Hanyar Kano-Abuja: Majalisa ta gayyaci Julius Berger

Majalisar Wakilai ta gayyaci kamfanin Julius Berger da ke aikin titin Abuja zuwa Kano ya gurfana a gabanta saboda rashin saurin aikin duk da cewar an samar da isassun kudin yin sa. Kazalilka Majalisar na neman bayani daga kamfanin kan tafiyar hawainiyar aikin titin Legas zuwa Ibadan da kuma gadar Neja ta biyu. Wakilin Aminiya […]

Hanyar Kano-Abuja: Majalisa ta gayyaci Julius Berger

Majalisar Wakilai ta gayyaci kamfanin Julius Berger da ke aikin titin Abuja zuwa Kano ya gurfana a gabanta saboda rashin saurin aikin duk da cewar an samar da isassun kudin yin sa.

Kazalilka Majalisar na neman bayani daga kamfanin kan tafiyar hawainiyar aikin titin Legas zuwa Ibadan da kuma gadar Neja ta biyu.

Wakilin Aminiya ya ambato majiya kwakkwara a Majalisar cewa jami’an Julius Berger za su bayyana a gaban Kwamitin Majalisar na Ayyuka a ranar 7 ga watan Yuli, sai dai majiyar ba ta yi karin haske ba.

Sama da shekara biyu ke nan kamfanin ke aiwatar da manyan ayyukan, sai dai korafe-korafe sun yawaita kan rashin kammala su.

Tun a watan Fabrairu Majalisar ta fara binciken tafiyar hawainiyar ayyukan duk da cewa an biya isassun kudin aiwatar da su.

Karo na biyu ke nan da kamfanin zai bayyana a gaban kwamitin kan rashin saurin aikin.

A watan Disamban 2019 ma majalisar ta gayyaci kamfanin kan wannan matsalar wanda a wancan lokacin gayyatar da hada da Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya da kuma Hukumar Kare Aukuwar Hadurra ta Kasa (FRSC).

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50