Hancin dari biyu

Wani dan sanda ne ya dawo daga aikin dare, a bisa hanyarsa ta komawa wurin da yake kwana sai ya gamu da wani mutum yana tura baro dauke da talabijin da fanka da dibidi da katifa da sauran karikitan daki, irin na dakin tazuru.dan sanda ya ce: “Kai, daga ina kake cikin daren nan da […]

Hancin dari biyu
Hancin dari biyu

Wani dan sanda ne ya dawo daga aikin dare, a bisa hanyarsa ta komawa wurin da yake kwana sai ya gamu da wani mutum yana tura baro dauke da talabijin da fanka da dibidi da katifa da sauran karikitan daki, irin na dakin tazuru.
dan sanda ya ce: “Kai, daga ina kake cikin daren nan da wadannan kayan, kuma ina za ka da su?” Mutumin ya ce: “Na tashi daga tsohon gidana ne zan koma sabo, to shi ne nake so in kwashe kayan cikin sirri kafin gari ya waye.” dan sanda ya ce: “To, ka yi wani abu ka wuce.” Shi kuwa ya ce: “Yallabai ban fahimta ba?” Ya ce masa: “Ka ji wawa, kawo ko dari biyu ce, idan ba haka ba kuma, mu koma sai ka nuna mini gidan da ka taso din.” Mutumin ya dauki Naira dari biyu ya ba shi, ya kyale shi ya wuce da kayan.
dan sandan nan na zuwa dakinsa sai ya tarar da shi a bude. Yana shiga ciki sai ya ida tabbatar da abin da yake tunani. Ashe mutumin nan da ya gani, barawo ne ya zo dakinsa ya kwashe masa kaya.
Daga Mu’awuya Abubakar Zurmi

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50 a Kaduna

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54