Hanyoyi biyar da za ki bi don inganta fatar jiki
Assalamu alaikum, yaya azumi tare da fatan ana cikin koshin lafiya. Yana da kyau mace ta kasance mai yawan kintsi da kuma gyaran jiki a kodayaushe. Musamman ma in har ta kasance matar aure ce. Sau da yawa sai ka ga mace da zarar ta haihu sau daya sai ta fita hayyacinta. Idan mace ta […]
Assalamu alaikum, yaya azumi tare da fatan ana cikin koshin lafiya. Yana da kyau mace ta kasance mai yawan kintsi da kuma gyaran jiki a kodayaushe. Musamman ma in har ta kasance matar aure ce. Sau da yawa sai ka ga mace da zarar ta haihu sau daya sai ta fita hayyacinta. Idan mace ta kasance mai yawan kintsi, a kullum maigida zai rika yi mata kallon tamkar budurwa ce a wurinsa. Don haka a yau na kawo muku hanyoyi biyar da za a bi domin inganta fatar jiki.
· Idan ana so fatar jiki ta kasance da sanyi a kodayaushe a za a iya hada man zaitun da gishirin teku (sea salt). Za a iya samun irin wannan gishirin a manyan shagunan da ake sayar da kayan kwalliya. Idan aka kwaba sai a rika murje jiki da shi a kullum musamman kafin a shiga wanka. Yin hakan na taimakawa wajen mayar da fatar mace ta yi fes tana sheki.
· Idan an kasance ana yawan shafe-shafe, kuma fatar ta yi dabbare-dabbare, sai a samu lemun zaki ko kuma lemun tsami a rika goge wurin da fatar ta canza kala. Sai a jira na tsawon mintuna hudu kafin a wanke. Yin hakan na haskaka wurin da ya kode a fatar.
· Man tuffa na daya daga cikin ababen dake gyara fatar kai. Kuma yana warkar da kowace irin cuta ta fatar kai. A samu man tuffa kamar kofi daya sai a hada da ruwa sannan sai a rika wanke kai a duk lokacin da kan ya yi datti. Yawan amfani da man tuffa na rage fitowar amosanin ka da kuma kurajen ka.
· Zuma abace wanda zaa sameta a ko’ina. Tana dauke da sinadarai da dama kamar na sanya santsin fata da kuma warkar da tabo da sauransu. A shafa zuma a fuska a kullum kafin a shiga wanka , sannan a bari ta dan jima kamar minti 14 sannan a wanke da ruwan dumi. Yin haka na warkar da kurajen fuska da sanya ta yin haske da kuma yin santsi.
· A rika amfani da man kwakwa a kullum domin yin haka na graya fatar jiki da fatar kai da kuma sanya gashi laushi da santsi da kuma tsawo. Idan aka shafa man kwakwa a kai sai a rufe kan da leda bayan awa daya sai a wanke. Da kin bude za ki sha mamakin yadda gashin kanki zai yi kyau.