Hankoron fita karatu kasashen waje
A makon jiya ne Shugaban Kwamitin Kula da Asusun Bunkasa Ilimin a Manyan Makarantu (TETFUND), Sanata Binta Masi Garba ta ce kasar nan tana kashe fiye da Dala biliyan biyu (kimanin Naira biliyan 400) don biyan kudin karatu ga daliban da ke neman ilimi a kasashen waje.Wasu za su iya kallon haka a matsayin shaida […]
A makon jiya ne Shugaban Kwamitin Kula da Asusun Bunkasa Ilimin a Manyan Makarantu (TETFUND), Sanata Binta Masi Garba ta ce kasar nan tana kashe fiye da Dala biliyan biyu (kimanin Naira biliyan 400) don biyan kudin karatu ga daliban da ke neman ilimi a kasashen waje.
Wasu za su iya kallon haka a matsayin shaida da ke nuna yadda iyaye suke son ’ya’yansu da ilimi, amma a hakika wannan manuniya ce ta yadda ake barna da rashin kishin kasa da kuma almubazzaranci a kasar nan.
Shugaban kungiyar Kula da Jarabawa ta Duniya, Mista Ike Onyechere ya taba yin wannan bayani a baya, inda ya ce Najeriya tana kashe fiye da Naira tirilyan daya da rabi kan karatun dalibai a kasashen waje.
A cewar Onyechere kasar Ghana tana samun Naira 160 daga wannan kudi a duk shekara, yayin da ’yan Najeriya ke kashe sama da Naira biliyan 80 don zuwa karatu a kasar Ingila. Wani rahoto da aka tattara a shekarar 2012 ya ce Najeriya ce take samar da kudin da bangaren ilimi na kasar Ingila ke dogaro da shi, inda ta samar mata da Naira biliyan 246, Rahoton ya kara da cewa, ’yan Najeriya da suke zuwa karatu a jami’o’in Birtaniya da Amurka sun kashe Naira biliyan 137 kan biyan kudin makaranta da na rayuwa a can a shekarar karatu biyu da suka gabata, ko kuma a ce kashi 34 cikin 100 na kasafin da Gwamnatin Tarayya ta kebe wa ilimi a wannan lokaci.
Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta ce ba ta kididdigar yawan ’yan Najeriya da suke karatu a kasashen waje, amma masu sanya ido suna ganin adadin da Sanatar ta ambata hakika yana kashin gaskiya.
A taron Kwamitin Bankuna da ya gabata, shugabannin bankunan sun nuna damuwa kan cewa kashi 15 cikin 100 na kudin musayar da Babban Bankin Najeriya ya kebe musu na tafiya ne ga biyan kudin karatu a waje. Babban Manajan Daraktan Bankin Access Bank Mista Herbert Wigwe ya ce babu hakikanin adadin nawa ake kashewa wajen biyan kudin makaranta a kasashen waje, amma rahotanni daga bankuna daban-daban sun nuna ba su gaza kashi 15 cikin 100 na daukacin kudin musaya ba. “Akwai mabambanta alkaluma game da yawan yaran da suke zuwa karatu kasashen waje. Wasu sun ce sun kai kusan miliyan daya. To idan muka dauka wadannan yara suna biyan Dala dubu 20 ko Dubu 30 ko dubu 40 a kowace shekara, adadin ba karami ba ne. Hakan na nufin akwai yiwuwar a bukaci Dala biliyan 20 ko ma fiye da haka,” inji shi.
Ana alakanta zumudin ’yan Najeriya na zuwa kasashen waje karatu da dalilai da dama kamar lalacewa da macewar kayan karatu a makarantu da almundahana a jami’o’i da kuma rashin wadatattun guraben karatu ga wadanda suke son karatu a jami’o’in.
Daga cikin fiye da dalibai miliyan daya da suke zaunawa daukar jarabawar shiga jami’a (JAMB) a kowace shekara, idan aka hada daukacin jami’o’in kasar nan za su iya bayar da gurabe ga dalibai dubu 300 ne kacal. Tura yara karatu a kasashen waje ya karu sosai a ’yan shekarun da suka gabata sakamakon yawan yajin aiki da kungiyoyin ma’aikatan jami’o’i ke yi, lamarin da ke jawo dalibai su shafe shekaru ba tare da sun kammala karatun ba. Gwamnatocin jihohi ma musamman na Arewa sun taimaka wa hakan ta hanyar tura dubban dalibai yin karatu a sassa da daman a duniya.
Abu mafi zafi game da lamarin shi ne daliban Najeriya sukan je karatu a kasashen da Najeriya take tallafa musu da malamai a karkashin shirin bayar dab tallafi na kasa (TAC). Kuma yayin da yaran Najeriya a baya ke zuwa Ingila da Amurka da Rasha, yanzu akwai dubban daliban Najeriya a kasashen Benin da Ghana da Sudan da Kenya da Uganda da Afirka ta Kudu da China da Maleysiya da Turkiyya da kubrus da Singapore. Ba sabon abu ba ne a ce jami’o’in kasashen waje suna cin riba daga Najeriya sakamakon yadda matasan Najeriya suke biyan dimbin kudi a matsayin kudin makaranta ga jami’o’in na waje. Wajibi ne a dakatar da wannan katobara. Idan da za a kashe wannan dimbin kudi a bangaren ilimi na kasar wasu za su iya yin tururuwa zuwa makarantunmu don yin karatu.
Wani abu kuma akwai bukatar gwamnati ta kawo karshen yawan yajin da kungiyoyin ma’aikatan jami’o’i ke yi ta hanyar aiwatar da yarjejeniyoyin da take yi da kungiyoyin. Kuma idan aka fahimci irin wadannan yarjejeniyoyi za su yi wahalar cikawa, sai gwamnati da kungiyoyin su sake dubawa su samu matsaya. Akwai bukatar a samu kokari na kasa wajen canja kayayyakin karatu da suka tsofe ko suka lalace a manyan cibiyoyin ilimi. A karshe, idan da za a kaddamar da yaki da cin hanci da rashawa domin gano tushen badakala a jami’o’in za a iya kawo gyara a wajen yadda suke sarrafa ’yan albarakatun da suke da su.