Hanyar Funtuwa zuwa Tsafe ta zama tarkon mutuwa

Matafiyan da ke bin wannan babban hanyar musamman direbobi kamar yadda aka ambata a sun yi mata laƙabi da Isra’ila

Hanyar Funtuwa zuwa Tsafe ta zama tarkon mutuwa

Babbar hanyar motar da ta tashi daga garin Funtuwa a Jihar Katsina ta nufi garin Tsafe cikin Jihar Zamfara mai tazarar Kilomita 50, ta zama tamkar tarkon mutuwa ga matafiya, sakamakon yawaitar hare­haren masu garkuwa da mutane da ke cin karensu babu babbaka a kanta.

Direbobi da fasinjojin da ’yan kasuwa da sauran matafiya da ke bin hanyar domin gudanar da harkokinsu suna ɗaukar ta tamkar yankin Gabas ta Tsakiya ko yankin Zirin-Gaza saboda tsananin fargabar faɗawa hannun mahara.

Duk da cewa yanayin lafiyar titin bai yi tsanani ba kuma akwai jami’an tsaro da suka haɗa da sojoji, amma yin tafiya a hanyar mai nisan kilomita 50 daga Sheme zuwa Tsafe ya zama tarkon mutuwa ga matafiya a ’yan kwanakin nan saboda tsanantar kai hare-hare tare da ɗaukar mutane daga masu da ’yan ta’addan daji sukan yi.

Direbobin ’yan kasuwa da sauran masu bin wannan hanya, suna yi mata laƙabi da Isra’ila ba wai don tana Gabas ta Tsakiya ba ce, sai don suna ganin tazarar kilomita 50 tamkar Isra’ila ce, saboda tsananin kashe-kashe da ake aiwatara a kan hanyar daga Funtua zuwa Sheme ta zarce zuwa Tsafe.

Matafiyan da ke bin wannan babban hanyar musamman direbobi kamar yadda aka ambata a sun yi mata laƙabi da Isra’ila ba don komai ba sai don irin zubar da jinin bayin Allah da ake yi.

Jaridar Aminiya ta tattaro rahoton cewa, ’yan bindiga a kullum sukan kai wa matafiya da dama hare-hare tare da sace su a kan wannan hanyar.

Har ila yau, a kullum, duk al’ummomin da ke zaune a wannnan yanki mai tazarar kilomita 50 kacal, sukan fuskanci hare-haren ’yan bindiga da kuma sace wasunsu daga lokaci zuwa lokaci.

Wannan yanki da ke da tsawon kilomita 50 ya shafi ƙauyuka da garuruwan jihohin Katsina da Zamfara ne da suka haɗa da Sheme da Kamfanin Mai-Lafiya da Unguwar Boka da ’Yankara a Jihar Katsina da Ɗanwuri da Wanzamai da Kucheri da Unguwar­Chida da Magazu da Gidan-Giye da Tsafe a Jihar Zamfara.

Binciken da Jaridar Aminiya ta yi ya nuna cewa ’yan bindigar sun yi kunnen­uwar-shegu tare da nuna turjiya ga matakan tsaro da aka sanya a kan hanyar, inda suka ci gaba da tayar da zaune tsaye a kan matafiya da al’ummar wannan yanki.

A baya-bayan nan ’yan fashin dajin sun gudanar da jerin ayyuka ta’addanci a kan wannan hanya inda suka kai hari kan abubuwan hawa, tare da sace matafiya da ba a san adadinsu ba.

Kamar yadda Aminiya ta ruwaito, a tsakanin watan Yuli zuwa Satumba na wannan shekarar kaɗai ’yan bindigar dajin sun duƙufa wajen kai hare-hare a kan hanyar babu ƙaƙƙautawa.

Wakilinmu ya tattaro rahoton cewa waɗannan ’yan fashin daji sukan kai hari ga matafiya da ma’aikatan gine-ginen hanya da sauran al’umma dare da rana.

Wasu daga cikin ƙauyukan da waɗannan ’yan fashin daji kan kai hare-hare akai-akai su ne ƙauyukan Kamfanin-Mailafiya da ’Yankara da Magazu da Wanzamai da Kucheri.

Duk da cewa an samar da ƙarin shingayen binciken sojoji a tsakanin Kamfanin Mai-lafiya da Tsafe, har yanzu ’yan bindigar na ci gaba da munanan ayyukansu a ƙauyukan Kucheri da Gidan-Giye da Kanye kusan a kullum.

Aminiya ta samu rahoto cewa kowane mako wannan yanki yana fuskantar hare-haren ’yan fashi fiye da ɗaya. Hasali ma dai a wasu lokutta waɗannan ɓarayin daji sukan kai hari fiye da sau biyu a rana guda yadda idan sun kai harin sukan ci karensu babu babbaka.

Cikakken Rahoton a nemi Jaridar AMINIYA .

Yadda gwamnati ta yi sulhu da ’yan bindigar Kaduna

‘Da kuɗin yankan farce na je Hajji’

Zambar Intanet: EFCC ta kama ’yan China 4 da wasu 101 a Abuja

Gwamnan Akwa Ibom ya kori duk Kwamishinoninsa