Hanyoyin da za a bi don rage kibar jiki

Assalamu alaikum matan gidan nan. A yau na kawo muku wata hanyar da za a bi domin inganta kwalliyarmu. Babbar magana a nan ita ce rage kibar jikinmu, domin kiba ba karamar kara wa mace muni take yi ba. Ko da akwai hanci kibar sai ta shanye hancin. Idan har ana son a yi kyau, […]

Hanyoyin da za a bi don rage kibar jiki
Hanyoyin da za a bi don rage kibar jiki

 ZumaAssalamu alaikum matan gidan nan. A yau na kawo muku wata hanyar da za a bi domin inganta kwalliyarmu. Babbar magana a nan ita ce rage kibar jikinmu, domin kiba ba karamar kara wa mace muni take yi ba. Ko da akwai hanci kibar sai ta shanye hancin. Idan har ana son a yi kyau, idan an yi kwalliya, sai an taimaki kai wajen rage wannan kibar. Ba a rana daya aka hada wannan kibar ba. Don haka sai an yi hakuri da juriya kafin a rage kiba. Ga kadan daga cikin hanyoyin da za a bi domin rage kiba don taimaka wa kwalliyarmu.
•A dage wajen cin kayan lambu; kamr su ganye da kabeji da sauransu, domin suna taimakawa wajen rage kibar jiki.
•Ka da a bar ‘ya’yan itatauwa a baya; yawan shan ‘ya’yan itatuwa kamar su lemu da mangoro da ayaba da kankana da sauransu na taimakawa wajen rage kiba, har ma su inganta fata da kwalliya..
•A rika shan ruwan lemun tsami da zuma a ruwan dumi idan gari ya waye kafin a ci komai.
•Ka da a zauna da hada maiko, alhalin ba a motsa jiki, sannan sai a ce ana son rage kiba. Don haka sai a dage da motsa jiki ko da kuwa ‘yar gala-gala ce ake yi za ta taimaka.
•Akwai wata ‘’yar na’ura ko damarar ‘tummy trimmer’ da mata ke amfani da ita domin rage kibar tumbi; idan an sanya wannan abu za a rage yawan ci, sannan a rage kibar tumbi.
• Bayan an yi wadannan abubuwan da na lissafo, tabbas idan an yi kwalliya za a yi kyawun gani, a fito fes sosai. Kuma za a ga kowace irin kwalliya aka yi sai a ga an yi kyau tamkar an rage shekaru. An ce dai  ‘in ana da kyau sai a hada da wanka.’