Hankalinka Jagoranka
Duk wanda ya bar abu don Allah, zai canja masa da wanda ya fi: 14 Duk wanda ya bari don Allah, tabbas Allah Yana canja masa da abin da ya fi wanda ya bari kyau da aminci da karfi. 15 Duk wanda ya yi abin da Allah ya ce ya yi, Allah zai saka masa […]
Duk wanda ya bar abu don Allah, zai canja masa da wanda ya fi:
14 Duk wanda ya bari don Allah, tabbas Allah Yana canja masa da abin da ya fi wanda ya bari kyau da aminci da karfi.
15 Duk wanda ya yi abin da Allah ya ce ya yi, Allah zai saka masa da abin da ya fi, duk da cewa Allah ne Ya ba shi ikon yin abin da ya yi, da wanda ya fi.
16 Duk wanda ya samu ilimi mai amfani ba zai rasa abu uku a duniya ba, sannan a Lahira, Allah Ya ba shi wanda ya fi.
17 Duk wanda ya amfana da ilimi za a samu yana aiki da shi na biyu ba zai yi girman kai ga Allah ba, da mutumin da ya fi shi da wanda shi ya fi.
18 Duk da cewa tawali’u da kankan da kan malami ko dalibi, bai barin a mayar da kansa dolo ko sakarai; zai rika girmama ilimi yana mutumta kansa da martabar ilimin da ya fi.
19 Duk wanda ya samu ilimi mai amfani ba zai yi mummunan zato ga waninsa ba, tsaransa ne ko na gabansa da wanda ya fi.
20 Duk wanda iliminsa ke amfanarsa za a same shi ko a same ta da wadannan halaye uku, ban da wadanda ke biye da su masu kyau da dadi kamar wakafi.
21 Duk wanda ya yi ilimin da ba ya aiki da shi, kamar yadda Allah (TWT) Ya fadi a Kur’ani, zai zama hujja a kansa har mutuwa su ne farkon shiga wuta mafi zafi.
22 Duk wanda ya ki bidar ilimin kuma, ko yana bin wanda bai aiki da ilimin, makomarsu daya, neman ilimi da yin aiki da shi ne ya fi.
23 Duk wanda zai yi ilimi bai rabu da girman kai ga Allah ko mutane ba, bai yi ilimi ba, duniyarsa ya nema wadda yake ganin ta fi.
24 Duk wanda bai nemi ilimin sanin Allah da sanin ManzonSa da yadda zai bauta maSa ba, mummunan zato a wurinsa shi ne zai fi.
25 Duk wanda ke aiki da ilimi tsakani da Allah, ba ya girman kai, ba ya mummunan zato, mafita yake nema ga kansa da waninsa, kuma shi ake so shi ya fi.
Za a iya samun Malam Mahmud Sabo Wushishi ta:
08055736329, 08034358678