Hancina na nan?

Akwai wani dattijo da mura ta sako shi a gaba, hancinsa na ta yoyon majina. Sai ya tafi wani kanti kusa da shi don ya sayi Robb ya shafa. Da ya isa kantin ya ce a ba shi Robb, sai mai kanti ya ce babu, ya tambayi Mistaleta, aka ce babu. Mai kanti ya ce […]

Hancina na nan?
Hancina na nan?

Akwai wani dattijo da mura ta sako shi a gaba, hancinsa na ta yoyon majina. Sai ya tafi wani kanti kusa da shi don ya sayi Robb ya shafa. Da ya isa kantin ya ce a ba shi Robb, sai mai kanti ya ce babu, ya tambayi Mistaleta, aka ce babu. Mai kanti ya ce Loko kawai yake da shi, amma yana da zafi sosai.
Dattijo ya ce wane zafi ne lokacin Yakin Basasa ba su gani ba, har barkono mai sa hawaye suke shaka. Mai kanti ya ba shi Loko. Dattijo ya ba shi Naira 500 a ba shi canji, mai kanti yana neman canji. Sai dattijo ya lakaci Loko ya sanya a kofar hancinsa daya, ya kara lakata ya sa a dayan.
Kafin mai kanti ya ba shi canji sai dattijo ya shiga tsalle, saboda tsabar radadi.
Mai kanti na kokarin ba shi canji sai ya ji dattijo ya ce: “Hancina na nan?” Mai kanti ya ce masa yana nan mana. Sai dattijo ya ce,  “Amma yana fesar da wuta ko?” Mai kanti ya fashe da dariya, sannan ya ce masa, a’a.
Bashir Musa Liman, 07036925654

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya