Hankalinka Jagoranka

Ko ka yi sha’awar aikin banza ba ka son naka ya yi:   58. Ko ka yi sha’awar tsirancin wani ko shigar banza ko halin banza da wani ke yi ko ake yi wa wani, ba ka son a ce naka ne ke yi, ko ake yi mawa ba ka son ginin naka da shi, […]

Hankalinka Jagoranka
Hankalinka Jagoranka

Ko ka yi sha’awar aikin banza ba ka son naka ya yi:

 

58. Ko ka yi sha’awar tsirancin wani ko shigar banza ko halin banza da wani ke yi ko ake yi wa wani, ba ka son a ce naka ne ke yi, ko ake yi mawa ba ka son ginin naka da shi, ko ka kai shi wurin ya yi.

59. Ko iyayenka ba su da abin yi maka yanzu ka san Allah Ya sa su sun yi maka, abin da ba wani mai yi maka lokacin da kake yi musu fitsari da kashi da jinyarka da yi maka sutura da tsaron lafiyarka, ban da su wa ke son ya yi.

60. Ko ka so yi musu abin da suka yi maka, ba za ka iya ba, sai dai ka yi wa danka ko ’yarka ko ’ya’yanka, in kana da sauran hankali ba za ka kosa da iyayenka ba, komai kake yi musu ko su suka ce ka yi.

61. Ko ka san ba sai da kudi ne ake rayuwa ba, kamar rai, hankali, lafiya, abinci, sutura wurin kwana; in babu su ko ga kudi duk ba ka yi; Allah kadai ke ba da su in ba wadannan ba a jin dadi, ko ana neman kudi?

62. Ko ka san ga kowa da komai sai da ilimi ne za ka san mai kyau da mummuna, al’adar al’umma da mu’amalarta, ba su zama bidi’a cikin Musulunci, ba da an samu nassin da ya kore su ba, abin da ya kawo farin ciki ne kan kawo maka ma bakin ciki, sai in duka ba ka yi.

63. Ko ka san in kai ba Manzon Allah ba ne ko Annabi ko sahabin Annabi; in kana tsoron Allah, ba kamarka, musamman in malamin addinin Allah kake, in ba kai ne ka kaskantar da kanka da abin da Allah Ya ba ka a kan na waninka ba, ba a sanin Allah da ManzonSa da Sallah da komi, in babu kai duka ba a yi.

Za a iya samun Malam Mahmud Sabo Wushishi ta: 08055736329,

08034358678

Gwamnatin Yobe ta tallafa wa magidanta 53,000 da N3.91bn a 2024

Uwargidan Sanata Goje ta tallafa wa mata da matasa a Gombe

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano