Hana shigo da motoci ya kassara mutum miliyan 10 – Yahaya Kega
Shugaban kungiyar dillalan motoci ta Nijeriya reshen Jihar Filato, kuma shugaban kamfanin sayar da motoci na Kega Motors da ke garin Jos, babban birnin jihar Filato, Alhaji Yahaya Muhammad Kega ya bayyana cewa, sama da mutane miliyan 10 ne suka rasa hanyar samun abinci, sakamakon hana shigo da motoci ta kan iyakokin kasar nan. Alhaji […]
Shugaban kungiyar dillalan motoci ta Nijeriya reshen Jihar Filato, kuma shugaban kamfanin sayar da motoci na Kega Motors da ke garin Jos, babban birnin jihar Filato, Alhaji Yahaya Muhammad Kega ya bayyana cewa, sama da mutane miliyan 10 ne suka rasa hanyar samun abinci, sakamakon hana shigo da motoci ta kan iyakokin kasar nan. Alhaji Yahaya Muhammad Kega ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.
Ya ce a gaskiya daga lokacin da aka kafa dokar hana shigo da motoci ta kan iyakokin kasar nan zuwa yanzu, mun shiga cikin wani mawuyacin hali. Domin shi dan kasuwa duk lokacin da aka toshe masa wata kofa, da yake saye da sayarwa dole ne zai shiga matsala.
Ya ce babu irin abin da basu yi ba, domin gwamnati ta gane cewa wannan doka tana cutar da ‘yan kasa, musamman mutanen jihohin arewacin kasar nan. Domin ta kan iyakokin kasar nan da ke Arewacin Najeriya ake shigo da motocin nan, kuma mutane suna amfani da wannan dama, suna samun abin da suke ci da iyalansu. Amma an rufe kan iyakokin kasar nan, an hana shigowa da motoci.
Ya ce ba kowa ne yake iya zuwa Legas ya sayo mota ba. Kuma mutanen da suke zuwa Turai su sayo mota su kawo Legas, ba za su iya wadatar da ‘yan Najeriya da motocin da suke bukata ba.
“Don haka mun sami koma baya a wannan kasuwanci na sayar da motoci a Nijeriya kwarai da gaske. Kuma wannan matsala ta shafi mutane da yawa a Nijeriya. Muna da mutane da dama da suke cin abinci da iyalansu ko’ina a Nijeriya ta hanyar wannan kasuwanci. Sama da mutum miliyan 10 ne suke cin abinci ta hanyar wannan kasuwanci domin muna da masu wannan kasuwanci a duk jihohin kasar nan, 36 har da babban birnin tarayya Abuja. Kuma ta hanyar shigo da motoci ta kan iyakokin kasar nan, ake samun gudanar da wannan kasuwanci” inji shi.
Ya ce sun zauna da Shugaban Hukumar Kwastan na kasa kan wannan al’amari, sun gaya masa damuwarsu, amma har yanzu babu wani mataki da gwamnati ta dauka kan wannan al’amari.
Alhaji Yahaya Kega ya yi bayanin cewa maimakon kafa wannan doka, kamata ya yi gwamnati ta tsaurara tsaro kan fasa kwauri kan iyakokin kasar nan, kuma ta saukaka kudin harajin fito, da kowa zai biya ya wuce ba tare da wata matsala ba.
Ya ce ko ada kafin a kafa wannan doka, duk da tsadar kudin fito wasu suna biyan gwamnati kudin fito. Ba kowa ne yake fasa kwauri ba.
Ya yi kira ga gwamnati ta sake duba wannan al’amari, ta hanyar kiran su ta zauna da su, domin su ba da shawara kan yadda za a warware wannan matsala. Ya ce babu shakka shawarar da za su bai wa gwamnati kan wannan al’amari zai sanya ta samu kudin da zai fi wanda take samu yanzu, kan wannan al’amari.