Hankalinka Jagoranka
Barin sallama kan saduwa ko gamuwa a kan hanya: 26 Ba a sallama wa budurwa wadda ba muharramarka ba, ko ita ajanaba in akwai aure tsakaninku yankakke a kan hanya. 27 Ba a sallama wa budurwa ajanaba da nufin aure ba da izinin iyayenta ba, domin kasancewarta manisanciya. 28 Ba a sallama wa bazawara […]
Barin sallama kan saduwa ko gamuwa a kan hanya:
26 Ba a sallama wa budurwa wadda ba muharramarka ba, ko ita ajanaba in akwai aure tsakaninku yankakke a kan hanya.
27 Ba a sallama wa budurwa ajanaba da nufin aure ba da izinin iyayenta ba, domin kasancewarta manisanciya.
28 Ba a sallama wa bazawara cikin idda da nufin aure balle nema, amma ana iya daura auren ta da ta kare, tare da nema da yin magana, a ranar a lokaci daya.
29 Ba a son sallama da budurwa balle wani abin da zai biyo bayan sallamar, amma ba a hana sallama ga tsohuwa ba, ko a kan hanya.
30 Ba a amsa sallama ga wanda ko wadanda ba a yarda a yi masa sallama ba, sai dai ta al’ada ko a ce a kanku, ga masu tarbiyya.
31 Ba a sallama ga masu wasa ko masu saba wa Allah, ko dabbobi da wadanda aka san ba za su amsa ba, sai don sanayya.
32 Ba a hana yin sallama ga wanda ba a san halinsa ko addininsa ba, domin shi ko su za su san ka koda a kan hanya.
33 Ba a sanin addinin mutum in ya gamu da wani ko wadansu don sutura ko magana sai don sallama; ko a kan hanya.
34 Ba a sanin kai Musulmi ne ko ba Musulmi ba, sai in ka yi sallama, haka kai ma ba za ka san masayonka ne ba ko makiya.
35 Ba a barin sallama yinta ne ko amsata, a kan haduwa ko gamuwa da wanda ma ba ka sani ba, ko a kan hanya.
Barin sallama kan haduwa ko gamuwa a hanya, sai ga wanda aka sani, yana sanya kin dan uwa da daidaita su ko shi ko ita da makiya