Hana shigo da shinkafa alheri ne ga manoma amma….

Shugaban kungiyar Manoman Shinkafa ta Jihar Kebbi Alhaji Muhammadu Sahabi Augie ya ce yunkurin hana shigo da shinkafa zuwa kasar nan daga waje nasara ce ga manoman kasar nan. Shugaban ya bayyana haka ne a tattaunawa da Aminiya a Birnin Kebbi, inda ya ce shirin a koma gona na wanna gwamnatin abin farin ciki ne […]

Hana shigo da shinkafa alheri ne ga manoma amma….

Shugaban kungiyar Manoman Shinkafa ta Jihar Kebbi Alhaji Muhammadu Sahabi Augie ya ce yunkurin hana shigo da shinkafa zuwa kasar nan daga waje nasara ce ga manoman kasar nan. Shugaban ya bayyana haka ne a tattaunawa da Aminiya a Birnin Kebbi, inda ya ce shirin a koma gona na wanna gwamnatin abin farin ciki ne da murna, domin bincike ya nuna wuraren da ba a noma yanzu an koma ana noma su, hakan ya kawo karuwar manoma masu yawa a kasar nan.

Shugaban ya ce, kafin zuwan wannan gwamnati masu sana’ar noma ba su samun ciniki sosai kuma shinkafar da suke nomawa ba ta tsada, amma hana shigo da shinkafar waje ya sanya shinkafar gida ta samu tagomashi a kasar nan da kasashen waje.

“Hakan na nuna idan wannan mataki na Shugaban kasa ya ci gaba da samun nasara nan gaba babu bukatar a shigo da shinkafa, kuma hakan zai zama babbar nasara ga manoman kasar nan,” inji Shugaban.

Ya ce lokacin da gwamnatin Buhari ta fito da shirin a koma gona, Jihar Kebbi ce ta fara sayar da buhun shinkafa a kan Naira dubu 6 har ta kai dubu 8, zuwa dubu 12, inda jihohin Najeriya ke zuwa su sayi shinkafar saboda haka su a Jihar Kebbi suna murna da hana shigo da shinkafa a kasar nan.

Ya ce manoma za su kara himma don noma shinkafa mai yawa da za ta wadaci kasar nan, inda ya ce komawa ga noman ya samar da aikin yi ga dimbin jama’a da kuma habaka tattalin arzikin Najeriya, inda ya ce yanzu haka suna da sunayen manoma dubu 85 da suka yi rajista da kugiyarsu. 

Ya ce idan aka kara rufe iyaka wajen hana shigo da shinkafar waje za su kara samun yawan manoma saboda shinkafar za ta kara yin daraja saboda rashin ta waje.

Wani manomi mai suna Abubakar Garba Besse wanda ya shaida wa Aminiya cewa lokacin rani yana noma shinkafa buhu dubu biyu zuwa dubu hudu, a damina kuma yana noma masara da dawa sama da buhu dubu hudu, ya ce noman da ya yi a bana ya sayar da buhu 1,500 na shinkafa a kan miliyoyin Naira. 

Ya ce manoma a Jihar Kebbi sun ci gaba domin a shekarun baya idan ka yi noma sai ka rasa wanda zai saya, amma yanzu idan ka noma shinkafar Naira miliyan 100 ma za a saye ta cikin sa’o’i kadan.

Dangane da hana shigo da shinkafa daga waje, Abubakar Besse ya ce akwai alfanu kuma akwai rashin alfanu. “Alfanun shi ne manyan manoma wadanda suka sa kudinsu suna noma sun fi son a hana shigo da shinkafa, saboda idan ana shigowa da ta waje manyan manoma za su rika faduwa a nomansu saboda ba za a saye ba, kuma kamfanoninmu na casar shinkafa za su durkushe, kuma matasanmu za su rasa ayyukan yi,” inji shi.

Ya kara da cewa: “Rashin alfanun shigo da shinkafa shi ne zai haifar da tashin farashin ta gida ta yi sama. Saboda haka idan gwamnati za ta hana shigo da shinkafar kwata-kwata to ya kamata a dauki abin a hankali. Misali a dauki shekara uku ana ba sashen noma muhimmanci kamar samar wa manoma da taki a kan lokaci kuma a farashi mai sauki da maganin feshi da iri ingantacce da kuma taraktocin noma manya da kanana. Kuma kada gwamnati ta ce ta hana shigowa da ita kwata-kwata, idan tamu ta gida ta yi yawa a cikin kasa ba sai gwamnati ta hana shigowa da ta waje ba, yawan tamu zai sa a manta da ta waje domin tamu ta fi inganci da kuma sa lafiya.”

Abubakar Besse ya ce a bana a Jihar Kebbi in ba Allah Ya gyara ba, noman shinkafar rani za a samu matsaloli musamman kananan manoma domin kuwa manomi ya saba sayen man fetur 145 yanzu ga shi tun a cikin watan 11 ake fama da tsadar man fetur, wasu wurare ma a kauyuka ba ka ganin man ballantana ka saya. Rashin man fetur da tsadarsa za ta kawo cikas ga noma a Jihar Kebbi.

Shi kuwa masanin noman ne kuma malami a sashin bincike da nazarin aikin gona na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Farfesa Salihu Adamu Dadari da wakilinmu ya tuntube shi kan jawabin na Shugaba Buhari cewa ya yi hana shigo da shinkafar alheri ne ga Najeriya.

Farfesa Salihu Dadari ya ce wannan mataki na hana shigo da shinkafa Najeriya ya yi daidai. Domin Najeriya tana da kasa da dausayi da rafukan da za iya noma kowace irin shinkafa da ake nomawa a duniya. “Don haka muna yi wa Shugaban kasa godiya kan daukar wannan mataki, muna fatar Allah Ya ba shi ikon aiwatarwa,” inji shi. 

Farfesan noman ya ce hana shigo da shinkafar zai kawo wa Najeriya rarar kusan Naira biliyan 700, saboda Najeriya tana sayo shinkafar wannan kudi daga kasashen Thailand da China da makantansu. 

“Duk kasar da za ta ware wannan makudan kudi domin sayo abinci daga kasashen duniya ta shiga uku. Domin duk kasar da za ta sayar wa wata kasa kaya, sai inda ta kai ta. Irin wannan sayo kayan abinci daga waje yana bai wa manoman kasashen da ake sayo amfanin gonarsu dama su bunkasa nomansu. Ita kuma kasar da take sayo kayan abincin, manomanta suna rage gonakinsu da masu aiki, ta haka sai a rasa aiki a kasar,” inji shi. 

Sai dai ya bukaci a tallafa wa manoman kasar nan da magungunan feshi da takin zamani a farashi mai rahusa, domin a samu nasarar wannan mataki na hana shigo da shinkafa daga waje. 

Ya ce akwai jami’an hana fasa kwuri su mike, su kara kokari kan kokarin da suke yi, don ganin an samu nasarar wannan mataki. Kuma ya bukaci ’yan Najeriya su bai wa gwamnati goyon baya kan haka. Domin matakin alheri ne da zai shafi kowa idan ana so Najeriya ta ci gaba, ta yi tasiri a kasashen duniya ta rika kai wa makwabta da sauran kasashen duniya shinkafa suna saye, ba su rika sayowa ba.

Dangane da ko shinkafar ake nomawa a Najeriya za ta iya wadatar da ’yan Najeriya, Farfesa Dadari ya ce, duk da cewa bai san adadin shinkafar da ’yan Najeriya suke bukata ba, ya san bana an noma shinkafa mai yawa a Najeriya. “A bara, Jihar Ebonyi ta tattara shinkafar da aka shigo da ita daga waje, ta hana sayarwa ta ce dole kowa ya ci shinkafar da ake nomawa a jihar. Abin da ya kamata a yi ke nan, domin wannan mataki alheri ne ga Najeriya baki daya,” inji shi. 

Da ya juya kan korafin da manoman alkama da masara suke yi kan faduwar farashinsu a bana, Farfesa Dadari ya ce a bara, a kasuwar bayan fage an sayar da buhun alkama kan Naira dubu 30 zuwa dubu 40. Wannan ya sanya monama suka yi noman alkama sosai a bana, kuma ta yi kyau sosai.  “Amma an wayi gari buhun alkama ba ya wuce Naira dubu 14. Su kuma manoman alkama suna tsammanin cewa tun da bara alkama ta yi kudi, dole ne bana ma ta yi.Ya kamata manoma su daina raina riba, idan suka yi noma suka samu riba, komai kankantarta kada su rika rainawa. Ita harkar rayuwa abi ta a hankali, a noman alkama idan manomi ya kashe Naira dubu 7, ya samu dubu 9 ko dubu 10, ya kamata ya gode Allah. Amma matsalarmu kowa ya yi noma, yana son ya samu fiye da abin da yake tsammani, abin da ya kamata shi ne mu tabbatar mun yi noman,’ inji Farfesan.  

Kuma ya ce tun da yanzu manomanmu, sun fara noman alkama da yawa, gwamnati ta tabbatar ta tana saye alkamar, kuma ta kyautata wa manoman ta ba su farashi mai kyau, su ci gaba da noma ta har su kai ga noma alkamar da za ta wadaci kamfanonin fulawa na kasar nan. 

Ya ce ita kuma masara da ake cewa farashinta ya fadi, ya ce ai ba faduwa ya yi ba domin dama a duk lokacin girbi, masara takan yi irin wannan faduwa. Sai ya ce abin da ya kamata gwamnati ta rika yi, shi ne ta rika bayar da farashi mai kyau kamar yadda aka taba yi a kasar Ruwanda, lokacin da Kamuzu Banda yake Ministan Gona, kafin ya zama Shugaban kasar.  “Ya kamata kafin a karanta kasafin kudin kasa kowane amfanin gona gwamnati ta fitar da farashin da take son a saya. Ta fadi takaitatcen farashi na amfanin gona wanda ta yarda shi. Kada wani dan baranda ya zo ya sanya kudi kalilan ya zalunci manoma. Idan aka yi haka za a samu mafita a Najeriya kan farashin kayan amfanin gona,” inji shi. 

Ya ce haka a jihohi idan gwamna zai yi kasafin kudi, ya yi bayanin cewa a bana farashin buhun masara ko na alkama da sauran kayan amfanin gona ga farashinsa, wannan ne zai bai wa manoma kariya. “Idan noman ya bunkasa gwamnati ta shirya tsarin ta yadda za a rika fitar da kayan amfanin gonar zuwa kasashen waje” inji shi. 

Farfesa Dadari ya shawarci manoma cewa kada su ji tsoro, domin noma zai tafi daidai. “Idan an ce yanzu ne za a sayi masara Naira dubu 10 kafin wata masarar ta zo, za ta iya kaiwa Naira dubu 20, ba haka muke nufi ba. Manomi na gaskiya yana son ya ci riba wadatacciya ba kazama ba. Idan kasuwa tana tafiya sai a samu riba, kada abin ya zama kamar kasuwancin fetur ana kawo fetur, wadansu suna boyewa don ya yi tsada,” inji shi. 

Ya tunatar da manoman cewa kasa ba ta zama wadatacciya, sai tana da abinci wadatatce. Kuma in kasa ba ta da wadataccen abinci, to ba ta da kwanciyar hankali. 

Game da halin da masu sayen shinkafa domin ci za su shiga kuwa Farfesa Dadari, ya ce dan Najeriya yakan dora wa kansa wani abu, wanda idan bai same shi ba, wani tashin hankali ne a wurinsa. “Amma gaskiyar magana wannan abu ba zai damu talakan Najeriya ba,” inji shi.