Hanyoyi mafiya sauki na rabuwa da amosanin kai
Mata da dama suna fuskantar matsalar amosanin kai. Musamman idan sun je unguwa ko gidajen biki, sai a ga suna ta soshe-soshe kamar masu kwarkwata. Wadansu kuma sukan je shagunan wanke kai domin a magance musu wannan matsalar. Albishirinku ’yan uwana mata! Yau na kawo muku hanyar sauki da za ku bi don rabuwa da […]
Mata da dama suna fuskantar matsalar amosanin kai. Musamman idan sun je unguwa ko gidajen biki, sai a ga suna ta soshe-soshe kamar masu kwarkwata. Wadansu kuma sukan je shagunan wanke kai domin a magance musu wannan matsalar. Albishirinku ’yan uwana mata! Yau na kawo muku hanyar sauki da za ku bi don rabuwa da wannan matsala ta amosanin kai. A ciki akwai ganyen kashu da lemun tsami da ruwan kwakwa da kuma kwallon mangwaro.
Shin ko kun san cewa ganyen kashu na maganin amosanin ka? To ga yadda za a sarrafa shi.
• A wanke ganyen kashu sannan sai a daka shi a kwaba da ruwa.
• Bayan haka, sai a shafa a fatar kai a bari na tsawon rabin awa kafin a wanke. Za a iya yin haka har na tsawon mako biyu insha Allah za a samu saukin amosanin ka.
Ko kun san cewa lemun tsami ma yana warkar da amosanin ka, musamman idan an hada shi da ruwan kwakwa?
• A samu lemun tsami sai a matse ruwan, sannan a hada da ruwan kwakwa.
• Sannan a shafa a fatar ka a jira na tsawon rabin awa kafin a wanke.
Kwallon mangwaro na mangance amosanin ka. Kuma ana iya hada shi ne da madarar ‘butter milk’ kamar haka;
• A busar da kwallon mangwaro, bayan ya bushe, sannan a daka.
• Za a iya kwaba garin kwallon mangwaro da ruwa sannan a shafa a kai ko kuma da madarar ‘butter milk’ sannan a shafa a fatar kai. Bayan minti 30 sai a wanke. Ana yi a kai-a-kai domin harkar fata sai a hankali ake samun sauki.