Hanyar samarwa kowa sana’a da kiwon lafiya
Kasancewar hakkin kowanne dan Najeriya, da tsaron lafiya yana hannun gwamnati, hakkinta ne ta tabbatar kowanne dan kasarta yana da sana’a ko aiki na rayuwar yau da kullum, gwargwadon basirar masu mulkinta da amanarsu da adalcinsu.Misali: Kowanne rukuni na daukacin al’ummar kasar a tarbiyyantar da su sana’o’i daban-daban, musamman wadanda gwamnati za ta dukufa wajen […]
Kasancewar hakkin kowanne dan Najeriya, da tsaron lafiya yana hannun gwamnati, hakkinta ne ta tabbatar kowanne dan kasarta yana da sana’a ko aiki na rayuwar yau da kullum, gwargwadon basirar masu mulkinta da amanarsu da adalcinsu.
Misali: Kowanne rukuni na daukacin al’ummar kasar a tarbiyyantar da su sana’o’i daban-daban, musamman wadanda gwamnati za ta dukufa wajen samo kasuwar su a kasashen duniya, kamar yadda ake fitar da gyada da auduga, kwara da ridi da karo da fatu da kiraga da kaho da makamantansu a da, wanda yanzu ana iya sarrafasu a nan gida Najeriya.
Hatta makafi da guragu da bebaye da makamantansu ana iya tarbiyyantar da su sana’ar da kowannensu zai iya yi. Kamar yadda makafin da guragun da tsofaffin suke saka tabarmar kaba da igiya da ragaya da faifai da mafici da kindai da mangala da gwado da luru da jaka da matasai na fatu, amma a da. Idan gwamnati ta binciko irin kayayyakin da kasashen duniya suke da bukata, sai ta dauki nauyin koyar da su a zamanance, ta ba su oda, duk yawan abin da suka sarrafa gwamnati ta saya, ta biyasu nan take. Sannan ta nada mutane da za su rika saya, suna fitar da su zuwa kasashen duniya (LBA’s). Ta haka ne kurum kowanne dan Najeriya zai sami sana’ar da zai rike kansa, ya dogara da kansa, ya rayu, kyakkyawar rayuwa a mutunce.
(2) Ina mamaki duk tutiyar ilimin masu mulkin mu har yanzu sun rasa yadda za su yi da shara, sun kasa tsaftace muhalli da magudanan ruwa. Mafi saukin al’amari shi ne, maimakon bada bashi (Micro finance) a rika bai wa matasa kananan kwangiloli (MICRO CONTRACT). Duk matasan da ake da su a raba musu kwangilolin yashe magudanan ruwa da kwashe shara zuwa wasu gurare da gwamnati za ta ware na musamman, inda za ta rika sarrafata zuwa takin noma na gargajiya, da sauran abubuwa na leda dana karafa. Hatta ‘yan kasuwa da manyan manoma za su iya hada gwiwa da gwamnati su aiwatar da wannan tsari na ci gaba, da rage shigo da Takin Zamani da nau’in abinci; shinkafa da alkama masu dauke da sinadarai masu cutarwa.
Muna gani ana shigo da taki da kayan abinci na biliyoyin Naira, amma talakawa na fama da yunwa saboda rashin kudin saye, sakamakon rashin sana’o’i da aiki. Idan da nine mai mulkin babu abin da zai hanani yin wadannan abubuwa da na wassafa, domin ba za su gagara ba idan aka maida kai cikin yardar Allah (S.W.T).
Abdulkarim Daiyabu
Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya
08060116666, 08173106666, 08023106666.