Hanya mafi sauki da za ta kai uwargida gidan Aljanna

Assalamu alaikum ’yan uwa maza da mata musamman magidanta da ke bibiyarmu a wannan fili da muke tattauna lamurran da suka shafi zamantakewarmu da iyali da tarbiyya a bisa mahanga ta shari’a da kuma al’adunmu. A yau zan yi magana ne a kan garabasar da Allah Madaukaki Ya tanadar wa uwargida in har ta tsare […]

Hanya mafi sauki da za ta kai uwargida gidan Aljanna

Assalamu alaikum ’yan uwa maza da mata musamman magidanta da ke bibiyarmu a wannan fili da muke tattauna lamurran da suka shafi zamantakewarmu da iyali da tarbiyya a bisa mahanga ta shari’a da kuma al’adunmu.

A yau zan yi magana ne a kan garabasar da Allah Madaukaki Ya tanadar wa uwargida in har ta tsare abububuwa uku a nan gidan duniya za ta samu rabo mai tsoka a Lahira.

In muka dubi mu’amalarmu ta yau da kullum Allah Ya halicci mata a bisa wata irin daraja da ta dara ta maza irin yadda aka kebance su daga wahalhalu na nema da ciyar da kai.

Su kuma maza Allah Ya dora musu hakkoki na ciyarwa da kula na mata da ’ya’ya da iyaye da duk wani wanda ya jibince su.

Ta bangaren ibadoji kuma mata an kebance su da tsare ibadojinsu a cikin gidajensu yayin da maza aka dora musu fita masallatai da fita jihadi da sauransu.

Akwai ayoyi da hadisai da dama da suka yi magana a kan mace ta zauna cikin gidanta kuma ta tsare hakkokin da Allah Ya dora mata domin a gidanta za ta samu lahirarta.

Akwai Hadisin Annabi (SAW) da ya ce “Idan mace ta yi imani da Allah ta kiyaye salloli, ta yi biyayya ga mijinta za ta shiga Aljanna.”

Akwai wani Hadisin da yake cewa “Duk matar da ta mutu mijinta na yarda da ita za ta shiga Aljanna.”

Akwai kuma Hadisin da Annabi (SAW) ke cewa “Aljannar mace na karkashin tafin mijinta.” Ke nan idan har ba ta yi masa biyayya ta yadda zai yarda da ita ba, ba za ta shiga Aljanna ba.

Sau tari mata na yi mini tambayoyi cewa me ya sa muka fi magana a kan hakkokin maza, su mata ba su da hakkoki ne?

Sai in ce yadda maza suke da hakkoki haka mata suke da su, sai dai kamar yadda na yi bayani a sama kusan duk ribar ’ya mace ta rataya ne a dakin mijinta wanda saba wa hakan na iya jefa ta cikin hallaka.

Sannan na biyu, uwargida sai ki gode wa Allah da har ake yawan fadakar da ku a kan hakkokinku don kuwa Hausawa na cewa “Gyara kayanka ba ya zama sauke mu raba.”

Akwai wani sanannen Hadisi da Annabi (SAW) ya yi Isra’i da Mi’iraji yayin da aka zagaya da shi cikin wuta ya ce “Ya ganta cike da mata da masu kudi,” sai aka tambaye shi me ya sa mata suka fi yawa a wuta? Sai ya ce “Saboda suna saba wa mazansu.” Sannan ya yi umarnin su yawaita yin sadaka.

Uwargida ga garabasa sai dai sai an yi hakuri domin nasara tana tare da hakuri.

Na san irin barazanar da kuke fuskanta a gidajen mazanku, amma saboda ku a cikin gida kuke kuma sai abin da aka kawo muku, wanda kuma duk inda kuka ga biyayya tana tare da hakuri.

Da fatan Allah Ya sada mu da ladan masu hakuri,  Ya ba mu dacewa da Aljanna Madaukakiya.

Sanusi Hashim Abban Sultana

Mai sharhi ne a kan al’amurran da suka shafi yau da kullum.  Ya turo wannan sako ne daga Jihar Katsina.

Za a samunsa ta:

[email protected]

08065507271