‘Hana cin naman daji ne ya kassara ni’
Wani da ke sayar da naman kaji da shanu da ke kauyen Gwagwa a yankin Abuja mai suna Malam Muhammadu Manya, ya ce masu sayar naman kaji irinsa sun shiga mawuyacin halin tun bayan da aka hana cin naman daji sakamakon bullar cutar Ebola.Ya ce yana samun cinikin gasasshen naman kaji da shanu sosai, amma […]
Wani da ke sayar da naman kaji da shanu da ke kauyen Gwagwa a yankin Abuja mai suna Malam Muhammadu Manya, ya ce masu sayar naman kaji irinsa sun shiga mawuyacin halin tun bayan da aka hana cin naman daji sakamakon bullar cutar Ebola.
Ya ce yana samun cinikin gasasshen naman kaji da shanu sosai, amma a kwanakin nan jama’a sun kaurewa masa sakamakon hana cin naman daji da jami’an lafiya suka yi bayan bullar cutar Ebola.
Ya ce ya shekara sama da ashirin yana sayar da naman jaki da na shanu, amma bai taba fuskantar rashin kwastomomi kamar a wannan karon ba.
Ya ce ya yi gadon sayar da nama ne, inda ya fara tun yana dan shekara goma a garinsu Kabo da ke Jihar Kano, daga bisani ya dawo Kaduna bayan ya zama saurayi.
Ya ce yayansa ne ya kafa tukuba a makarantar Kaduna-Poly, sannan ya bar masa bayan wajen ya bunkasa, don ya dogara da kansa.
“Sai dai bayan wasu shekaru, sai Gwamnan Jihar Kaduna Usman Mu’azu a lokacin Janar Buhari ya ba da umarnin rusa rumfunan da ke cikin harabar makarantar, a sanadin haka na dawo nan Abuja.
Ya ce ya samu ci gaba kwarai a Abuja, har ya gina gida.