Hana talla a baro da bakin hanya ya jawo cece-kuce a Yobe
Dokar da gwamnatin Jihar Yobe ta kafa ta haramta talla a kura ko baro da kuma umartar masu shagunan wucin gadi da ke gefen tituna a Damaturu fadar jihar su gaggauta kawar da su ta haifar da cece-kuce da nuna rashin jin dadi daga ’yan kasuwa da jama’ar gari. Dokar ta hana tallace-tallace, Ma’aikatar Muhalli […]
Dokar da gwamnatin Jihar Yobe ta kafa ta haramta talla a kura ko baro da kuma umartar masu shagunan wucin gadi da ke gefen tituna a Damaturu fadar jihar su gaggauta kawar da su ta haifar da cece-kuce da nuna rashin jin dadi daga ’yan kasuwa da jama’ar gari.
Dokar ta hana tallace-tallace, Ma’aikatar Muhalli ta jihar ta ce dokar za ta fara aiki ne daga shekaranjiya Laraba, inda ta yi gargadin cewa duk wanda aka samu da karya ta ya yi kuka da kansa.
Dokar wadda ta zo ba-zata ga al’umma ganin yanzu ne garin yake farfadowa daga halin rashin tsaro na tsawon lokaci.
Da yake nuna rashin jin dadinsa kan kafa dokar, Shugaban kungiyar Muryar Talaka ta Jihar Yobe Malam Saleh Bakwaro ya ce an kafa dokar ce ba tare da tunani ba, ya ce duk da cewa watakila gwamnatin ta yi haka ne don wasu boyayyun dalilai, dokar na iya kawo nakasu ga tattalin arzkin jama’a.
Shugaban ya ce, yaya za a ce mutane na gudanar da kasuwancinsu ta amfani da kura don shiga sako-sako, saboda ba su da sukunin samun shaguna amma a hana su.
Ya shawarci gwamnatin jihar da hukumomin tsaro su sake duba lamarin.
Wani mai sayar da kayan marmari a kura da ya ce sunansa Umaru dan Jigawa ya shaida wa Aminiya cewa a yanzu bai san yadda zai yi ba, “An ce mu tafi kasuwa don kasa kayanmu to, in mun je wa zai bi mu tunda sai ranar Lahadi jama’a ke zuwa don cin kasuwar,” inji shi.
Ya ce barin garin Damaturu ya zame masa wajibi shi da abokansa tunda ba su da hanyar samu in ba wannan ba.
Malam Saminu Mai Doya, cewa ya yi wannan doka ta zo musu ne bagatatan kuma a ganinsa kora da hali ne ake yi wa baki da ke zuwa ci-rani, tunda akasarin masu talla da kura ba ’yan gari ba ne.
Duk kokarin da Aminiya ta yi don jin ta bakin Kwamishinan Muhalli na Jihar Alhaji Idi Barde Gubana kan lamarin ya ci tura, sai dai jami’in watsa labarai na ma’aikatar Malam Zubairu ya tabbatar da kafa dokar, ya ce an yi ne da kyakkyawar manufa.
Shugaban karamar Hukumar Damaturu Alhaji Kale Muhammad ya shaida wa Aminiya cewa bai san da dokar ba, kuma ya yi tafiya, da zarar ya dawo zai bincika.