Hana kai fetur bakin iyaka: Farashin mai ya kai Naira 600 a iyakokin Najeriya

Mazauna iyakokin Najeriya sun koka kan tashin farashin man fetur da suke fama da shi bayan Gwamnatin Tarayya ta dakatar da kai man fetur zuwa garuruwan da ke makwabtaka da kasashen waje. A makon jiya ne Shugaban Hukumar Kwastam, Kanar Hameed Ali (mai ritaya) ya bukaci a dakatar da kai man fetur zuwa duk wani […]

Hana kai fetur bakin iyaka: Farashin mai ya kai Naira 600 a iyakokin Najeriya

Shugaban Hukumar Kwastam Kanar Hameed Ali (mai ritaya)

Mazauna iyakokin Najeriya sun koka kan tashin farashin man fetur da suke fama da shi bayan Gwamnatin Tarayya ta dakatar da kai man fetur zuwa garuruwan da ke makwabtaka da kasashen waje.

A makon jiya ne Shugaban Hukumar Kwastam, Kanar Hameed Ali (mai ritaya) ya bukaci a dakatar da kai man fetur zuwa duk wani gidan man da bai wuce nisan kilomita 20 ba da iyakar Najeriya.

Lamarin ya jawo cece-ku-ce, inda bayan dakatar da kai man, sai farashinsa ya yi sama, inda ake sayar da shi a kan Naira 600 kan lita daya a wasu yankunan.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa gidajen mai da yawa sun rufe bayan jami’an Gwamnatin Tarayya sun kai musu samame.

Wani mazaunin yankin Ipokia mai suna Elijah Akinola ya ce, “Ta yaya mutum zai sayi litar man fetur a Naira 600? Idan muna son samun man fetur a farashinsa na Naira 145, dole sai mun je Owode, wanda nisansa ya kai kilomita 28. Ban san yaya ake so mu yi rayuwa ba a nan.

Babban Sakataren NUPENG Olawale Afolabi

Da can ai jami’an gwamnati ne suke karbar na goro su bar masu fasakwaurin mai suna fita da man. Yanzu kuma Gwamnatin Tarayya ta sanya doka, amma mu muke shan wahala.”

An ruwaito cewa jami’an tsaro suna cin zarafin mutane. Wani mai suna Idowo ya ce, “Jami’an tsaro da suka hada da sojoji da sauransu suna zuwa gidajen mai suna rufe su, sannan suna bugun mutanen da suka gani a gidajen man. Yanzu litar mai ta kai Naira 600 a Idiroko da Ipokia, bayan sun kulle gidajen mai da yawa. Duk mutane sun watse kama an sanya dokar hana fita. Idan kuma muka fita muka sayo man, sai a kama mutum idan zai shigo.”

A Jihar Katsina kuwa, masu gidajen mai suna ci gaba da harkokinsu duk da dokar da aka sanya.

Rahotanni sun ce ana ci gaba da saya da sayar da man fetur a wasu gidajen mai a iyakar Jibiya da Kongolan a ranar Litinin da ta gabata.

Wani mai sayar da man fetur ya ce, “Babu wanda ya ce mu dakatar da sayar da man fetur. Har jami’an tsaro ma sun zo sun sayi man fatur a nan.”

A Jihar Adamawa, ana sayar da litar man fetur a Naira 200 ne. Rahotanni sun ce a iyakokin Mulduwa da Gelda da ke makwabtaka da Kamaru, farashin man fetur da a da yake Naira 178, yanzu ya kai Naira 200.

Wata majiya ta ce duk da cewa an fara aiwatar da dokar, har yanzu ana ci gaba da fasakwaurin man fetur zuwa Kamaru, inda ake amfani da jarkuna ana shiga da man zuwa Kamaru.

Kwanturolan Kwastam mai kula da Adamawa da Taraba, Kamardeen Olumoh ya ce sun bayar da umarni a dakatar da harkokin saye da sayar da man fetur a yankunan da abin ya shafa kamar yadda doka ta bukata.

A Jihar Jigawa, al’ummar Babura sun shaida wa BBC cewa matakin na baya-bayan nan ya haddasa rufe gidajen man fetur da dama.

“Ba mu san inda za mu je mu shawo man ba, ballantana mu san nawa za mu rika daukar fasinja,” inji wani mai sana’ar acaba a yankin.

A cewarsu, a wasu gidajen mai ana samun layuka wajen sayen man a kan farashi mai tsada, abin da ya bude kasuwar ’yan bumburutu.

Sun kara da cewa jami’an Hukumar Kwastam suna samame kan duk wani gidan mai da aka samu yana sayarwa.

A Ilela na Jihar Sakkwato, jama’a sun ce kashi 90 cikin 100 na gidajen man da ke yankin na rufe.

Man da ake sayarwa a kan Naira 145 da gwamnati ta kayyade, a cewarsu, yanzu farashinsa ya ninka sau kusan uku.

Masu fasakwauri ne kawai suke kai mai iyakokin kasar nan – NUPENG

Da suke bayani kan lamarin, Kungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Gas ta Najeriya (NUPENG) ta ce za ta kafa kwamiti mai karfi domin tabbatar da an aiwatar da dokar a gidajen man da abin ya shafa.

Kungiyar  NUPENG ta ce masu fasakwauri ne kawai suke kai man zuwa yankin iyakokin kasar nan bayan dokar da Gwamnatin Tarayya ta sanya.

Babban Sakataren Kungiyar, Olawale Afolabi ne ya sanar da haka, inda ya ce, “Muna sane da dokar Gwamnatin Tarayya ta hana kai man fetur zuwa gidajen man da ba su wuce kilomita 20 ba daga iyakokin kasar nan. Amma masu fasakwauri suna kai man har yanzu. Akwai wahala hana ayyukan bara-gurbi, amma za mu tabbatar dokar ta yi aiki.”

Da aka shaida masa cewa wadansu daga cikin tankokin man suna dauke da tambarin Kungiyar NUPENG, sai ya ce suna amfani da kungiyar ce kawai su tsere wa doka.

“Yanzu haka muna kokarin sake samfurin tambarinmu. Sannan kwamitinmu zai yi aiki ba sassauci domin tabbatar da doka da oda. Muna kokarinmu, amma ina so ka sani cewa wadannan masu fasakwauri suna da bindigogi, don haka zai yi wuya mu iya fuskantarsu kai-tsaye.

Don haka za mu yi kokari wajen mayar da hankali kan ilimantar da mambobinmu tare da wayar musu kai a kan illar harka da masu fasakwauri. Amma dole sai jami’an tsaro sun taimaka wajen dakatar da lamarin,” inji shi.