Hanyoyi biyar da ke haifar da gautsin fata
Assalamu alaikum. Editan Aminiya, ka ba ni dama in nuna takaici na dangane da yadda wasu mara sa kishin kasa suka kasafta kudin da aka ware domin tabbatar da tsaro a yankinmu na Gabashin Arewa da rikicin Boko-haram ya tagayyara, tare da haifar da mummunan koma baya. Hakika wannan batu bai zo mana da mamaki […]
Assalamu alaikum. Editan Aminiya, ka ba ni dama in nuna takaici na dangane da yadda wasu mara sa kishin kasa suka kasafta kudin da aka ware domin tabbatar da tsaro a yankinmu na Gabashin Arewa da rikicin Boko-haram ya tagayyara, tare da haifar da mummunan koma baya. Hakika wannan batu bai zo mana da mamaki ba, ganin yadda muke ji ana ta lissafin milyoyin kudi a zamanin mulkin PDP da sunan tabbatar da tsaro, amma muka kasa ganin komai, illa ma dada fuskantar hare-hare, kashe-kashe da sace-sacen mutane ake yi. To mu dai al’ummar Arewa maso Gabas da aka ci amanar mu, tare da ba da kafar durkusar da yankinmu, ba abin da za mu ce wa wadannan jama’a da suka kasafta kudinmu a al’jihunsu, illa Allah ya musu abin da suka yi mana. A bangare daya kuwa, muna kara jinjina da godiya ga shugaban kasa kan wannan aiki nasa na yakar ‘yan fashi da alkalami, muna addu’ar Allah ya ba shi nasara, Allah ya kuma kare sa daga dukkan sharrin da munafurcin makiyanmu da kasarmu. Daga Usman bin-affan damaturu, dalibi a jami’ar maidguri. 08038001563 [email protected]
Nasiha ga iyayen ’yan mata
Assalamu alaikum Aminiya ina tare da ku a kowane mako, Allah Ya taimake ku. Don Allah ku mika nasihata ga iyayen ’yan mata kan su taimaka musu, su rika aurar da su a lokacin da ya fi dacewa. Daga Zainab Musa Bauchi 08109967691.
Kira ga Gwamnatin Kaduna
Salam.Ina gaida ’yan uwa ma’abota karatun jaridarmu, mai farin jini da ’yan uwana mata da matasa. Ina kira ga gwamnatin Jihar Kaduna. Mun gode wa gwamnati da samun gada da titin hayin Malam Bello. Yanzu kuma bukatarmu, ita ce makarantar Firamare da Sakandare. Saboda yanzu ’ya’yanmu sai dai su tsallakawa babban titi suke yi, sannan su je makarantar Kagoro ko Kargi. Muna rokon gwamnati su taimaka mana saboda mutuwar yaranmu a wannan hanya. Nagode. Daga Aishatu Kabala.08166339024.
Kira ga Gwamnan Zamfara
Salam Edita dan ka ba Ni dama in yi kira ga Gwamna Abdul’azizu Abubakar Yari na Jihar Zamfara, kuma gwamnan gwannonin Najeriya. Don Allah ya taimaki matasan Jihar Zamfara ta hanyar fitowa da hanyoyin samar musu ayukkan yi. Domin gaskiya halin da matasa suke ciki yanzu a Jihar Zamfara ya yi muni matuka. Ganin yadda gwamnan ya ke nuna halin ko-in-kula ga matasan jihar. Wanda yanzu haka sama da shekaru hudu ke nan matasa na kare makaranta, amma ba aiki, haka ba wani tallafi da ake bai wa ‘yan kasuwa ko kirkiro hanyoyin dogaro da kai. Daga Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau. 08069807496 [email protected].
Addu’a ga Janar Burtai
Salam. Ya maigirma Babban Editan Amintacciyar jaridar mu, mai tarin farin jinni (AMINIYYA). Ina son a mikamun sakon gaisuwata ga mai girma Sayyeed Tukur Yusuf Burutai (H). Da fatan Allah ya dafa masa shi da abokan aikinsa, Allah ya ja zamanin rundunar sojan kasar nan, ya ja zamanin kasar mu (Najeriya). Aamin. Daga Abdurrazak S.Inuwa 08051210606.
Kira ga masu tukin ganganci
Edita ka isar min sakona ga irin direbobi masu tukin ganganci lokacin da suka loda fasinja. To ku sani wadannan fasinjojin da kuka dauko rayukansu da lafiyarsu da dukiyarsu amana ce a gareku. Don haka ku natsu ku kiyaye wannan amana da kuka dauka. In kuwa kuka ki daina tukin ganganci, har ya kai ga yin hadari. In jinin su ya zuba, ko suka rasa rayukansu, to ku sani Allah yana ganinku, kuma zai tambaye ku wannan amana. Idan kunne ya ji, jiki ya tsira. Daga Malam-Malam Mai zanen hula Gololo 08032822433.
Kira ga jami’an tsaro
Salam. Ina so ka ba ni dama in yi kira ga jami’an tsaron kasata Najeria, musamman wadanda suke fagen fafatawa da ‘yan ta’dda kayar baya. A yanzu haka a garin Maiduguri ya kamata su kara dagewa. Kuma su ma su canza salon dabarun yaki. Domin maganin ta’addancin da ke faruwa. Nagode. Gaba dai, gaba dai sojojin Najerya. Daga Ismail Alkyabba Funtuwa.
Ga masu sukar Mauludi
Salam. Na ji wasu suna suka akan Mauludi, to, sun makara, duk wadda ya ce bidi’a ne, shi ma yana bidi’a. Ga hujja_ ina babin gasar kur ani da yaye dalibai da tara fatun ragunan layya a sayar da tafsirin watan ramalan da wa’azin kasa da jinkan kudin tafsiri ? A ina aka samo su? Na ji wata malama tana suka a kan maulud. Ina aka ce mace ta yi wa’azi ko shugabanci? Mai suka a kan mauludi makiyin Manzo (s.a.w) ne. Wasu suna cewa mana’yan mushirkai suna mutuwa to su su dauwama. An mutu a harami, da wurin jifa da kuma gobara a asibiti. Rantsuwa suka yi da kur ani? An ki Maulidin Manzo (s,a,w.) an yi na shugaban kasa. Daga dankanam 08110995574.
Allah Ya kare mu daga ‘yan ta’adda
Salam. A isar man da gaisuwata ga ’yan Najeriya. Kiristoci sun yi Kirsamati lafiya Mu ma Musulmi Allah Ya kara ba mu ikon ibada lafiya Ya kare mu daga ’yan ta’addar kasa, kasarmu ta zauna lafiya Ameem Daga Bello Danladi Damba Gusau Phone 07065700052
Kira ga Gwamna Ganduje
Don Allah Editan Aminiya, ku gaya wa Ganduje cewa, su Usman Bala (PPS) suna yi masa ingiza mai kantu ruwa, amma idan an ki ji, to ba a ki gani ba. Daga Com Musa Abdullahi Miltara07068885999
Gaisuwa ga Shugaba Buhari
Edita don Allah a mika min gaisuwa ga Shugaban Muhammadu Buhari ya yi daidai hukucin Sambo Dasuki sai ya bi kudin ‘yan Najeriya. Daga Musbahu Gwaska Kano Madobi danbaure 08066664580.
Kira ga shugabannin Arewa
Salam. A gaya wa shugabanin Arewa su duba tarin ayyukan Sardauna da na Firayiministan farko. Ku duba akin da suka yi, ku yi suma koyi dan Allah 07037476846.
Kira ga PDP a Sakkwato
Assalamu alaikum ga Aminiya barka ku da hidamar jama’a. Don Allah Edita ka bani dama in yi kira ga ’yan jami’yyar adawa ta P D P ta Sakkwato ya kamata ku yi maza-maza ku tara kudin da Kanar Sambo ya bai wa Bafarawa, ya ba ku, ka da abin ya kawo Sakkwato. Kuma mu Sakkwatawa,. muna jinjina ga hukumar EFCC, saboda yanzu ta fara adalci kai mayaudaran gwamnati kotu. Don haka Kanar Dasuki da Baffarawa kuwa Allah ku ba da kudi mutane in ba haka ba, to gidan yari tanan na jiran ku Allah ya agaji ku mutanen P D P na Bafarawan sakkwato. Daga M. Murtala Amwa. Sakkwato.Kanwuri. nagode.