Hannu daya ba ya maganin kazamar miya
Kazantar Najeriya ta fi karfin tsofaffin hannaye musamman kazaman tsofaffin shugabanni, sojoji da fararen hula wadanda su ne matsalar Najeriya su yi maganinta. Maganinta sai sababbin hannaye ba matasa ba, gogaggun mutane wadanda ba su shiga rukunin masu mulki ba balle a bata su, ko su bi shanun sarki. Mun yi sa’ar samun Janar Murtala […]
Kazantar Najeriya ta fi karfin tsofaffin hannaye musamman kazaman tsofaffin shugabanni, sojoji da fararen hula wadanda su ne matsalar Najeriya su yi maganinta. Maganinta sai sababbin hannaye ba matasa ba, gogaggun mutane wadanda ba su shiga rukunin masu mulki ba balle a bata su, ko su bi shanun sarki.
Mun yi sa’ar samun Janar Murtala Mohammed da Janar Muhammadu Buhari a cikin sojoji kamar yadda muka samu su Sa Abubakar Tafawa Balewa da Sa Ahmadu Bello da Cif Obafemi Awolowo da Cif Akintola da Malam Aminu Kano da Alhaji Yusuf Maitama Sule a cikin fararen hula ’yan siyasa masu mutunci da rikon amana, adilai masu kaunar Najeriya da mutanen Najeriya, masu tsoron Allah da tausayin bayin Allah ba barayi ba.
Duk wadannan da na lissafo sun riga mu gidan gaskiya, kuma har yanzu ba a samu kamarsu ba balle wadanda suka fi su. Ba su da tarihin sata ko kisa ko zalunci, ba su bar wa ’ya’yansu abin kunya ba, sai kyakkyawan suna da tarihind a ba za a mance da su ba, har duniya ta tashi. Allah Ya jikan dukan Musulmi, Ya yi mana kyakkyawan karshe Ya sa mu gama da duniya lafiya, mu cika da imani, amin.
Yanzu Muhammadu Buhari ne kadai ya rage daga cikinsu, sai dai shi bai yi sa’ar mataimaka ba, ga shi ba dan siyasa ba, ba ya da malamai tsarkakakku masu tsoron Allah da za su rika nusar da shi tafarkin Allah a tsarkake kamar yadda Sa Ahmadu Bello ya yi muwafakar samun Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, Alkalin Alkalan Najeriya, ya rika nusar da shi da duk shugabanni masu mulki kan yadda za su gudanar da mulkinsu cikin adalci irin na Allah ba tare da son zuciya ba.
Wannan ya sa Sa Ahmadu Bello ya gina Bankin Arewa ya kafa Hukumar Sayen Amfanin Gona (Marketing Board) da kamfanin wutar lantarki na Arewa da Hukumar Aikewa da Sakonni duka a Kano. Ya gina Jami’ar Ahmadu Bello a Zariya ya gina Gidan Rediyo da Talabijin na Arewa, ya gina kamfanin buga jaridun New Nigerian da Gaskiya Ta Fi Kwabo da Kamfanin Bunkasa Masana’antu da Zuba Jari na Arewa (NNDC) da Masakar Kaduna (KTL), ya gina wurin kera kayayyakin yaki (NDI) duka a Kaduna.
Kamfanin NDI tare da na Brazil aka kafa su, amma yanzu na Brazil yana kera kusan komai na kayan yaki har da jiragen yaki na sama da na ruwa da makamashin Nukiliya kuma yana kera jiragen kasa da motoci da sauransu. Amma mu sojoji suka mayar da namu kamfanin na yin kujeru da gadaje, bayan sun kashe Firimiyar Arewa Sa Ahmadu Bello da Firayi Minista Abubakar Tafawa Balewa.
Sardauna ya yi dubi ne da cancanta da dacewa wajen kafa wadannan bai ce komai sai a Sakkwato ba.
Kuma Sa Ahmadu Bello ya rika taimaka wa mabukata a lokacinsa har da masu rayuwa tsirara a kan duwatsu da masu sa ganye a matsayin sutura, ya rika ba su sutura ta kamala.
Yanzu ana maganar cewa shugabannin da suka biyo bayansu sun sace mana Dala biliyan 450 sun kai wasu kasashe sun boye an kasa kwatowa balle a dawo mana da su. Jagoran kwatowar tunda ya kamu da rashin lafiya ake kukan ’yan uwa da wadansu abokai da wadanda ya amince musu sun ci amanarsa, sun ci amanarmu, sun ci amanar kasa. Maimakon su tausaya masa su kwatanta irin yadda ta kasance a Kyuba tsakanin Fidel Castro da dan uwansa lokacin da Castro ya kamu da rashin lafiya tsawon shekaru, kanensa ya ci gaba da rike kasar kamar yadda Shugaban Kasar Fidel Castro yake gudanar da mulkin kasar babu wani bambanci har ya rasu komai na tafiya daidai babu wani bambanci kamar Castro yana raye.
Don haka tilas ne mu samar da sababbin hannu su shigo lamarin ceto da gyaran kasa ko ana so ko ba a so, idan har muna so mu samar da irin canjin da muke bukata na adalci ga kowa. Sabodaa haka sai mun nemi irin mutanen da suka san abin da ya faru kamar yadda na zayyano wasu a baya, ba wadanda ba su san komai kan abin da ya faru a kasar nan ba. Domin wanda bai san inda ya fito ba, ba zai san inda ya dosa ba. Wannan ne ya sa barayin shugabannin suke ta daddasa ’ya’yansu da surukansu don su ci gaba da ta’asa daga inda suka tsaya kama daga sata da kisa don mayar da mutanen kasa bayinsu, da ganin ba mu kwato dukiyar kasarmu da suka sace mana da kadarorin gwamnati da suka mallake da sunan sayar da hannun jari ba. Wannan danyen aiki da suka yi ya kai a ce an kashe wadansu ta hanyar harbewa kamar yadda ake yi ga barayin gwamnati a kasashen China da Iran, ya kai a rataye wasunsu, wadanda ya kamata a yanke wa hannu da kafa a yanke kamar yadda Allah Ya yi umarni a yi ga masu watsa fasadi a bayan kasa. Allah Wanda Shi ne Ya halicce mu Shi ne Ya tsara wannan ka’ida domin mu samu rayuwa mai dadi mai kyau da inganci, a samu adalci.
Su Sa Abubakar Tafawa Balewa da Sardauna da Malam Aminu Kano da Alhaji Yusuf Maitama Sule a nan Arewa da takwarorinsu na Kudu babu wanda ya tsaya dasa dansa ko dan uwansa ko surukinsa a harkar mulki ko ya gadar wa magadansa kazamar dukiya ta sata.
Hasali ma Sa Abubakar Tafawa Balewa da Sa Ahmadu Bello da suka yi shekara shida da rabi suna mulki an kashe su abin da suka bari wa magadansu bai kai dukiyar da shugaban karamar hukuma yake sata a wata shida ba a wannan zamani.
Saboda haka tunda Allah Ya sa Shugaba Buhari ya samu cikakkiyar lafiya ya wajiba ya kafa kwamiti na musamman mai karfin shari’a, don kwato dukiyar talakawan kasar nan da aka yi wa wa-ka-ci-ka-tashi, ba sai ya jira ya sake cin zabe ba. Aikin yaki da cin hanci da rashawa da almundahana ba na Hukumar EFCC ko ICPC ko ’yan sanda kadai ba ne, Kuma a tabbatar mambobin kwamitin tsarkakakku ne wadanda ba su da wani zargi a kansu balle wadanda aka taba daurewa ko ake zargin sun yi sata. Kada a maimaita irin kwamitocin da aka yi a baya, wadanda suka ba da rahotanni kan wadanda suka yi sata amma ba a kwato ba, kuma ba a hukunta su ba. Marigayi Shugaba Sani Abacha ma saboda ya rasu ne ake terere a kansa ana cewa ya saci dukiya.
Olusegun Obasanjo yana kurkuku ’yan uwansa sojoji suka fito da shi suka kakaba mana shi a kan mulki ya ci gaba daga inda suka tsaya, lamarin da ya kawo suka sayar da dukan muhimman kadarorin gwamnati hatta gidajen ma’aikata manya da kanana a kasa da jihohi sun sayar, baya ga kamfanoni da muhimman hukumomi. Kuma a zamaninsa ne aka kara wa kasar nan bala’i ta hanyar kirkirar Boko Haram la’ada waje, idan ya daka musu tsawa su sara masa, shi ya sa ya yi ta yin abin da ya ga dama babu mai iya cewa komai.
Don haka akwai bukatar mu zamo mataimaka ga Buhari a samu irin Buhari da yawa a Najeriya idan ana so a gyara kasar nan, domin hannu da yawa maganin kazamar miya, don haka hannu daya ba zai iya maganin kazamar miya ba.
Alhaji Abdulkarim Daiyabu
Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya (MOJIN), Tsohon Shugaban Kungiyar ’Yan Kasuwa da Masu Masana’antu da Ma’adanai da Ayyukan Gona ta Jihar Kano, (KACCIMA)
08060116666, 08023106666.