Hana likitocin gwamnati aiki a asibitocin kudi zai inganta harkar lafiya kuwa?

A makon da ya gabata ne Ministan Lafiya, Farfesa Isaac Adewole ya sanar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta hana likitocin gwamnati aiki a asibitocin kudi. Lamarin ya janyo cece-kuce, musamman a tsakanin likitoci. Hakanan suma mutane wadanda su ake dubawa a asibitocin ba a bar su a baya, domin suna ta tofa albarkacin bakin […]

Hana likitocin gwamnati aiki a asibitocin kudi zai inganta harkar lafiya kuwa?

A makon da ya gabata ne Ministan Lafiya, Farfesa Isaac Adewole ya sanar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta hana likitocin gwamnati aiki a asibitocin kudi. Lamarin ya janyo cece-kuce, musamman a tsakanin likitoci. Hakanan suma mutane wadanda su ake dubawa a asibitocin ba a bar su a baya, domin suna ta tofa albarkacin bakin su. Hakan yasa wakilan Aminiya suka zagaya domin jin ta bakin jama’a, kuma ga amsoshin da suke bayarwa:

 

Matakin ba zai taimaka ba – Kabir ’Yar-aduwa

Bashir Yahuza Malumfashi, a Katsina

Malam Muhammad Kabir ’Yar-aduwa: “Ni dai a ganina, wannan mataki na hana likitoci aiki a waje ba zai taimaka ba, domin kuwa babban abin da ke sanyawa suke irin wadannan ayyuka shi ne, saboda ba su samun biyan bukata daga gwamnatocin da suke yi wa aiki. Idan da a ce gwamnatoci suna biyan hakkokin likitoci yadda ya kamata kuma ana kyautata masu, babu dalilin da zai sa su rika hada aiki biyu. Don haka idan ana son a inganta harkar lafiya, to a kyautata wa likitoci, a tsare masu hakkokinsu yadda ya kamata. Wannan zai sanya su maida hankali kan ayyukansu sosai, sannan zai sanya su daina shiga yaje-yajen aiki, wanda haka zai inganta harkokin lafiya amma ba dokar hana su aiki a asibitocin kudi ba.”

 

Matakin zai kawo gyara – Abubakar Isah Muhammad

Hussaini Isah, Jos

 Alhaji Abubakar Isah Muhammad: “A ganina wannan mataki da gwamnati za ta dauka na hana likitoci aiki a asibitoci masu zaman kansu, zai kawo gyara ga harkar kiwon lafiya a Najeriya. Domin su likitoci a Najeriya da dama suna aiki ne a asibitocin gwamnati, amma sai ya zamanto suna bude asibitocinsu. Sau tari za ka je asibitocin gwamnati, sai ace maka babu kayan aiki amma sai likitocin da suke aiki a asibitocin gwamnatin, su ce wa mara lafiya ya tafi a asibitocinsu da suka bude. Domin ni kaina irin wannan ya faru da ni, a wannan gari na Jos. Don haka ni a ganina wannan mataki zai taimaka wajen gyara harkokin kiwon lafiya a asibitocin gwamnati. Domin likitoci suna yi wa asibitocin gwamnati zagon kasa ne.” 

 

Ya dace a hana su – Buhari Yanusa Mohammed

John D. Wada, Nasarawa

Malam Buhari Yanusa Mohammed: “Nidai a nawa ra’ayi, ya dace a hana likitotin asibitocinmu aiki a asibitocin kudi. Don sau da yawa idan ka kai mara lafiya asibiti, za ka ji wai likita baya nan. Idan ka bincika za ka ji wai ya tafi asibitinsa wanda ake kira pribate a turance. Kaga haka bai kamata ba. Wasu marasa lafiyan da yawa sukan rasa rayukansu sakamakon rashin likita a ainihin asibitin da yake aiki. Saboda haka ni dai kamar yadda na bayyana idan za a hana su aiki a irin wadannan asibitocin kudi, ba shakka zai taimakawa fannin kiwon lafiya a kasar nan.

 

 

Matakin zai taimaka – Abdullahi Yahaya

Bashir Yahuza Malumfashi

Malam Abdullahi Yahaya: “Ni dai a ganina, wannan mataki na hana likitocin da ke aiki a asibitocin gwamnati yin aiki a asibitocin kudi ya dace kuma zai taimaka wajen inganta harkokin lafiya a kasar nan. Idan mun lura da abin da ke faruwa, za ka ga an kai marasa lafiya asibitocin gwamnati amma likitocin ba su gudanar da ayyukansu yadda ya dace. Suna yin haka ne domin a rika zuwa asibitocinsu na kudi, ana kyale na gwamnati. Hatta magungunan da ake ajewa a asibitocin gwamnati, ana zargin cewa ana kwashe su ana kai wa asibitocin kudi, kan haka za ka ga mutum ya je asibiti amma likita yana ce masa ya je waje kaza da kaza ya sayi magani. Misali, idan aka ce mutum ya je tes a wani wuri, idan ba can ya je ba, sai likitocin su ki amsa dole sai ya je inda suka zaba masa. Ni kaina shaida ne kan irin haka, domin an taba yi wa matata haka lokacin da za ta haihu. Haka kuma, koda an haramta wa likitoci aikin waje, to kuma sai an kula da su sosai, domin suna aikata rashin gaskiya da yawa. Suna sanya mutum ya sayo magani, amma su yi wa wani aiki da shi.”

 

 

 

 Matakin zai kara bata harkar kiwon lafiya – Ibrahim Namakaram

Hussaini Isah, Jos

Alhaji Ibrahim Namakaram: “A ganina wannan mataki na hana likitoci aiki a asibitoci masu zaman kansu, ba zai taimaka wajen gyara harkokin kiwon lafiya a Najeriya ba. Matakin da ya kamata gwamnati ta dauka kan gyara harkokin kiwon lafiya, shi ne ta inganta asibitocinta. Idan gwamnati ta yi haka zai taimaka wajen gyara harkokin kiwon lafiya a Najeriya, domin jama’a ba za su rika zuwa abibitoci masu zaman kansu ba. Amma maganar a hana likitoci da suke aiki a asibitocin gwamnati bude asibitocinsu, ko kuma yin aiki a asibitoci masu zaman kansu ba zai taimaka ba, sai dai ya kara tabarbarar da harkokin kiwon lafiya  a Nijeriya.”

 

 

Hana su alheri ne – Aisha Mbaka

John D. Wada, Nasarawa

Aisha Mbaka: A gaskiya na yi matukar murnar samu labarin shirin gwamnati na hana likitocin asibotocin kasar nan aiki a asibitocin kansu ko na kudi wadanda suka bude wasu ma har a gidajensu. A gaskiya wannan ba alheri bane. Kuma su wadannan likitoci babu wanda ya kai su tafiya yajin aiki akai-akai a duk lokaci da ba a biya su ba. Amma sai ya kasance ba sa zama a asibitoci su gadanar da ayyukansu yadda ya kamata. Shi yasa galibin marasa lafiya a kasar nan ke tafiya kasashen waje don neman magani. Saboda haka zan yi matukar farin ciki idan gwamnati ta aiwatar da wannan shirin.