihar inda majalisar ta amince, Gwamnan ya sa hannu ta zama doka.
Naksassun sun gudanar da zanga-zangar lumana inda suka nemi Gwamna Nasir El-Rufa’i ya janye dokar kafin mako daya.
Jagoran nakasassun Kwamared Rilwanu Abdullahi Muhammed ya shaida wa taron manema labarai a Sakatariyar ’Yan jarida ta Kaduna cewa, “Ranar Litinin mai zuwa za mu kara yin wata zanga- zangar zuwa gidan gwamnati, ko muyi rai ko kada mu yi za mu hallara kwanmu da kwarkwata don nuna bacin ranmu a kan dokar. Gwamna El-Rufa’i ya yaudare mu domin lokacin yakin zabe ya yi mana alkawarin cewa ba zai yi dokar da za ta takura wa rayuwarmu ba, amma abin takaici ashe yaudara ya yi mana.”
Kwamared Rilwanu ya ce dole ke sa su yi bara ba don suna so ba, sai domin su kare mutuncinsu da na iyalansu.
Nakasassun sun gudanar da zanga-zangar dauke da kwalayen da aka yi rubutun: “El-Rufa’i ka cika alkawarinka na zabe kafin hana bara” da “Hana bara ba zai taba yiwuwa a Kaduna ba, sai an kafa hukumar kula da nakasassu,” da “Majalisar Jihar Kaduna kin ci amanarmu, a ba mu kashi dari goma na aikin yi kafin a hana bara,”  da “A kaddamar da kudirin mu na kirkiro mana da hukumar nakasassu kanfin ku hanamu bara.”