Hanyar Saminaka: Shekara 14 ana ware kuɗin gyara, amma kamar an shuka dusa

Babban titin da ya tashi daga Kaduna zuwa Pambeguwa zuwa Saminaka ya nufi Jos na da matuƙar muhimmanci, kasancewarsa wanda ya haɗa yankin Arewa ta Tsakiya da Arewa ta Yamma. Amma yanzu babbar hanyar ta zama tarkon mutuwa saboda tsananin lalacewarta, duk kuwa da irin biliyoyin kuɗade da Gwamnatin Tarayya ta yi ta warewa domin […]

Hanyar Saminaka: Shekara 14 ana ware kuɗin gyara, amma kamar an shuka dusa

Babban titin da ya tashi daga Kaduna zuwa Pambeguwa zuwa Saminaka ya nufi Jos na da matuƙar muhimmanci, kasancewarsa wanda ya haɗa yankin Arewa ta Tsakiya da Arewa ta Yamma.

Amma yanzu babbar hanyar ta zama tarkon mutuwa saboda tsananin lalacewarta, duk kuwa da irin biliyoyin kuɗade da Gwamnatin Tarayya ta yi ta warewa domin gyara titin, wanda aka fara ginawa shekara 34 da suka gabata.

Gwamanatin Tarayya ta fara bayar da gwangilar gyaran wannan muhimmiyar hanya ne a zamanin gwamnatin Marigayi Shugaba Umaru Musa ’Yar’Adua a shekarar 2010.

Amma har gwamnatocin Goodluck Ebele Jonathan da Muhammadu Buhari suka wuce, zuwa zamanin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, mai ci a yanzu, Gawmnatin Tarayya ba ta gyara titin ba.

Maƙalewar ababen hawa musamma a lokacin damina ya zama ruwan dare a hanyar, hakazalika yawan haɗari da lalacewar motoci da ke bin hanyar da tsawonta bai wuce kilomita 200 ba.

Mummunan yanayin hanyar sama da shekaru ashirin, sai ƙara taɓarɓarewa yake yi, inda ya zama abin tsoro ga matafiya da masu direbobi da al’ummomin ƙauyuka da garuguwan da ke kan titin.

Lalacewar hanyar

Wata majiyar da ke kan hanyar ta bayyana wa Aminiya cewa ababen hawa sukan maƙalewa sakamakon lalacewar hanyar wadda ta haɗa wani ɓangare na jihohin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.

Direbobi musamman na na manyan motoci suna samun kansu a cikin mawuyacin hali a sakamakon mummunan halin da hanyar take ciki, inda a mafi yawan lokaci santsi da laka da sauransu ke sa motocinsu maƙalewa ko kafkawa ramukan da ke gefen titi.

Wannan yanayi da a kullum ke yake ƙara taɓarbarewa inda ya zama abin tsoro ga masu ababen hawa da mazauna al’ummomin da ke kan wannan dogon titin.

Da zarar an samu kai a wannan hanyar da ta haɗa jihohin Kaduna da Filato, wadda matafiya da dama ke guje mata saboda hatsarin da ke tattare da ita, sai addu’a domin ga gajiyar jiki ga direbobi da fasinjoji da kuma yiwuwar lalacewar manyan motoci saboda ramuka mummunan yanakin hanyar mai tsawon kusan kilomita 199.50.

Kamar yadda rahoto ke nunawa akasarin masu ababen hawa sukan ce ɓangaren Saminaka zuwa Jos a hanyar ya fi sauran lalacewa.

A yayin ziyarar, wakilinmu ya lura cewa, motoci da dama a yanzu sukan daina hawa kan hanyar sai dai raɓawa ta ƙasan hanyar, in banda manyan motoci da ke kasadar bi ta cikin manyan ramuka.

Zullumin masu ababen hawa

Da yake bayyana takaicinsa, wani direban babbar mota mai suna Aminu Yari, wanda motar sa ta maƙale ta kuma karkace a cikin wani rami yayin da wasu matasa da ke ba da agajin gaggawa ga masu motoci irin ya hakan, ya ce lamarin ya faru ne duk da ƙoƙarin da ake yi na tafiya a hankali.

Ya ce, “Muna kan hanyarmu ta zuwa Jihar Kano sai motarmu ta maƙale a cikin laka da misalin ƙarfe 1 na dare,.”

Yari ya ƙara da cewa yunkurin fita daga cikin laka ya ci tira, don haka ya buƙaci “Gwamnatin Tarayya ta taima ta sanya baki wajen tabbatar da cewa an gyara hanyoyin da suka lalace a faɗin kasar nan, domin wannan titin misali ɗaya ne na tituna da yawa da ke matuƙar bukatar gyara a faɗin Nijeriya, kuma ko da ma gyara ne na wucin gadi, gara a yi shi, kasancewar gyaran hanya ya fi dacewa da a bar ta a halin da take ciki,” inji shi.

Ana cikin hakan ne wakilinmu ya samu ganawa da wani direban motar da ke maƙale a cikin wani rami mai zurfi a kan hanyar, Jamilu Tukur, wanda ya shaida wa wakilin namu cewa sun shafe kwanaki biyu a maƙale.

“Duk da muna aiki dare da rana, ba mu iya cire motar ba, mun kasance a maƙale na kwanaki saboda hanyar ta lalace gaba ɗaya, hasali ma da muka iso nan mun tarar da wasu motoci guda biyu su ma sun maƙale,” inji shi.

Malam Isa Muhammad, direban tasi ne da ya shafe sama da shekara 20 yana aikin tuƙi a kan hanyar, ya ce, lamarin ya ƙara taɓarɓarewa a shekarun bayan nan.

Ya ce a duk lokacin da yake kan hanyar Saminaka, idan motarsa ko ta ’yan uwansa direbobi suka makale a cikin laka, sai sun nemi taimakon matasa don wajen ciro ta.

“Ba da nisa ba daga nan, akwai motoci uku da suka maƙale a cikin laka. Ba za su iya motsawa ba, don haka suna buƙatar su nemo mutanen da za su cire musu motocin nasu,” in ji shi.

Yin zaɓe bai yi mana rana ba

A cewarsa, “Mu al’ummar ’yankin nan ba mu cin gajiyar mulkin dimokuraɗiyya domin ba mu fahimci manufar zaɓe ba saboda ba mu samun wata riba daga shugabannin siyasa .

Ya ƙara da cewar, “ka yi tunanin a ce an samu marar lafiya da ke da buƙatar yin gaggawa don kai shi asibitin ko kuma mace mai ciki wacce ita ma tana da buƙatar kai ta asibiti cikin gaggawa.

“To idan haka ta kasance yaya za ka yi da bin wannan wadda hanya, wadda in ba wani ikon Allah ba, kafin a kai majinyacin da ke buƙatar kular gaggawa, jinkirin da za a samu kafin kai shi asibi saboda wahalar da ke tattare da bin wannan hanya, a tarar da majinyacin ya kai ga rasa rai.”

Don haka ya bukaci gwamnatin tarayya da ta kawo ɗaukin gaggawa don sake gina hanyar lura da cewa tana da matuƙar muhimmanci mausamman ga manoma da al’ummomin yankin da ke gudanar da harkokin sufuri a kanta.

Ƙoƙarin aikin gayya

A cewarsa, shekaru da dama wasu matasa ’yan sa kai da suka fito daga yankuna daban­daban suna aikin cike ramukan da ke kan hanyar da yashi da duwatsu don sauƙaƙa wa masu abubuwan hawa.

Duk cewar, suna wannan ƙoƙari na cike ramukan kan hanyar amma daga bisani matasan suka fara nuna alamar gajiya lura da cewar sun ɗauki lokaci suna yi amma gwamnatoci ta yi biris da ita.

Da suke zantawa da wakilinmu, wasu daga cikin matasan sun bayyana cewar, lalacewar hanyar mota ta yi muni matuƙa, lura da cewar a kullum abin ƙara ta’azzara yake yi, domin a kowane lokaci masu abubuwan hawa sai azaba suke sha sakamakon munin hanyar da ke haddasa lalacewar motocinsu.

A jawabinsa jagoran matasa ’yan sa-kai da ke fafutukar toshe ramukan da kan wannan muhimmiyar hanya, Ibrahim Ɓaro Aiki, cewa ya yi sun ɗauki shekaru da dama suna gyara hanya, don haka yake kira da roƙo ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta shigowa cikin wannan lamari kafin ya kai ga taɓarɓarewa gaba ɗaya.

“Muna debo duwatsu a kodayaushe domin cike ramukan da ke kan wannan hanya, amma a kullum hanyar na cigaba da taɓarɓarewa duk da ƙoƙarin da muke yi wadda a yanzu har ta kai ga fin ƙarfinmu,” in ji shi.

Don haka ya roƙi jami’an gwamnati da su kawo ziyarar gani da ido don su gane wa kansu irin lalacewar da wannan hanya ta yi.

“Mun yi imanin cewar, matukar sun ziyarci wannan hanya don gane wa idonsu irin lalacewar da ta yi, akwai yiwuwar ɗaukar matakin gaggawa don sake gyara ta,” in ji shugaban matasan.

Shi kuwa Muhammad Rabi’u, wani mazaunin Kwanar Bauda, da ke noma wata gonarsa da ke maƙwabtaka da babbar hanyar, ya ce akasarin masu ababen hawa sukan guje wa bi ta hanya ta Jos zuwa Saminaka musamman a lokacin damina saboda lalacewar da motocinsu suke yi ga kuma samun jinkirin isa wuraren da suke so su je.

“A cewarsa, a mafi yawan lokaci idan aka yi rashin sa’a wata babbar mota ta faɗi akan wannan hanya sai ka tarar da ta tare hanyar gaba ɗaya yadda masu abubuwan hawa kan rasa wurin shigewa don zuwa wuraren da suka nufa, wadda hakan babbar matsala ce,” in ji Rabi’u.

“Hakan takan sa a mafi yawa-yawan lokaci za ka tarar da masu abubuwan hawa in hakan ta kasance, suna bi ta cikin gonakinmu yadda suke lalata mana amfani gona don samun hanyar wucewa wadda kuwa mukan cutu matuƙa.”

Hakimin kauyen Federe a Ƙaramar Hukumar Lere, Umaru Babangida Ubale, a yayin hirarsa da wakilinmu kan wannan lamari, kada baki ya yi ya ce, lalacewar hanyar ta haifar da asara ga mazauna yankin da daman gaske, wanda kuwa abin babu daɗi ko kaɗan.

Shekara 34 da ginata babu gyara

Basaraken ya zaga da wakilinmu domin duba yananin hanyar, wadda ya ce an gina ta ne tun lokacin Asusun Rarar Man Fetur (PTF) a shekarar 1990.

A cewar basaraken, “tun daga lokacin ba a sake gyara wannan hanya ba alhali a mafi yawan lokaci direbibin motocin haya da ke fitowa daga Fatakwal da sauran garuruwan kudanci na biyowa ta wannnan hanya zuwa Kano da sauran wurare, amma a yanzu lamarin ya sauya sakamakon lalacewar wannan hanya.”

Ya kara da cewar “a mafi yawan lokaci lalacewar wannan hanyar mota tamu kan sa motoci da dama faɗuwa wanda hakan ke haifar da babbar asara.”

A cewarsa yawaitar haɗɗuran da ake samu a wannan hanya kan haifar da asara ga al’ummar yankin musamman ma manoma da ’yan kasuwa waɗanda kan biya kuɗi mai yawa kafin a kai musu amfanin gonar da suka noma zuwa gidajensu da kuma kasuwanni domin sayarwa a samu ɗan abin kashewa saboda lalacewar hanyar.

Gyara hanyar ya gagara

Duk da aikin kwangilar sake gyara wannan hanya daban-daban da aka bayar a kuma lokuta daban-daban, har yanzu babu ko da guda ɗaya da aka kammala.

Wannan hanyar mota ta Kaduna Marabar Jos ta bi ta Pambeguwa Saminaka da Jos an bayar kwangilar sake gyara ta a shekarar 2010 ga kamfanin P.W Nigeria LTD a lokacin tsohuwar gwamnatin Marigayi Umaru Musa ’Yar Aduwa da wa’adin shekara guda na kammalawa amma har kawo yanzu shiru kake ji.

Har ila yau a watan Disambar shekarar 2020, gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ta sake ba da kwangilar aikin sake gina wannan hanyar ga Kamfanin Setraco Nigeria LTD a kan jimilla kuɗi Naira biliyan 38.5 da wa’adin watanni 12 don kammala shi, amma aka tsayar da aikin a ƙauyen Kayarda tsakanin Pambeguwa da Saminaka, kuma tun daga lokacin babu amo babu labarin ci-gaba da aikin.

Hakazalika wannan hanya, ma’aikatar kula da ayyuka, hanyoyi da gidaje ta tarayya ta sake ba da aikin gyaranta a shekarar 2020.

Har ila yau a 2020 an ware kusan Naira biliyan 38, don gudanar da aikin amma saboda tsadar kayan aiki, ma’aikatar ta yanke shawarar raba aikin zuwa kashi na daya da na biyu.

A farashin kayan da ake sayarwa a yanzu, kashi na daya kaɗai zai ci zunzurutun kuɗi kimanin Naira biliyan 33, domin har yanzu ɗan kwangilar zai sake yin wasu gyare-gyare a kan hanyar don ƙara mata ƙarfi,” in ji shi.

Ya ce gaba ɗayan aikin titin da aka ƙiyasta zai laƙume kusan Naira biliyan 98,761.

A cewarsa yanzu, “kashi na biyu zai je matsayin BPP ba tare da takardar shaidar hakan ba wadda za a miƙa ga majalisar zartarwa ta tarayya don neman amincewa wanda zai kai ga fara aiki a mataki na biyu bayan amincewar ta,” in ji shi.

Ya ce har yanzu ɗan kwangilar yana bin bashin Naira biliyan 15, inda ya ƙara da cewa: “Gwamnati ta biya shi rabin kuɗin sannan ta buƙace shi da ya nemi sauran rabin don cigaba da aikin, amma gwamnati za ta biya idan ta samu daga baya.

Don haka, a yanzu, duk wani aikin da ɗan kwangilar zai yi za a tantance shi ta hanyar takardun shaida daga BPP da amincewar majalisar zartarwa ta ƙasa (FEC) .

Wannan ba zai yiwu a wannan shekara ba, don haka sai a kasafin kudin shekara mai zuwa ta 2025,” in ji shi.

 

Mun kusa kawo ƙarshen rikicin manoma da makiyaya — Tinubu

Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na Gombe, ya rasu

Matatar Dangote ta rage farashin man fetur 

Na kusa zama ɗan ƙwaya a baya — Obasanjo