Hanyar Damaturu zuwa Maiduguri na neman zama maƙabarta

Halin da babbar hanyar Damaturu zuwa Maiduguri take ciki, abu ne mai daga hankali. Sanin kowa ne cewa wannan hanya ce ta haɗa garuruwan Arewa maso Gabas, ita ce hanya ɗaya da ake shiga birnin Maiduguri daga ko’ina a faɗin Najeriya. Amma abin haushi da takaici a kullum sai ’yan ta’adda sun fito sun tare […]

Hanyar Damaturu zuwa Maiduguri na neman zama maƙabarta
Hanyar Damaturu zuwa Maiduguri na neman zama maƙabarta

Halin da babbar hanyar Damaturu zuwa Maiduguri take ciki, abu ne mai daga hankali. Sanin kowa ne cewa wannan hanya ce ta haɗa garuruwan Arewa maso Gabas, ita ce hanya ɗaya da ake shiga birnin Maiduguri daga ko’ina a faɗin Najeriya. Amma abin haushi da takaici a kullum sai ’yan ta’adda sun fito sun tare wannan hanya, wani lokaci su kashe mutane wani lokaci su tafi da mutane. Wanda hakan na jefa tsoro da fargaba a zukatan mutane musamman direbobi.

Yanzu a halin da ake ciki direbobin manyan motoci irin su Ludurious da tankoki da ƙananan motoci duk wanda ya zo Damaturu to fa a nan zai tsaya, domin kowa yana tunanin cewa a kowane lokaci ’yan ta’adda za su iya fitowa. Yanzu har ta kai daga Damaturu zuwa Maiduguri idan mutum zai je sai ya biya Naira 1000 a tashar gwamnati a tashoshin ’yan kasuwa kuwa Naira 1,500 zuwa 2000, wanda a baya Naira 500 ne zuwa 600. Ganin cewa ba kowane direba ba ne yake  kasadar zuwa.

Shin sai yaushe ne al’ummar Najeriya za su samu cikakken tsaron lafiyarsu da dukiyoyinsu? A gaskiya kada mu yaudari kanmu, mu fito mu fada wa gwamnatocinmu gaskiya, domin suna neman siyasantar mana da rayukanmu da dukiyoyinmu.

Ku duba jama’a yadda aka girke jami’an tsaro a tsakanin wadannan jihohi biyu amma har yanzu a ce ana samun matsalar tsaro a kan hanyar. A gaskiya ya kamata Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohin Borno da Yobe su tashi tsaye domin magance mana wannan matsala domin tuni ta fara shafar tattalin arzikinmu, Na gode Aminiya.

Daga Idris M. Idris Damaturu Kakakin Kungiyar Muryar Talaka Reshen Jihar Yobe (08033775767)