Hanyoyi goma wanda za a bi don gyaran jiki
Barkanmu da sake kasancewa da ku a wannan fili namu na kwalliya. A yau na kawo muku hanyoyi goma wanda za a bi don gyaran jiki ba tare da an kashe kudi a shagon kayan kwalliya ba. Ya kamata mata su koyi dabaru da dama domin taimaka wa mai gida. Idan maigida ya saba ba […]
Barkanmu da sake kasancewa da ku a wannan fili namu na kwalliya. A yau na kawo muku hanyoyi goma wanda za a bi don gyaran jiki ba tare da an kashe kudi a shagon kayan kwalliya ba. Ya kamata mata su koyi dabaru da dama domin taimaka wa mai gida. Idan maigida ya saba ba da kudin sayan kayan kwalliya, ranar da babu kuma sai a hadura a gwada daya daga cikin ababen da muke kawo muku na gyaran jiki. A sha karatu lafiya.
>Idan ana so a gyara gashi za a iya hada ayaba da dwai sai a kwaba su sosai sannan a shafa a gashi a jira na tsawon mintuna sha biyar zuwa talatin sannan a wanke.
>domin gyaran farce, za a iya tsoma hannu a cikin man zaitun na tsawon mintuna biyar sannan sai a cire a kullum. Farce zai yi kyau sosai.
>Ana amfani da zuma mai kyau domin samun fuska mai sulbi da laushi. Ana shafawa a fuska a jira na tsawon mintuna goma sha biyar zuwa ashirin sannan a wanke da ruwan dumi. A gwada wannan hadin sau daya a sati za a ga canji.
> Ana amfani da ruwan amfuna da ruwa ana wanke kai. Yin hakan na cire dattin da ke madale a gefen gashin kai.
>Domin masu yawan shafe-shafe za su iya yanka lemon tsami biyu sai su rida shafawa a inda ya yi duhu. Yin hakan a kullum na haskaka badin da ya bayyana a wasu gafen fata.
>Domin samun fatar jiki mai sulbi, za a iya amfani da man zaitun da gishirin rafi a kwaba sai a rida dirzawa a fatar jiki a kalla sau uku a sati.
>Man kwa-kwa na matudar gyaran zubewar gashin ka. Za a iya shafa man kwa-kwa a fatar ka, sannan a shafa a jikin gashin. A bari ya jima kamar na awa daya sannan a wanke.
>Maza masu son man gyaran gemu, za su iya amfani da man kwa-kwa.
> A samu lemon tsami sannan a zuba zuma a kai.Sannan a rida shafawa a kan durajen fuska. Yin hakan na kasha su sosai.
>Man zaitun na sanya santsin fata idan an kasance ana yawaita shafa shi a koda yaushe a matsayin man fata.