Hana mata aikin jinkai ta haifar wa MDD tsaiko a Afghanistan
MDD ta ce shigar mata ayyukan jinkai abu ne da babu makawa kuma dole a ci gaba da hakan.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce wasu shirye-shiryenta sun tsaya a Afghanistan bayan da gwamnatin kasar ta Taliban ta haramta wa mata shiga ayyukan jinkai.
MDD ta ce ta dakatar da wasu shirye-shiryenta masu muhimmanci a Afganistan sannan ta yi gargadin akwai yiwuwar wasu ayyukan nata a kasar su sake tsayawa saboda matakin da gwamnatin Taliban ta dauka.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Za A Tabbatar Da Zaman Lafiya A Harkokin Zabe
- Yadda mahara suka kashe mutum 14, sun sace 81 a Sakkwato da Katsina
Shugaban sashen jinkai na MDD, Martin Griffiths ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar ranar Laraba.
Ya ce, shigar mata ayyukan ba da agaji abu ne da babu makawa kuma dole a ci gaba da hakan, tare da kira ga hukumomin kasar da su janye wannan mataki da suka dauka.
“Haramta wa mata shiga ayyukan jinkai babbar barazana ce ga rayuwar al’ummar Afganistan.
“Tuni wasu shirye-shirye suka tsaya saboda rashin ma’aikata mata,” in ji sanarwar.