Hanyoyi biyar da ke haifar da gautsin fata

Assalamu alaikum matan gidan nan. Yaya sanyi da yara, tare da fatan ana cikin koshin lafiya. Akwai abubuwa da dama da sanyi ke janyo wa  fata, kamar gautsin fata da sauransu. Don haka ne a yau na kawo muku yadda  wadannan al’amura ke faruwa da kuma yadda za a magance su.  A sani cewa fata […]

Hanyoyi biyar da ke haifar da gautsin fata
Hanyoyi biyar da ke haifar da gautsin fata

Assalamu alaikum matan gidan nan. Yaya sanyi da yara, tare da fatan ana cikin koshin lafiya. Akwai abubuwa da dama da sanyi ke janyo wa  fata, kamar gautsin fata da sauransu. Don haka ne a yau na kawo muku yadda  wadannan al’amura ke faruwa da kuma yadda za a magance su.  
A sani cewa fata ita ce mace, in ta yi kyau za ta rika haskawa a lokacin tashen shekarunta; in kuwa ta baci lallai tsufan mace zai bayyana da wuri, ko da ba ta kai shekarun ba.
A sha karatu lafiya.
•Rashin shan isashen ruwa; ruwa na da matukar mahimmanci a fata. Don haka ya kamata a dage da shan ruwa da kuma cin kayan lambu da kuma ’ya’yan itatuwa. Rashin shan ruwa na haifar da gautsin fata.
• Amfani da sabulu mai zafi; yawan amfani da sabulan dake dauke da sinadarai masu karfi na illatar da fata da kuma haifar da samun gautsi a fata. Don haka sai a kula. A samu sabulu wanda ba su dauke da sinadaren illatar da fata kamar su sabulan yara da sauransu.
•kura; yana karya sinadarin bitamin A a jiki wanda ke da mahimmanci wajen gyaran mataccen fata. A rage bude fatar jiki a wajen da ke da kura. Domin ba iskar gari kawai ke kawo shi ba, shan taba sigari ko kuma zama a inda ake sha zai iya zama matsala ga lafiyar fata.
•Shafe-shafe;  yawan amfani da kayan shafe-shafe da ake yin su da sinadaran maiko na shanye maikon da ke cikin fata, kuma hakan yakan haifar da yamutsewar fata.
•Amfani da mayuka masu dauke da turaruka masu karfi; matsalar dake tattare da amfani da irin wadannan mayuka shi ne, yawwan shafa ta a lokuta da dama, yin hakan na sanya sinadarin da ke gyara fata  ya daina amfani a jikin mutum.