Hankalinka Jagoranka

In ka ga mutum yana baya-baya da kai bayan ya sanka, dayan biyu ne: 112. In ka ga mutum yana baya-baya da kai, bayan ka san shi ya san ka, dayan biyu ne; in ba masharrancinsa kake ba, to, shi masharrancinka ne. 113. In muka lura da kowa da komai Mahaliccinmu Ya yi kowanemmu Yana […]

Hankalinka Jagoranka

In ka ga mutum yana baya-baya da kai bayan ya sanka, dayan biyu ne:

112. In ka ga mutum yana baya-baya da kai, bayan ka san shi ya san ka, dayan biyu ne; in ba masharrancinsa kake ba, to, shi masharrancinka ne.

113. In muka lura da kowa da komai Mahaliccinmu Ya yi kowanemmu Yana sonsa da gurbin da Ya ajiye shi in ka gane.

114. In ka taka wannan, sai wannan ya taso, kamar takun saka, amma Allah Bai boye mana mu bayinSa ba ko mene ne.

115. In ka ce Allah, Sai ka bi Shi, haka gida ko gari ko kasa ko al’umma guda ta addini, ban da saba maSa ka gane.

116. In kuma ka karyata Shi ko addininSa to, sai ka koma ga waninSa, a gida ko gari ko kasa da irinka a ko’ina ne.

116. In kana ga Allah dole ka bi Annabi da malamai mabiyansa da dogara da su da littafansu; shi Allah Bai son kishiya ne.

117. In ka kasance mai karyata Allah da ManzonSa, to, ba ruwanka da kowane malami sai fa in shi lauya ne.

118. In ka ki bin Allah, ba za ka ki bin hukuma ba, ta Allah ce ko ba ta Allah ba, bin doka da oda dole ne.

119. In ka tafi inda ba addini na Allah, suna da irin nasu dokokin, mai bin Allah da wanda bai bi tilas, ya bi, mutane ba dabbobi ba ne.

120. In babu bin Allah, kuma babu bin dokar hukuma ba a zaunawa lafiya, sai a koma ya dabbobi ko’ina ne.

Komai tsananin da zai sa ka yin barna da sabon Allah Mai jiranka ta fi ta in ba ka tuba ba:

121. Komai tsananin da zai sa ka saba wa Allah domin ka huta da tsananin nan duniya gara yin hakuri da tsananin, domin komai tsananin rayuwar duniya da dadinta masu karewa ne, amma ta Lahira ta fi tsanani, kuma wata a can ba za ta kare ba.

122. Komai tsananin rayuwar duniya da dadinta tarihi suke zama, kuma ga wadansu nan cikin tsananin da sabon da barnarsu suna son yin maganinta ko su fita su tuba ta ko’ina sun kasa fita cikin tsananin ko a nan duniyar, barnar da suka yi ba za su iya biyansu ba.

123. Komai kafirai ke yi na sabon Allah, tare da ci gabansu na harkokin duniya alkawarin da Ya yi musu ne, suna bin dokokin da suka riga suka kafa wa kansu ne dolensu, tunda ba na Allah suke bi ba, a nan Yakan fitine su ne su yi ta magani ba zai kama su da naSa ba in ba can Lahira ba.

124. Komai ilimin mutum na duniya, in bai yi na Lahira ba, da sunan Allah da girmama Allah, ko an ce masa ga dokar Allah, ko na gwamnati, ba ya bi sai inda bin zai kare shi kawai, ba waninsa ba.

125. Komai kokarin hukuma da sa doka da ’yan sanda kowa ya sani in yana da hankali in ba mai tsoron Allah aka sa tsare dokar ba, kuma shi mai tsoron Allah ne mai bin dokar ba, ba zai bar ra’ayinsa ba.

126. Komai ake yi tun daga gida da makaranta da wurin aiki na baya ne ake koyawa, kuma da su zai tashi ko za su ta tashi, masu wasan kwaikwayo ba su yin aiki da ilimi na addini sosai ga karancin shekaru, ana kuma daukaka darajojinsu da samun ciniki mai riba.

 

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato