Hana cin naman daji ya bunkasa cinikin naman kaji – Mahammadu Manya

Wani mai sana’ar gasa naman kaji da na shanu a garin Gwagwa da ke yankin Abuja Malam Muhammadu Manya, ya bayyana yadda yake samun bunkasar cinikin naman kaji da na shanu a kwanakin nan, a sakamakon kaurace wa cin naman daji da jama’a ke yi bayan bullar cutar Ebola. Muhammad Manya wanda ya ce ya […]

Hana cin naman daji ya bunkasa cinikin naman kaji – Mahammadu Manya
Hana cin naman daji ya bunkasa cinikin naman kaji – Mahammadu Manya

Wani mai sana’ar gasa naman kaji da na shanu a garin Gwagwa da ke yankin Abuja Malam Muhammadu Manya, ya bayyana yadda yake samun bunkasar cinikin naman kaji da na shanu a kwanakin nan, a sakamakon kaurace wa cin naman daji da jama’a ke yi bayan bullar cutar Ebola.
Muhammad Manya wanda ya ce ya shekara sama da ashirin yana gudanar sana’ar, ya ce baya ga kwastomomi da suka saba sayan nama a wajensa, jama’a da ke zuwa wajensa sun karu kwarai a ’yan kwanakin nan.
Ya ce ya gaji sana’ar sayar da naman kaji da na shanu ne, inda ya fara ta tun yana dan shekara goma a garinsu Kabo da ke Jihar Kano daga bisani ya bi yayansa zuwa Kaduna bayan ya zama saurayi.
“Yayana ya kafa tukuba a makarantar Kaduda Poly, sannan ya bar mini ita bayan ta bunkasa, ya yi mini hakan ne don in dogaro da kaina.” Inji shi.
“Sai dai bayan wasu shekaru, Gwamnan Jihar Kaduna Usman Mu’azu a lokacin Janar Buhari ya ba da umarnin rusa rumfunan da ke harabar makarantar, a dalilin haka na dawo Abuja. Na samu ci gaba kwarai a nan, har na yi gida, na kuma zama tamkar dan kasa, ko lokacin da aka yi rushe-rushe a Abuja a shekarun baya, masu garin ba su bari an taba gidana ba.
Ya ce yana fuskantar matsalar rashin kyan hanyar garin, wanda ta taso daga Deidei zuwa Karmo.
 “Hakan ya sa wasu kwastomomina da ke zuwa daga nesa ke samun rashin karfin gwiwa a sakamakon rashin kyan hanyar, don haka ya kamata gwamnatin Abuja ta kawo musu dauki.” Inji shi.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya