Hanyoyin amfani da gawayi a fata
Assalamu alaikum manyan mata da kanana. Barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan filin namu na kwalliya. Ko kun san cewa gawayi na da matukar mahimmanci a fata? Yana dauke da sinadaren cire matattun fata domin bada hanya ga fitowar sabuwa ga hana fesowar kurajen fuska da kashe su idan sun fito da […]
Assalamu alaikum manyan mata da kanana. Barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan filin namu na kwalliya. Ko kun san cewa gawayi na da matukar mahimmanci a fata? Yana dauke da sinadaren cire matattun fata domin bada hanya ga fitowar sabuwa ga hana fesowar kurajen fuska da kashe su idan sun fito da kuma rage maikon fata domin yawanta ke haifar da kurajen fuska. A yau na kawo muku hanyoyi da za a bi domin amfani da gawayi a fata a cikin sauki.
• Domin cire kwalliya: a samu man kwa-kwa da na ‘labender’ da ‘baking soda’ (za a iya samu a shagunan da ke sayar da kayan girke-girke) sannan a nika gawayi a tankada shi sannan a zuba wadannan ababen da na lissafo sai a samu gora a zuba. Kafin a kwanta barci sai a dauko shi a rika tsoma auduga ana goge fuskar domin cire dauda.
• A samu nikakken gawayi sannan a samu ‘gelatine’ (za a iya samu a wajen masu sayar da kayan girki) sannan a dora ruwa kadan a tukunya sannan a sake saka wani kwano karami a ciki sai a zuba gawayin sannan ‘gelatin’ din da kuma ruwa kadan haka za a yi ta juyawa har sai ‘gelatin’ din ya narke sannan a zuba a murza a ajiye. Za a iya shafawa a fuska domin cire gishirin fuska. Idan an shafa sai a bari ya bushe kafin a bare.
• Gawayi don magance kurajen fuska: A sami nikakken gawayi sannan a samu ruwan ‘witch hazel’ (za a iya samu a inda ake sayar da kayan kwalliya) sannan a kwaba su tare da diga man kwakwa sai a sake kwabawa sanan a shafa a fuska na tsawon mintuna ashirin kafin a kwanta bacci.
• Rage shekaru: Idan ana bukatar fuska ta yi sumul kamar na karamar yarinya, sai a hada garin gawayi da man kwakwa da ruwa kadan a kwaba sai a rika shafawa a kalla sau biyu a rana na tsawon min tuna talatin kafin a wanke.
• Maikon fuska: A tafasa koren ganyen shayi sannan a tace a jira ya yi sanyi sannan a sami garin gawayi a kwabasu sannan a shafa a fuska banda saman idanu sai a bari na tsawon mintuna goma sha biyar sannan a wanke. Wannan hadin na rage maikon fuska sosai idan an dage.
• Bakin hammata: a kwaba nikakken gawayi da zuma mai kyau sannan a shafa a hammata sannan a bari na tsawon mintuna ashirin kafin a wanke. Ana so a rika yin wannan hadin sau biyu a sati na tsawon sati hudu zuwa biyar.
• karin cikan gashin kai: a zuba man wanke gashi a karamin turmi sannan a zuba nikakken gawayi sannan a kwaba. A tsaga gashi a shafa hadin sannan a bari na tsawon mintuna talatin kafin a wanke. Yana da kyau a rika wanke gashi da wannan hadin a kalla sau daya a sati domin samin sakamako mai inganci.
• Kada a manta a kula wajen amfani da wannan hanyoyin domin kada a bata waje sannan yana da kyau idan aka yi hadin a yi gwaji a kan fatar hannu domin ganin ko fatar ba za ta samu matsala da hakan ba kafin a kai fuska ko gashi.